Chapter twenty-seven

1.4K 150 0
                                    

Bakinta a hangame tsabagen abun mamakin da take gani a gaban ta, wani irin mak'eken gida wato mansion ne wanda ko daga wajan ya tsaro, ba ita kad'ai ba har sauran k'awayen nasu suma baki suka saki sai zuba ma gidan kallo suke, wannan ne irin gida na biyu ta tab'a gani a rayuwar ta bayan gidan su Abdulshakur,

Sauri tayi ta kulle bakin ta dan kada abun kunya yayi yawa, Sacen kallan wajan da abokan ango suke a tsaye tayi ko sun ganta tana k'awyanci, amma ina kowa harkar gaban shi yake sai ma hira da suke ko ajikin su, in har irin wannan gidan ne tasan su sun Saba gani ba sabon abu bane, way'anda suke wanka a cikin naira,

So tayi ta juyar da idanta ta ci gaba da bama gidan kallo abo karo tayi da abudulshakur shima tsaya yake ya nutsu yana jin abinda khalifa ke gaya mishi, tunda suka had'u a airport bata kalle shi ba sai yanzu, wani irin kyau ya k'ara mata, ga sajen shi ya k'ara cika, gashin kanshi ya wani kwanta kamar na larabawa, ko daga nesa da take kallan shi ya k'ara wani irin kwarjini gaba d'aya a cika wurin, sauri tayi ta d'auke kanta da taji murayar zayyan na magana

"Ni da ismail musu mu kama resort amma kawai muka zauna makati tunani muka ya gaskiya matan za sufi sake wa a gida shine mukayi renting wannan mansion d'in" yadda yayi maganar irin he's very proud of himself d'inan

"To yanzu me muke a tsaye, anfi 10 minutes da drivers suka sauke mu amma har yanzu mun kasa shiga ciki" Mubarak yayi maganar duk ya k'osa so bar wurin

Dariya sauran abokan nasa sukayi sannan nasir yace "yana da gaskiya sai mu shiga ko," ai kuwa yana maganar kowa ya fara jan akwatin shi yayi hanyar cikin gidan,

Zayyan ne yayi saurin nuna ma matan wani d'an k'aramin gate

"In kuka shiga ta gate d'innan zai kai ku side d'inku, abu d'an kad'an ne zai dunk'a had'a mu a cikin gidan and akwai wata k'ofa da take linking to side d'inmu saboda dai gaskiya ku zaku dunk'a mana girki" ya fad'a da wasa

Duka matan wurin sai da sukayi dariya sannan suka ce tom ba matsala, sallama sukayi musu sannan suka shige ta wannan gate d'in.

Ashe kallo na ciki, samira bata tab'a sanin ita y'ar k'waye bace sai yau, bayan sun shiga ya gate d'in sai da sukayi y'ar tafiya sannan suka ya wata k'ofa, ai kuwa suka bud'e ta suka shiga,

wani mak'eken parlor suka gani wanda ya sha royal chairs, samira dai bata tab'a ganin irin kujerun ba tunda uwar ta ta haif'e ta, ga wani ne had'ad'en dinning area daga gefe, kujerin wajan suma abun kallo ne, tsayawa ita tayi tama kasa k'arasawa ciki, sai da nabila ta d'an zungure ta,

Bin k'awarta tayi da kallo wacce take faman zuba mata murmushi, wata k'ila nabila ta saban ganin irin wannan duniyar saboda itama iyayen ta masu hali ne,

"Yanzu da four rooms ne a nan, tunda mu 8 me kenan ko wana d'aki mutane biyu," nabila ce ke faman yi ma k'awayen nata bayani, ba wanda ma ke sauraron ta a cikin su kowa ya saka kwayar idanshi zai zuba kallo yake

Samira ce tayi k'arfin hali ya fara cewa

"Ladies!!!, kallon ya isa haka mana, kuna san mazan can side d'in suyi mana dariya" ai kuwa tace sa'a yanzu duk kallon ya dawo wurin ta, k'ara maimaita me nabila ta ce tayi, kowa d'aga kai yayi almun ba matsala, kowa ya nada partner d'in kwanan shi,

"Nikam bazan shiga wani d'aki ba sai na gama kashe kwarkwatar idona tukun" Asiya ta fad'a sannan ta ci gaba da zuba ma pallor d'in kallo

"Lah kuzo kuga, kitchen d'in, Ilham ta fad'i had'e da y'ar murnar ta,

Ai kuwa hannatu da meena da farida har y'ar rige rige suke, suna shiga kowa ya hangame baki, kitchen d'in built in kitchen ne, komai a ciki yakai gashi very spacious, yau kuma tabbas sun zama y'an kwaye,

Sai da suka gama kallo har suka k'oshi sannan kowa yayi d'akin shi, daman d'akin Samira da nabila a kusa Dana farida da meena yake, sai d'akin hannatu da asiya da kuma Ilham da zahra da yake opposite nasu,

Samira na shiga d'akin shima sakar mishi baki tayi, wani irin mak'eken daki ne ga gadon irin queen size bed d'innan, nabila ce ta katse mata kallon da take,

"Zaki fara shiga wankan ne ko in shiga?" Ta tambaye k'awar tata,

Samira ce mata tayi ta shiga ita bari taji ta d'an za zaga, tana fad'an haka ta fita daga d'akin

$$$$$$$$$$$

Dukkan su suna zaune a mak'eken parlor d'in side d'insu hira kawai suke zubawa, wannan ya kamo can wancan ya kamo nan, shi dai abdulshakur dake zaune akan kujera ya jingina da ita da bayan shi yayi shiru kawai yana kallan had'adden garden d'in gidan ta window,

Gaba d'aya abokan nashi wani irin haushi suke bashi, wai su basa gajiya da surutu, yaso ya shiga cikin d'aki amma in har ya shiga ya zauna shi k'ad'ai ya tabbata tunanun nukan da ya tsani yi ne zasu zaman mishi abun hira,

Gaba d'aya kallan shi na kan garden d'in amma gaba d'aya kunnan sa guda biyun suna sauraron su duk da ba maganar da suke illa ta shiririta a ganin shi,

Yana cikin haka kawai yaji nasir ya tab'o shi, shima juya wa yayi ya zuba mishi manyan idanunshi

"Hmm bamu baka labarin abunda ya faru a wajan airport ba kan kazo" sauran najin abun da nasir yace suka saki iho har wasu na zungurar Ismail, shikam abdulshakur ba abunda yake illa ya kalli wannan sai ya kalli wancan,

Nasir ne ya bashi labari kaf abunda ya faru da Ismail har jan wuyan rigar shi da khalifa yayi, me sauran abokan suke in banda dariya, ismail kuwa ya sunkuyar da kai tsabar ya gaji da tsokanar sa da abokan nashi suke,

"Komai ai yazo gidan sauki, khalifa ne kawai zai yima farida magana ta samo maka number d'in yarinyar" zayyan ya fad'a muryar shi dauk'e da zolaya

"Mene ma sunan ta ma?" Shahid ya tambaya

"Samira" khalifa ya fad'a yana murmushi sannan ya kalli ismail yace mishi "Allah in kana son number d'inta zan samo maka, amma ka sani farida bata wasa da rayuwar friends d'inta in har playing d'inta zaka yi ka gaya mun tun wuri"

Tunda abdulshakur yaji an ambaci Samira gaba d'aya wuta ta d'auke masa, mata mutuwar zaune yayi baya ko motsi balle ya gane me sauran ke fad'a, wani irin abu yaji yana taso mai, bai san lokacin da ya zuba ma abokan nashi wata muguwar harrara ba, k'ara kallan ismail yayi yana ta wani sunkuyar da kai sai kace munafiki, ji yayi kamar ya tashi ya kai mishi duka tsabar takai ci,

Baisan lokacin da ya mik'e daga wajan ba yayi hanyar garden saboda in har ya tsaya a wurin komai zai iya faruwa, bai bi takan al-ameen ba da yake ta faman tambayar shi Ina zai je,

K'ofar garden d'in ya buga da wanni mahaukacin k'arfi har sai da ya saka abokan suka tsaya cak suka bari gaba d'aya abunda suke tare da toshe kunnan su,

Abdulshakur wani zafi yaji ko ta ina ajikin shi, gumi ne ya rufe shi, ga wani abu da ya tokare mishi a mak'ogaro, tsabar iskanci irin na ismail, daga ganin yarinya, haka kawai, wani irin jin haushin shi yake, ji yake kamar ya koma cikin gidan yayi mishi dukan kawo wuk'a,

Pacing yake kawai acikin garden d'in abubuwa goma da ishirin sun taru sunyi mishi yawa, za hannu shi yayi ya dafe kirjin ji ko ya d'an daina jin abu na taso mishi,

Yayi mintuna a haka, sai can kuma ya saki hannun shi a hankali da yake kan kirjin shi,

me wannan behavior d'in nashi yake nufi? badai kishi yake ba? Wani irin haushin kanshi yaji ya rufe shi, ya tabbata da abdulshakur d'in daa ne da sai yayi dariya ba y'ar k'arama ba, amma yanzu sam sam halin shi ya daina bashi mamaki, ka manta alkwarin da kayi ma kanka ne, ya tambaye kanshi, ji yayi yanzu kuma kamar ya rufe kanshi da duka, ko maza d'ari zatayi soyyaya dasu me ruwan ka aciki, me sa kake yi kamar saurayin ta ko kuma wani mijinta, wata kuma azababbiyar kunya ce da rufe shi, yanzu ya koma ciki yace ma abokan shi mene, ajiyar zuciya yayi sannan ya sami wata kujera dake a cikin garden d'in ya zauna, in har sun wayar daga pallor ya koma dan yanzu bama yaso su had'u ko mutum d'aya daga cikin su yayi maganar a zuci.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now