Chapter thirty-seven

1.4K 193 2
                                    

Yafi minti goma a tsaya a wurin ya kasa motsawa tun bayan marin da samira tayi mishi, har yanzu kanshi a daure yake, wai ace yarinyar yar k'arama wace bata fi sa'ar k'annan shi ba ce ta saka hannunta a fuskar shi a matsayin mari, hannunshi ya saka fara shafa sumar kanshi kamar yana bar baza gashin tsabar takaici da abun mamaki, shi da ya kwana jiya a zaune ya kasa bacci saboda gaba d'aya damuwar sa na wurin ta, shi ya saka ma tun asuba daya tashi ya fara shirin zuwa gidan saboda bala'in son da yake ya ganta, kuma shi yasan lafiya suka rabu jiya haka kawai baisan hawa ba baisan sauka ba, dole yaje ya same ta tayi mishi bayanin marin shin da tayi

Sauri yayi ya juya ya koma cikin gidan had'e da fitowa da key din motarshi, bai tsaya ya shiga cikin gidan ba yayi musu sallama kawai ya fada cikin motar shi yayi hanyar inda gidan da suka sauka yake.

Yana isa ya fito, gaba d'aya fuskar shi a daure take, babu wasa acikin ta, yanzu kuma wani haushin ta yake ji, tayi za'ace mace ta d'aga hannun ta mare shi, shi ABDULSHAKUR , wani sauri yake bazawa dan ya isa cikin gidan yaci mata mutunci, har yana ban k'ade khalifa wanda suka fito shi da al-ameen,

Khalifa da tunda ga nesa ya hange shi yake washe mishi hakura, daman jiya sun kwana suna neman shi a waya basu same shi ba, da yaga ya bangaje shi kamar hankalin abdulshakur d'in gaba d'aya baya wurin, ya kamo hannunshi,

Sai a lokacin abdulshakur ya lura suna wurin,

"Where have you been ne?? Muna ta neman ka a waya mun kasa samu" abunda khalifa ya fara ce mishi kenan

Abdulshakur kallon su yayi, sannan ya bashi amsa

"Kasan me, yanzu is not the time, I'm in a hurry, ka bari na fito tunkun na" yana gama fad'a ya kwace hannun shi daga rikon da khalifa yayi mishi yayi hanyar cikin gidan yabar abokan shi tsaye a wurin,

Yana shiga side d'in su Samira ya tarar ba kowa a parlor, Tini yayi hanyar d'akin su, har lokacin zuciyar shi azalzalashi take, har zai bud'e k'ofar kawai ya fad'a cikin d'akin wata zuciyar tace mishi a'a yasan a halin da zai tsince ta, kawai ya fara knocking, bai dad'e a tsaye ba yaga a wangale kofar, hannatu ce a tsaye a wurin,

Sai da ya kalli cikin d'akin yaga duk matan a zazzaune, sun juyo sun zuba mishi ido amma banda samira wace take faman kaiwai da kawo wa na had'a kayanta dan yau zata koma kano, tana sanye da wata abaya kanta ba d'ankwali, gashin nan nata a kwance Yana cikin ribbon, har sai da ya kulle idunshi tsabar kyan da tayi nishi,

Yana shirin yaji matan sun mishi magana, ko su tambaye shi me yake yi a wurin yaji shiru, tsabar fuskar shi da take a had'e ba allamar wasa a tare da ita, ga kwarjinin da yayi mishi yawa, bai juya yaga yanayin su ba amma ya tabbata dukan su a tsoarace suke, Samira kuwa daya kafama manyan idanunshi, ko d'agowa batayi ba ta kalli shi, wani haushi ne ya k'ara kamashi, Shiga cikin d'akin yayi,

"Ku bamu wuri" yayi maganar da deep voice d'innan nashi wacce bata d'auke da wasa ko k'adan, yana maganar yaga duk matan su fara tashi suna shirin barin d'akin, sai da yaji ba mutum ko d'aya tare da k'arar kule k'ofar sannan ya k'ara maida hankalin shi kan samira, wacce har lokacin ninke kayanta kawai take, ko kallanshi bata yi ba,

Yafi minti biyar yana zuba mata kallo da wannan laulausan idanun nashi, wani irin takai ci ne ya mishi yawa, me ya hau kanta yau ne, ya tambayi kanshi, ci gaba yayi da kallanta yana so yaji ta fara mishi magana yaji shiru, samira da yanzu tana wurin dressing mirror d'in tana kwasar kayan Shafe shafen ta, shi kuwa abdulshakur da yaga bata da shirin yin magana, ya fara takawa har ya isa wurin da take, hannunta ya kama ya juyo da ita wurin da yake ya kafa mata idanun,

Kwace hannunta tayi, sannan ta k'ara juyawa ta ci gaba da abunda take,

Abdulshakur kulle idanshi yayi da yanzu sunyi jaa tsabar baccin rai, can ya bud'e su ya fara magana

"For Goodness sake kina gani na a wurin nan na tsawan mintuna, atleast kya d'aga ido ki kalle ni ko baza ki yi mun magana ba" yayi maganar cikin mugun fad'a

Samira k'ara yin banza tayi dashi ta ci gaba da harkar gaban ta, a wannan lokacin abdulshakur ya gama k'uluwa,

K'ara binta yayi inda take ya kwacce kayan dake hannunta ya wurgi dasu a k'asa, sannan ya rik'e k'afadarta guda biyu yayi jikin bango da ita ya buga bayan ta dashi, samira sai da kulle idanunta saboda sai da bayan ta yace tas yayi k'ara.

Idanun abdulshakur sun canza, gaba d'aya fuskar shi ta koma jaa, kallon ta kawai yake,

"Ni ba k'aramin mutum bane da zan dunk'a mikin magana kina yi mun shiru nasan sarai kina da bakin yi mun magana ki amsa ni kuma kiyi mun baya nin mari na da kikai" ta hak'oranshi yayi magana wacce da daa ne da sai ta saka Samira yin fitsari,

Har ya gama maganar samira idanunta na gefan shi, can kuma ta juya ta kalle hanna yanshi dake kan kafad'arta sannan ta k'ara juyawa ta kafa idanunta cikin kwayar idanunshi,

"Bance ka daina tab'a ni bada izini na ba, ko marin da na maka d'azu bai maka bane"

Kaiii kaiii, abunda abdulshakur ke cewa a ranshi kenan, gaskiya ya sakar mata fuska da yawa shi yasa har ta ke gaya mishi wannan maganganun, dariya ya saka dan abun yayi mutuk'ar d'aure mishi kai,

K'ara kallanta yayi da manyan idanunshi, a lokacin ranshi ya gama bacci zuciyar shi na tafasa, fuskar shi a d'aure,

"Duk ranar da kika saki kika k'ara saka hannun ki a fuskata a matsayin mari, a ranar zan karairaya yatsun hannun ki"

Kana ganin yadda yayi maganar kasan ranshi a mutuk'ar bace yake, dan yana santa bai bata damar da zata dunk'a treating dinshi haka ba, bata isa ta wulaqanta shi ba, shi da mata ke rubibin shi, ke son ya kula su,

Sakar hannushi yayi daga riketan da suke, ya juya ya bar d'akin tare da buga mata k'ofar, saboda ya k'ara sakwan a wurin baisan abunda zai mata ba, dan wani haushin ta yake ji,

Yana fita Samira ta zube a k'asa tana maida numfashi.

(It took me a week to post this so wheww, I hope you like it, and Samira is trying to push abdulshakur away saboda nabila, duk na gane abunnan da take, But the question is, is it going to work???, cuz as far as I know, they're madly in love with each other especially from his side, don't forget to vote, THANK YOU ❤️)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now