Chapter six

1.9K 161 0
                                    

Samira na fita daga dakin hawaye suka fara zuba daga fuskan nabila tuni ta ruga a guje tayi side din umma tana bude kofan bedroom dinta ta fada jikin ta fara rera kukan ta kuka nabila take yi sosai tsakanin ta da Allah
umma kuwa shiga tambayar ta tayi

"me ya faru, me aka miki ki haka kike kuka iye nabila me ya faru haka kika tada hankalin ki zaka tada mun da nawa hankalin"

nabila bata ce komai ba ta ci gaba da sharar kukan ta sai da tayi mai isar ta sannan ta dago daga jikin ta, umma kuwa saka mata ido tayi tana jiran ta fara mata baya nin me ya faru amma nabila ta kasa cewa komai dan tana fad'awa samira wadannan mugayan kallamai take a wurin tayi da na sani taya zata gaya ma umma abunda tama samira ai babban abun kunya ne kuma ta tabbata umma in taji sai ta ci mata mutunci ba kuma karamin cin mutunci ba dan haka kawai ta share hawayan ta had'e da cewa

"titanic na kalla umma karshen film din abun tausayi shine naji ina son yin kuka"

umma tabi nabila da kallo saboda tasan karya take kuma tabbas akwai abunda take boye mata amma baza ta tuhumeta ba in tayi tsami zasu ji kuma aje a dawo nabila bata da kowa sai ita, ita ce uwar ta dole in abun ya dame ta zata zo ta gaya mata, kawai ta girgiza kanta

"jimin wawiyar yarinya, shine ki rasa inda zaki zo kiyi wannan ta sar sai ah jiki na, ni da Allah daga ni kinbi kin danne ni haka kawai zaki tada mun da hankali ni fitar mun daga daki ma"

nabila tayi murmushi tana shirin fita, umma tace

"zo, zonan ina samirar take badai ta tafi ba?"

Nabila fara shafa kanta tayi sannan tace

"eh wallahi iman ce take ta rigima taki sauraron kowa shine safiya ta kira ta sanar da ita a waya kinsan ya murjanatu ta kawo mata ita yaye"

umma tace a ranta anya ba wani abu ne ya hada su ba saboda samira da wuya tazo ta tafi bata mata sallama ba komai saurin take, amma sai ta dake tace

"kash akwai wasu turaran wuta masu kanshi da aka kawo mun daga maiduguri nayi niyar bata takai ma hajia asma'u dan nasan zata ji dadin su, sai dai nabaki ki kai mata gobe in Allah ya kaimu" nabila kawai murmushi tayi ta tace toh' haka ta fito daga dakin duk jikin ta yayi sanyi.


Haka samira ta dunka tuk'a mota tana hawaye wanni abu ne yazo kirjin ta ya tsaya, ji take kamar bata numfashi, wani zafi take ji a zociyar ta a haka har ta k'arasa gida Allah ya taimake ta yau ba wani traffic. tana shiga sama tayi da gudu kobin takan gwaggo batai ba da take faman mata magana tana shiga dakin ta saka mukulli tayi ta kulle kofan, sannan da zube a kasan dakin ta fashe da kuka, samira tayi kuka tayi kuka har sai da kanta ya fara mata ciwo amma ah haka bata bar kukan ba kowa yasan samira akwai ta da hakuri kuma da wuya abu ya bata mata rai balle har ta sa wani a ranta ko ta zubar da hawayen idanta saboda da wani, yau babbar kawarta wacce ta dauka a matsayin yar uwa ta jini ce ta gasa mata wannan maganganu masu daci dole ne tayi kuka saboda abu ne ta bata taba tsamani ba ko a mafarki, amma zata bar ta da halinta ko an saka nabila a gabas za'a yanka ko uffan bazai fito daga bakin ta ba tayi alkwarin saka ma ta ido kawai ba ruwanta da shiga harkar ta, in har namiji ne to zata gani saboda namiji ba abun goyo bane, tana gama wannan tunanin ta fada bathroom dan wanke fuskar ta dayin alola ana ta kiran sallah la'asar.

Abdulshakur zaune yake akan abun sallah yana lazimi acikin hadaddan bedroom dinshi, kamshi da sanyin AC ya cika dakin saboda shi me san kamshi ne , shi yasa mommy dinshi sai ta tabbata kullum masu aikin gidan sun karaya dakin shi da turaran wuta, yana cikin haka yaji ana kwad'a sallama daga kofar parlor, sai da ya idar tsab da abun da yake sannan ya mik'e hade da nannad'e abun sallar shi ya dora akan wani stool dake gefan gadon shi, yayi hanyar parlor dinshi, yana shiga yaga khalifa (abokin shi) a tsaye ya bude hakwara yana mushi murmushi, Abdulshakur mai da mishi da murmushin yayi hade ta cewa "shigo mana ka wani tsaya a bakin kofa sai kace wani bako" nan khalifa ya shigo tare da baje wa akan 3 seater, abudulshakur shima samin wuri yayi ya zauna, khalifa ne ya fara cewa

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now