Chapter twenty-three

1.5K 156 1
                                    

Abdulshakur na shiga babban parlor din su farida yaga abokanan nasu na shirin mik'ewa alamun sun gama abun da ya kawo su.

Tsayawa yayi ya d'an jingina da bango yana jiransu su gama sallamar da zasuyi, shi a ganin shi in ya shiga yanzu alamun rashin respect ne bayan yayi letti, ga kuma akwai manya a wurin, yana cikin wannan tunanin yaga abokan nasu sun fara fitowa d'aya bayan d'aya, shima bin bayan sun yayi.

Ismail ne ya kalle shi, "wai kai ina ka tsaya ne har aka gama abunda za ayi"

Samira ce ta fad'o cikin ranshi, har yanzu shi bashi da niyar gaya ma abokan shi me yake ji game da ita da kuma matsayin ta a rayuwar shi,

Shima kallan ismail d'in yayi "wani urgent call ne ya tsai dani, nima banso nayi missing komai ba"

Ismail bai ce komai ba ya sani sarai ya aikin abdulshakur yake baya samun hutu wani lokacin, haka sukayi ta tafiya har suka isa wajan motocin su,

Abdulshakur na kai duban shi ga motar nasir gaban shi yayi mummunar fad'uwa, Samira ce a tsaye a wurin da k'atan tray a hannunta, k'ass take kallo duk hayaniyar da abokan ango suke bata d'ago ta kalli kowa ba.

Duk k'awayen amaryar na wurin suma rik'e da wasu trays d'in, sai wani rangwad'a sukeyi da iyayi wato suna so suma su samu shiga wurin wani daga cikin su, wani haushi suka bashi, gaskiya samira daban ce, tunda yake a rayuwar shi bai tab'a ganin mace ba irin ta.

K'ara sacen kallanta yayi yaga har lokacin idanunta na kan tray d'in dake rik'e a hannunta, wani burgeshi yaji ta k'ara yi, wannan ya nuna mishi tabbas Samira daga gidan tarbiya da Kamala ta fito, da wuya ka samu irin mata kamarta yanzu a duniya, masu rik'e ajin su da mutuncin su, ji yayi wani abu ya k'are dakar zuciyar shi, wani irin abu yake ji game da ita a dukkan jikin shi, wani irin masiffafan mutunci ta yake gani.

Tunawa yayi yadda, d'azu ta nuna k'arara bata san taimakon shi, mata da yawa na hauka da mutuwa kawai dan ya kula su, amma ita sam sam duk abunda yake yi ko ajikinta, shi kanshi baisan me ya shige shi ba d'azu, ita ce mace ta farko da ya tab'a yi wa haka a duniya kuma yanaji itace ta k'arshe, in har ya ganta baya tsayawa yayi nazari ko tunani kan ma ya ankara yayi abunda zuciyar shi ta gaya mishi kawai,

Yana cikin wannan tunanin yaji nabila a gabanshi, sai wani rawa take da jiki kamar mai jin sanyi, had'e fuskar shi yayi sosai dan kada ma ta gaya mishi abunda baya so yaji,

"Ka tsaya a wuri d'aya tunda ka fito, abokanan ka har sun fara shiga mota, ga ni kuma inajin haushi da kishi saboda duk matan wurin nan kai suke kallo, ka bud'e mana boot d'inka musa wasu trays d'in ku kama hanya ku tafi dan gaskiya bana so su cinye mun kai da idanun su" ta fad'a ah shagwab'e,

Abdulshakur bema d'ago ya kalleta ba saboda gaskiya zai iya hanb'are da ko ya gaya mata wata maganar saboda wani irin haushin ta da yake ji, kawai zaro muk'ullin motar yayi ya danna remote d'in dake jiki boot d'in ya bud'e, sannan ya fad'a cikin motar be k'ara bin kan nabila ba,

Ya sani sarai so take da nuna wa duniya akwai wani abu a tsakanin su, dubawa yayi  ta mirrors din motar shi ko zai ga samira yaga bata wurin, alamun har ta koma cikin gidan, ji yayi ranshi ya b'aci saboda be gaji da ganinta ba, wayar shi ya zaro ya fara latsa wa dan takaici da bak'in ciki,

Ji yayi anyi knocking d'in window dinshi yana d'aguwa da kanshi yage nabila na sakar mishi murmushi, saura k'iris yayi rolling idanunshi, ya dad'e bai ga mace me naci kamar wannan yarinyar ba ace mutum kamar maye, ita bata ganin yadda k'awarta keyi ne, duk ya fad'a a k'asan ranshi, har da bazaiyi winning glass d'in ba, kawai dai yayi amma har lokacin idanunshi basu bar kan wayar shi ba,

"To mudai mun gama da komai, yanzu zaku iya tafiya, d'an Allah ayi driving a hankali, Allah ya tsaremun kai," can kuma tace "yaushe zaka zo ne? Tunda makayi hutun makaranta ban ganka ba sai yau, baka dauk'an waya ta ko kad'an, ni kuma wallahi ina so kullum in saka ka acikin idanun na" tayi maganar a irin muryar da ta Saba.

Abdulshakur ci gaba yayi da danna wayar shi kamar bada shi take magana ba, sai da ya gama abunda yake sannan yace,

"Zanyi tunani" had'e da kunna motar shi da saka seatbelt,

be k'ara bi takan ta ba ya fara reverse da shirin barin wurin, abokanshi na ganin haka suma suka fara bin bayanshi dama shi suka tsaya jira,

Nabila kuwa baki a hangame ta bishi da kallo, ai ita ta d'auka da ya fara kula ta har da zuwa dauk'anta a makaranta ya d'an fara santa ne, amma abunda yayi mata yanzu ya tabbata mata har yanzu suna jiya i yau, tasan baza ta k'ara ganin shi ba sai a trip d'innan da zasuje,

"Duk abunda zakayi sai na aure ka abdulshakur, komai wulaqanta ni da zakayi bazan tab'a daina sanka ba" ta fad'i maganar tare dayin murmushi, sannan tayi cikin gidan su farida, da murnar ta kamar ammata alk'awari da gidan aljanna.

$$$$$$$$$$$$

Zaune take akan gadonta ta k'ura ma bangon d'akin ta idanu, tunda ta dawo daga gidan su farida awa d'aya da rabi da suka wuce ta kasa tab'uka komai, ko d'ankwalin kanta bata cire ba ballanta na kayan dake jikin ta, tsoro ne cike a cikinta,

Taya za ace mutumin da baya gabanta wata biyu da suka wuce shine yau yake cikin ranta, gaba d'aya ta kasa gane kanta, tunda abunda ya faru a wajan gidan su farida ta kasa daina tunanin shi, ta canza gaba d'aya ko da ta koma wajan kawayen su har sai da suka gane, abu ta dunk'ayi jiki a sanyaye ga bata magana,

Tsoro ne ya sake kamata, wana irin hali take shirin sa kanta aciki ne, wai itace yau ta nemi tsanar da take mishi ta rasa, daa bata so ko kad'an su kasance a waje d'aya ko kallanshi bata sonyi, amma yanzu ko d'igo d'aya duk bata jin way'annan abubuwan,

Gaba d'ayan shi ya dagulamata tunaninta, gaba d'aya ta kasa sukuni, tayi niyar yaki ce shi gaba d'aya daga duniyarta amma yau duk ya ruguza mata shirinta, me yasa yau ya nuna ya damu da ita, me yasa ya taimaka mata, ita ta sani sarai abunda ya mata yau ba halinshi bane, da wata ce ta ce mishi ya taimake ta ko da nabila ce in har bai ga dama ba to wallahi bama zai kalli inda suke ba har kuma su d'ige ko kuma su narke, amma me yasa ita, dama bata tambaye shi ba,

Tunawa tayi yadda tun lokacin da ya fara dauko nabila a makaranta har zuwa yau, yadda gaba d'aya ya canza mata, wani irin abu taji ya daki zuciyarta sai kuma faman harbawa take, k'ara tuna matsayin nabila tayi a rayuwarta, da ita aminyar kwarai ce be kamata har ta zauna ta dunk'a tunanin saurayin babbar k'awarta ba, bai kamata ta dunk'a jin wani abu game da shi a ranta ba,

Gani tayi hannayanta dake zaune akan cinyarta sun fara jik'ewa alamar hawaye take, tausayin nabila take ji, bata cancanci ta zama k'awarta ba,

Ji tayi gabanta ya k'ara bugawa, zazzab'i me zafi ya fara shirin rufe ta, da ta fara gane abun da take ji game da abdulshakur, saboda ita ba yarinya bace shekaruta ashirin da uku, ta san mene SO kuma tasan yadda yake ta san azabar shi.

"wana abun kunyan ne ke shirin faruwa dake Samira" ta fad'a a fili

Zuciyar ta na san ta samu galaba akanta kenan, jikinta ne ya fara rawa saboda tsabar tsoron da firgicin da take ji a lokacin, kukane sosai yanzu yake shirin kub'uce mata,

A gaskiya zuciya bata da k'ashi, taya za ace mutumin da bata wani saniba a duniya da duka duka zata iya k'irga sau nawa magana ta tab'a had'asu shi ke shirin wargaza mata rayuwar ta gaba d'aya a d'an k'aramin lokaci,

Yanzu kuwa Samira kuka takeyi sosai, Allah ya taimake ta d'akin ta ne k'adai a sama da kuwa y'an gidan su sai sunji sun fito, har lokacin jikinta wani irin b'ari da rawa yake, ga ba abunda take ji sai tsoro.

Ta dad'e tana kuka, sai kuma can ta d'an sami nutsuwa, k'ara yi ma kanta akwari tayi, ba wanda zai tab'a sanin zancen nan, zata barshi acikin ranta komai wuya kuma zatayi kukari taga zuciyar ta bata k'arasa cin galaba a kanta ba, zata fitar dashi a cikin rayuwarta ko ta halin k'ak'a ne,

Share hawayen ta tayi sannan ta mik'e dan shiga bathroom d'inta tayi alwala dankai kukanta zuwa ga mai duka.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now