Chapater one

6.6K 321 6
                                    

Tafiya yake a guje a cikin motar shi, sharar gudu yake ko a jikin shi saboda tsabagen makaran da yayi wajen wani babban meeting da zai gudana a karfe goma na rana, makaran da yayi ya mutukar bata mishi rai saboda duk wanda ya sanshi yasan he is always on time, ba yasan latti that's the number one rule a company dinshi, amma wai shine yau ya makara of all days,

amma kuma ta wani bangaren baiyi blaming kanshi, ba jiya har 3am na dare yakai shi da daddy suna duba wasu muhimman takardu na company dinsu, bai samu yayi bacci ba sai wajan 4 na dare, shi da yasa ba ma kansa da tashi tun 3:30 na dare dan yin sallolo da adduoi har zuwa kiran sallar asuba, kuma in yayi asuba baya koma wa barci zai je gym din gidan shi na kamar awa daya, sai ya koma yayi wanka ya shirya duk inda 8 tayi mushi yana office.

Security guards din dake zaune a dadai gate din company dinshi ne suka hango motar shi tunda ga nesa har yadda yake faman gudu, ai tuni suka tashi da sauri suka wangale mai gate soboda duk yanda akai yau oga baya san ammai wasting time, haka ya cusa kan hancin motan shi a guje ya shige security guards din kuma saluting dinshi sukai,

yana zuwa wajan parking dinshi ya zarce wanda akayi personally saboda shi, yana parking secretary dinshi ya bude mai k'ofa, yafi awa biyu yana jiran shi a wajan duk ya gaji ga ba damar complaining saboda yasan ogan sa baya san raini, wa ma yake sakar ma da fuska harda zai sami damar raina shi ya tambayi kanshi,

fitowa daga motan yayi a lokacin secretary din shi yayi saurin rufe motar sannan yabi bayan shi cewa yake "sir sunfi awa biyu suna jiran ka a wurin meeting din(conference room)" tare da mika masa wasu takardu, Abdulshakur ya karba sanan yace "usman bana san surutu" yayin da yake kallan takardun Usman yace "sorry sir" bai ce mishi komi ba haka suka ci gaba da tafiya har sanda suka isa conference room din, wani guard ne ya bude musu kofa yana shiga duk wanda yake kan kujera sai da ya  mik'e, haka Abdulshakur ya ci gaba da takawa har ya isa inda kujerar shi take, ya zauna yana zama kowa na wurin ma ya zauna yace "zaku iya gaya mun cigaban da muka samu a wannan company din na watan da ya wuce"

tuni directors suka fara magana suna gama wa team leaders suka dauki nasu, abudlshakur a nutse yake kallan kowa kuma duk hankalin shi na sauraron su sai da yabari suka gama tsab sanna ya fara magana "I'm very impressed duk meeting din da mukai this is the first time Dana gamsu"

yan wurin suka bi juna da kallo, su sunsan abu ne me wuya a samu matsala a company din, wasu sunsu tunda suka fara aiki shekaru da shekaru kuma tun da ogan su ya fara aiki a wurin shekara biyar baya kenan kullum wurin kara bun kasa yake, a shekaru biyu da hawan shi kan kujera sukayi fuce ko wanne fannin a nigeria, suna da branch ko wane state ma haka, har da yawa a wasu african countries din ma kuma hakika ko wane wata sakamako na kyau yawanci ma wani watan yana fin wani, amma shine bai taba gamsu ba sai na wannan wata tabdi, "kun burge ni mutuka yadda kuka nuna mun kwazon ku dan haka akwai karin salary" tuni wasun su su ka fara shewa sannan ya kara da cewa "amma na wannan watan ne kadai" wayyo wa sunsu suka ce kash abudlshakur yayi murmushi har sai da dimple dinshi ya fito ya mike ya fuce daga wurin yabar su da hayaniyar su,

Usman yabi shi a baya. Sannin kowa ne a company din abudulshakur na mutukar san ma aikatan shi duk da bai sakar musu fuska sosai saboda baya san raini amma duk haka bai sa sun tsane shi ba saboda yana mutukar kyautata musu.

Yana shiga office dinshi ya aje files din dake hannu shi akan tebur dinshi sannan ya fara cire ma ballin suit dinsh, ya cire ta saman ya rataya ta wajan ratayawa, sannan ya zauna kan kujera tare da kallan Usman "wai kai baka gajiya da bini ko ina? Kafafun ka basa ciwo?" Usman yayi murmushi yace "kasan in har kaine bana gaji yawa kuma shine abunda ya kamata nayi a matsayi na na secretary dinka " abudlshakur ya gyada kai, sannan yace " to naji yanzu zaka iya tafiya in baka da abun cemun" usman yayi saurin cewa "kasan Naseer Abudllahi na gayatar ka gidan shi bayan ka tashi daga aiki yace baka daukan waya"

tuni abdulshakur ya tamke fuska saboda yasan maganar da zai mishi in har yaje bai wuce na yar shi ba kuma a gaskiya ya gaji da nabila tana da matsala sosai kuma shi baya san abun da zai tada mishi hankali, ya dan jingina da kujerar sanan yace " tom naji zaka iya tafiya" usman ya ce yes sir sannan yaja mishi kofa Usman na fita ya jawo takardun kusa dashi ya fara aiki.

$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$

Samiratu! Samiratu wai kina inane sai faman kwada miki kira nake, samira dake faman saka yarinyar yayarta yin barci ta mike a hankali ta fito daga dakin sanna ta wuce in da jiyo muryar kakar tata wacce take cikin daki tana faman gogan goro,

tura kofan tayi tare dayin sallama " gwaggo kiyi hakuri iman nake kokarin sakawa bacci kuma bana so nayi magana ta farka kinsan bata da nawyin bacci" kakar tata ta dago kai "oh ni maryama tunda nake ban taba garin irin soyyaya kamar irin take da wannan yarinyar" samira tayi murmushi sannan tace " kullum dai haka kike cewa baccin kinsan yaye aka kawo ta kuma in ban kula da itaba wane zai yi? Safiya bata da aiki sai yin chatting taci tasha ta kwanta yaya muazzam baka ma ganin shi sabgar gaban shi kawai yake yi" gwaggo ta kura mata ido "ni ba surutu nace ki cikani dashi ba ki shiga kitchen ki debo mun abunci yau tabawa ta wuce gida da wuri tana da suna" haba dai samira tace, shine baba tabawa ko sallama" gwaggo taci gaba da gogan goran ta " har wata sallama zata miki abunda zaki ganta gobe" kai gwaggo, ta fada tare da fada wa cikin kitchen tana shiga ta fara hadama ta abincin ta saboda ita abinci daban take ci saboda diabetes dinta, tana gama wa ta koma dakin ta ajiye mata plate din a gaban ta tace "to gashi na gama" kakarta duban ta tayi tace "to nagode Allah miki albarka" samira tace "amin gwaggo na muyi fada mu shirya" yayinda take fita daga dakin tana dariya gwaggo ta bita da kallo "jimin jairan yarinya ta mai dani kamar sa'ar ta zaki dawo ki Same ni ne" ta fada tana jawo plate din abincin,

Samira tana fita dakin ta tayi, tana kuwa shiga ta ci karo da wayan ta tana ringing, ta karasa da sauri ta dauki wayan sunnan BF❤️ ta gani akan screen din tayi sauri ta daga, tana dagawo taji ana sharshekar kuka, gaban samira ya fadi

" Nabila me ya faru kike kuka wane ya taba ki"

nabila dake can bangare ta amsa cikin kuka

"Daga kawai na tambaye shi yaushe zai kawo kudin aure da kuma kai maganar mu gaba shikenan ya kashe mun waya shine kusan kwana biyu bayan daukan wayata ko nakira har Abba na saka ya kira shi tunda ya dauka na farko yaji magana tace bai sake daukan wayar shi ba, shima dazu ya kira secretary dinshi yace yana neman shi a gida yace zai fada mishi amma har yanzu ba muji reply ba tun safe"

ta karasa tana kuka, samira kuwa tana jin haka hankalin ta ya kwanta, saboda ta zata wani abun ne ya faru saboda nabila bata taba kiranta tana kuka ba ta gyara murya tace "kinsan me nake so dake?? Ki kwantar da hankalin ki bari nazo gidan naku sai naga mene abunyi " tuni nabila ta saki murmushi me sauti "wallahi har na danji dadi best friend da kika ce zaki zo amma kuma mama bata gari gwaggo zata barki ki fito?"

Samira tayi dariya "to mene amfanin waya? zan kira na tambaye ta kuma nasan bazata hana niba" nabila tace "yauwa to ina jiranki" nan sukai sallama suka kashe wayan, suna kashe wa samira ta fara neman layin mamanta suka gaisa sannan ta tambaye ta zuwa gidan su nabila, ai kuwa ta barta tana kashe wayan ta nufi dakin safiya " sarkin chatting ni zan fita ki koma ki zauna da iman a guest room in case ta tashi, kuma in ta tashi ki dama mata custard dan Allah kada ki tsaya latsa waya, tana gama magana ta fuce bata tsaya taji me zata ce ba, saboda yanzu zata gaya mata useless excuses dinta ai kuma tana fita safiya ta fara bubuga kafa da kumburo baki ita an takura mata. Samira to koma dakin ta ta fara shirin fita.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now