Chapter five

1.8K 176 0
                                    

(Ci gaban labari)

Da samira ta isa gidan su nabila wanda yake a lamido crescent a garin kano ta danna horn da adduar kada Allah yasa malam ayuba (mai gadin su nabila) beje yawan shi na tsiya da ya saba yawancin kullum in tazo gidan nan sai ya shanya ta kamar shanya kan yazo ya bude mata gate wani sa'in sai ta hada da kiran nabila a waya ita sam sam baiyi mata ba saboda bashi da hali ta rasa mai yasa baza su dauko securities ba dan sun iya irin wannan aikin sosai tana wannan tunanin taji ana shirin bude gate nabila tace yau nayi sa'ah a zuciyar ta haka ta cusa kan motar ta ta shige gidan yayin da malam ayuba ke daga mata hannu yana washe way'annan hakuran nashi dan ya san samira ta saba mishi alkairi da wuya tazo gidan ta tafi bata bashi kudin goro ba haka har ta isa wurin parking ta aje motar ta sannan ta fito ta danna ma motar lock.

Sanye take da abaya bak'a tayi nad'i da mayafin tayi kyau sosai ta fara takawa zuwa cikin gidan, doorbell ta danna tana jiran a bude mata nabila dake cikin gida ta jiyo ta fito da gudu har tana bankad'e baba yalwa me aikin su wacce ta taho bude ma samira kofa nabila tayi saurin cema ta

"ki koma ki cigaba da aikin ki zan bud'e mata"

haka baba yalwa ta bita da kallo sannan ta kwashi k'afar ta ta koma kitchen daman tuwo take shirin tuk'awa, nabila na bud'e kofa ta fada jikin samira ta rungume ta har samira ta kusan fad'uwa sun danyi sakwanni ah haka sannan samira tace

"wannan irin murnar gani na haka kodai kin shirya da mutumin naki?"

Nabila ta d'ago daga jikin samira

"wallahi bestfriend bamu shirya ba kawai naji dad'in ganin ki kinsan tun shekaran jiya raban da na saka ki a ido na" 

had'e da jan hannun ta zuwa cikin gidan su, suna shiga nabila ta wuce side din umma dan tasan samira baza ta zauna a dakin taba sai ta gaishe da ita, suna shiga bedroom dinta su ka tarar da umma zaune akan gado tana gyran wasu kaya, samira ta tsugunna har k'asa ta gaishe ta had'e da ta cewa

"lah umma kikawo in taya ki ninke kayan"

umma ta amsa mata cikin fara'a

"lafiya kalau d'iyata, ki barshi kinji nama kusa gama wa, yasu maman taku?"

Samira da murmushin ta itama ta amsa mata

"wallahi tana nan lafiya tama tafi abuja jiya wai suna da wani meeting" umma tace

"Allah sarki to inta dawo ki gaida mun ita kice zanzo in karbi tsarabar hanya"

samira da nabila suka saka dariya

"toh shikenan umma insha Allah muka yi Waya zan gaya mata"

nan suka mik'e suka bar dak'in tare da jawo mata k'ofa.

Suna shiga dak'in nabila samira ta fad'a kan gado had'e da cewa wash Allah na, nabila dake binta da ido tace

"kingan yadda kika wani baje akan gado sai kace wacce ta kwana tana wani babban aiki"

samira ta d'ago kanta ta kalli nabila

"kulan da nake da iman ba dole na gaji ba, kinga tun 4 mike tashi ta fara neman nono haka nake had'a shayi na bata in ba haka ba ta dank'i yin kuka kuma in ta gama shan tea sai na goya ta sannan zata koma bacci in ko ban goya taba baza tayi shiru ba ga safiya tana can dakin ta tana sharar bacci ko ajikin ta mama ce ma da tana nan take  d'an taimaka min"

nabila ta saka dariya

"nifah tsakani da Allah banga laifin safiya ba saboda ba ita tace a kawo miki ita yaye ba san babies dinki ne ya jawo miki ba komai ba"

samira ta girgiza kanta

"wallahi duk randa aka miki aure ke da safiya kuma kuka haihu zaku gane ma aya zak'in ta, gwanda ni yanzu na saba ma kaina"

nabila tace

"ke kada ki damu nanny zan d'auko ta dunka kula mun dasu hanakali na a kwance nasan mijina ba hana wa zaiyi ba"

samira bata yi mamaki ba wannan kad'an daga aikin tane nabila ta daina bata mamaki,

"yanzu to ya maganar mutumin naki? Ya ake ciki ya dauki wayar taki ko kuma ya kira ki back"

nabila tace "hmmm" tare da samun guri akan gadon kusa da samira ta zauna

"kin san Allah bai kira ni ba kuma baiyi returning calls dina ba na rasa ya zanyi kawai na zauna jiran ki da kika ce in kinzo za'a samu abunyi"

samira tayi ajiyar zuciya sannan ta k'ara matsowa kusa da nabila ta kama duka hannayanta biyu ta ruk'e sannan da dago idonta ta kalle ta, ta fara magana ah hankali

"Nabila kinsan ni aminiyar kice ko? Kinsan kullum muna cikin nemar shawarar juna in abu yayi mana duhu ko?? Kinsan bazan tab'a gaya miki abunda zai cutar dake ba ko??"

duk abunda take cewa nabila na d'aga kanta alamar eh duk ta taro nutsuwar tana sauraran ta sannan samira ta cigaba da cewa

"Yanzu had'uwar ku da Shakur (haka samira take kiran shi) kusan wata 5 kenan bai taba nuna wa ya damu dake ba asalima kullum ke kike cikin kiran shi a waya kuma in zaki kira shi sau 100 sau 5 ne zai dauka duk missed calls dinki da zai gani bazai taba kiran ki ba, ki gaya mun dan Allah in haka soyayya take?"

Nabila shiru tayi ta zuba mata ido, samira ta cigaba da cewa

"Shakur baya sanki nabila me yasa kika dage dole sai shi? Kifa sani mu mata an sannmu da jan aji da k'ima da daraja, ba ajin ki bane bin wani wai shi namiji, in har mace ta nuna wa d'a namiji ta damu dashi to wallahi ya samu hanyar rainata da wulakanta ta ke nan bazai tab'a bata daraja ba, to ki gaya mun me yasa kike san zubar da mutunci saboda shi? Bafa shine kad'ai namiji a duniya ba, ba kuma ki rasa mijin aure ba maza da yawa suna san ki kula su kuma maza masu class masu kudi masu kyau duk abunda Shakur ke tak'ama yana dashi da yawan su suma suna-"

nabila fusge hannun ta tayi da yake cikin na samira bama ta bari ta k'arasa fad'ar abunda zata ce ba saboda magan ganun da take basu da ma'ana a wurin ta tare da tashi daga kan gado hadda sa hanuwan ta a kogo tayi shirin sauke wa samira buhun masifa dan tayi bala'in bata mata rai jinta take yi a mak'ogarun ta, ta fara cewa

" to sannu sarkin a sani, gaya mun bansan komai ba kuma bani da illimi da tunani ke kike dashi, samira tsabar ranin hankali ni zaki kalla ki gaya wa way'annan magan ganun to wallahi kinyi kad'an ba'a haife kiba kuma baza'a taba haifar ki ba sannu sarkin basirar duk duniya, wato ina zubar da mutunci na da nake bin Abdulshakur ke kinsan wane Abdulshakur babu irin shi a kaf Africa gaba d'aya ballan tana nigeria ina shirin samun alkairi kina so kimun buk'ulu to wallahi ahir dinki ki fita daga ido na, ai danaji kince in kika zo za'a san abunyi wallahi na zata abun arziki zaki fad'a min wallahi dana san wannan magan ganun zaki fad'a mun da tun a gate zance malam ayuba ya hana ki shigowa cikin gidan nan ke da tun ah waya zan sauke miki duk abunda kike ji dashi saboda ni ba tsoran ki nake ji ba"

samira dake zaune tayi shiru tana bin nabila da kallo kwalla ta cika mata ido taf jira kawai suke su fara zubo wa wai itace yau nabila ta rufa ido take gaya wad'annan magan ganu akan wani banza namiji, nabila dake aminyar ta shekara da shekaru itace yau take mata wannan cin mutunci abun ya daure mata kai saboda ko ah mafarki bata taba tsamin haka daga wurin ta ba, da taga kwallar ta na shirin fadowa tayi sauri ta dauki jakar ta ta mike ta fara shirin barin dakin barin ma gidan gaba daya dan baza ta taba yarda nabila taga kukan ta ba kuma baza ta iya tsayawa taji cin mutunci daga bakin taba haka ta fita tare da bugama nabila k'ofa bama tasan tayi ba saboda tsabar bakin ciki haka ta kama hanya tabar cikin gidan tara da fadawa cikin motar ta bama ta tsaya yima umma sallama ba, tuk'i kawai take yi tana zuwa bakin gate ta fara horn ba tsayawa haka malam ayuba ya fito daga ban daki a rikici yana gera tazuge yau duk yadda aka yi ba lafiya wannan irin horn da samira take zubawa haka shi tunda ya santa bai taba ganin tayi haka ba ko wani abun ne ya had'a ta da babbar aminyar ta, da sauri sauri da gudu ya karasa ya bude mata gate samira kuwa fisgar motar ta tayi ta fuce daga gidan a guje  malam ayuba ya fada a ranshi haka yarinyar nan zatayi tuk'i cikin wannan yanayin Allah dai ya tsare.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now