Chapter seventeen

1.5K 169 1
                                    

Kaunce yake akan doguwar kujera a cikin mak'eken office dinshi, dantsen hannun sa nakan fuskar shi, wani ya shigo zaiyi zatan bacci yake amma ko d'aya, wani ciwon kai yake da yanzu ya zame mishi jiki,

kullum da ciwon kai yake tashi kuma dashi yake kwanta wa bacci in har ya samu baccin kenan, abun duniya ya taru yayi mishi yawa, samira ta kusa ta haukata shi, har yanzu baisan yadda zai b'ullo wa alamarin ba, so yake ya gaya wa wani halin da yake ciki amma tsoro ya hana shi,

ya na jin tsoron jiye ma kanshi abunda be shirya ba, shi yasa har yanzu ya kasa sanarwa kowa, sati biyu yanzu da zuwan samira gidan su da kaimai kaya, kullum in zaiyi bacci zai saka wannan recording din muryarta, shi kad'ai ne ke sashi samun nutsuwa,

amma tun kwana biyar da suka wuce ya kasa samun bacci, dalili kuwa shine, so yake yaganta, so yake ya saka ta a idanun shi, amma kamar abu ne me wuya, shekran jiya da abun yayi mishi yawa ya dauki wayar shi ya kira number dinta amma busy, haka ya k'ara kira abu d'aya, a ranar ya kirata ya kai sau asirin amma busy, daga k'arshe ya gane blocking dinshi tayi, ranar baiyi baici ba shima saboda tsabar takai ci, wai har shi mace take wulaqanta wa, wai shine mace tayi blocking a waya, ranar alkwari yayi ma kanshi da bazai sake waiwaiyarta ba, amma ya kasa

Washegarin ranar yana zuwa office ya cewa usman ya nemo mishi inda gidan su yake a cewa shi zai je ya ganta, ya nemo gidan amma ya kasa zuwa, a ganin shi zaiyi invading privacy dinta, tunda ba ita ta bashi izini ba,

Kullum yana cikin jin haushin kansa saboda shi yasan duk haukan da yake yi akanta ita bama tasan yanayi ba, ya sanshi kad'ai yake kid'an shi da rawarshi, yanzu ya zaiyi yana ji in bai ganta ba kwana kusa zai iya zare wa,

Wani abu ne yazo masa ransa, da sauri ya mik'e daga kwanciyar da yake, me yasa tun tuni bai yi tunanin hakan ba, da sauri ya k'arasa inda yake ajiye suit jacket dinshi, daukan ta yayi tare da muk'ullin motar shi da wayar shi ya fita daga office d'in, gaya ma usman yayi ba zai dawo office ba sa gobe sannan yayi hanyar waje.

Yana isa gida, ya fad'a toilet, yayi wankan yayi shigar sa cikin k'ananan kaya, sky blue shirt, da dark blue jeans yayi kyau sosai, kiran nabila yayi a waya, a ringing na biyu ta dauk'a, muryarshi a had'e ya fara mata magana

"Yau kinje makaranta?" Ya tambaye ta,

nabila kuwa daga can b'angaran sai murna take, saboda raban da ya kirata a waya ko ta saka shi a idanta anfi wata biyu, yawan ci itace take kiranshi kuma bai cika dauka ba in ma ya dauka to tabbas ita zatai ta surutun kuma tana farawa yake katseta yace yana da abunyi in ya gama zai kirata amma bata k'ara jin shi,

"Eh naje makaranta, me yasa kake tambaya" ta bashi amsa had'e da mak'e muryarta

Abudulshakur tsaki yaja acikin ranshi, kwata kwata yarinyar batayi mishi ba, yanzu ma dan yana bala'in so yaga samirar shi shiyasa ya kirata da ba abunda zai sa shi ya b'ata lokacin shi,

"Karfe nawa zaki gama lectures?"

Ya k'ara tambayar ta muryar nan tashi ba wasa,

"Mumma gama, mun dai tsaya tutorials ne shima nan da minti talatin zamu gama"

Wata ajiyar zuciya yayi, sannan ya kai duban shi ga agogon dake manne ajikin bangon bedroom dinshi, karfe hud'u da rabi yanzu, 30 minutes ya isa yakai shi in har ba traffic a gari,

"Zanzo na dauke ki, ba sai kin kira driver dinki" ya gaya mata bai tsaya yaji me zata ce ba kawai ya k'ashe wayar.

Daukar muk'ullin motar shi yayi, ya fita zuwa garage, unlocking dinta yayi sannan ya fad'a ciki yayi hanyar buk.

$$$$$$$$$$

Samira ce ta kalli nabila, "har yanzu baizo ba gaskiya ni zan tafi, tunda bani yazo dauka ba abunda zai sa nayi ta jiranshi"

Nabila ta kalli agogon dake hannun ta, yanzu k'arfe biyar da kwata, sannan ta kai kallanta zuwa ga aminayar tata

"I'm sure traffic ne ya tsai dashi amma nasan ya kusa zuwa, farida ta tafi in har kika tafi kinga ni k'ad'ai zanyi ta tsayuwa dan Allah mu d'an k'ara jiranshi kinji bestfriend"

Samira tace mata tom, suka ci gaba da hira sun, bayan miti biyar sai ga wayar nabila ta fara ringing, tana dubawa kuwa abdulshakur ne, wani murmushi ta saka, ko da nabila tace mata shi zai zo daukan ta daga makaranta, samira taji abun wani iri, abun ya bata mamaki, har a k'asan ranta take cewa ko dai ya fara san k'awarta ne?

Horn din mota ne ya katse ta daga tunanin da take, tana can tana tunani ashe har nabila ta mishi kwatancen inda suke,

Dukkan su biyun suka bi da motar da ido har tayi parking, har mata da mazan dake wurin suma sai da suka bita da kallo saboda suga wane zai fito a mak'ekiyar motar nan me tsadan gaske, sai dai bai fito ba har suka gaji da sakin baki suka kulle kowa ya koma harkar shi,

Nabila tayi sallama da samira sannan tayi wajan motar abudulshakur.

$$$$$$$$$

Tunda yayi kwana ya hange su a zaune, kuma tun lokacin da ya hango su idanunshi nakan samira ga gabanshi da yake ta faman bugawa,

yanzu tana yi mishi kyau, ba kamar lokacin da ya fara ganinta ba da lokacin da ya ganta na biyu, tunda ya tun karo wajan ita yake kallo dukda driving yake, wani murmushi yayi, a take yaji kamar duk anyaye mishi dukkan bak'in cikin shi.

Samun wuri yayi yai parking motar shi, har lokacin da yake parking motar shi idanunshi na kan samira ya kasa dauke su daga kallanta, gani yayi sunyi sallama da nabila, ita ta wuce hanyar motar ta ita kuma tayo hanyar tashi, zuciyar shi ce ta ci gaba da bugawa, bai gaji da ganin ta ba, in ta tafi baisan yadda zaiyi ba,

Da yaga nabila na shirin bud'e k'ofa yayi sauri ya sauke idanunshi daga kallan samira da suke, ta na shiga ta wage mishi hak'ora, yana jiran tayi mishi magana kawai yaji tace "subhanallah" sannan ta bud'e murfin motar ta k'ara fita, binta yayi da kallo yaga tayi wurin samira da ta bud'e gaban motar ta tana faman tab'e tab'e da alamar motar tak'i tashi,

Idannun abudulshakur na kan k'awaye biyun da suke ta faman magana, can yaga samira ta girgiza kanta, nabila ce ta k'ara mata wata maganar, ita kuma tayi kamar tana nazarin wani abu, sannan ta sauk'e gaban motar, zuwa tayi ta bud'e bayan motar tata ta dauko jakar ta had'e da kulle motar, sannan ita da nabila suka fara tawowa zuwa inda motar shi take,

shi kuwa yana ganin haka dad'i da farin ciki suka kamashi, kenan motar shi zata hau ya kaita gida, yana gani sun kusa k'arasowa inda yake, yayi saurin d'auka wayar shi ya shiga danna wa, ya tumke fuskar shi kamar bai t'aba dariya ba, amma a k'asan ranshi sai farin ciki yake,

nabila ce ta d'anyi knocking window dinshi, sauke glass din yayi tare da zuba mata way'annan manyan idanun nashi,

"dan Allah if you don't mind zamu ajiye k'awata a gida, motar ta ta samu matsala"

Abdulshakur najin haka yakai duban shi da samira aiko yana kallanta suka had'a ido, gaban shi ne ya k'ara mummunar fad'uwa zuciyarshi ta fara bugawa, sauri yayi ya kai dubanshi ga wayarshi ya cigaba da latsa ta, fuskar shi still a had'e take, yayi kamar bazai yi magana ba sai can kuma yace,

"ba napep ne a gari"

yana fad'an haka yayi sacen kallan samira, harrara yaga ta daka mishi, har da murgud'a mai baki sannan ta bud'e bakinta alamar ta fad'i wani abu a kasan ranta, shi ya tabbata zagin shi tayi,

Saurin ki'ris dariya ta sub'uce mishi amma ya dak'e, sai da yayi dariyar a cikin zuciyar shi, a duniya mata uku ke iya kallanshi suyi mishi abunda suka ga dama kuma baya iya ce musu komi, daga mamanshi sai yayyen shi, amma yanzu sun dawo hud'u samira ta shiga sahun su,

nabila ce ta k'ara cewa "kasan baza ta samu napep ba acikin school har sai ta fita gate, kuma da nisa sosai ga shi yanzu yanma tayi ko ta fita da wuya ta samu abun hawa"

daura hannun shi yayi akan habar shi kamar ba dashi tayi magana ba ya ci gaba da latsa wayar shi, kamar bazai yi magana ba can kuma yace,

"zata iya shiga"

Yana fad'an haka ya k'ara sacen kallan ta, k'ara daka mishi harara tayi, wani farin ciki mara misaltuwa ne ya kamashi, gaskiya tana da babban matsayi a rayuwar shi, kallonta kawai ya saka shi nishad'i, ya manta rabun da yayi farin ciki irin wannan, Maybe tun ran da samira ta aiko mishi da text dinnan,

yana ji sun gama shiga, ya kunna motar shi sannan ya k'ara gaba zuciyar shi cike da anushuwa da farin ciki.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now