Chapter twenty-eight

1.4K 170 1
                                    

Samira ce tafito tour d'in gidan, shiga ko wane b'angare take dan ta kashe kwarkwatar idanun ta, bayan ta gama shan kallo wajan pool area kawai ta nufi wani b'angare wato garden area, sakar bakin tayi ta dunk'a zuba kallo, abun na bata mamaki yadda wasu mutannan ke yin abu kamar baza su mutu ba, d'aga kanta tayi ta kalli saman gidan, ko shi wace duniyar aka zuba mishi oho,

Juyawa tayi zata koma ciki kawai ta hango wani kamar mutum a zaune, k'ara d'an matsawa tayi, sama mutumin yake kallo amma da alama idanunshi a lumshe suke, k'ara k'ura ma wajan idanun tayi, ji tayi gaban ta yayi mummunar fad'uwa, zuciyarta da fara bugawa, abdulshakur ne a zaune a wurin,

Samira ta kasa motsawa, kawai ta zuba mishi idanu sai kallon shi take, wani irin abu take ji yana sokar zuciyar ta, so take ta matsa ta kama gabanta amma ta kasa, kallon shi kawai take yi ko k'ifta idanta bata yi, fuskar shi tana nuna alamun nustuwa, Kardai bacci yake yi a haka, murmushi samira ta saki, wani irin farin ciki ne ya saukar mata, bata san daga ina ba, an d'an k'ankanin lokaci fuskarta ta zama d'auke da anushuwa,

Haka tayi ta zuba mishi kallo tana murmushi bata ma san mintuna nawa tayi tsaye a wajan ba, gani tayi kamar ya fara motsi zai bud'e idanun shi, sauri tayi ta samu wani d'an wuri ta lab'e, k'irjinta ta dafa tsabar bugawar da yake, sai a lokacin abunda tayi ya zo mata, sauri tayi da d'aya hannunta ta toshe bakin ta tare da zaro manyan idanunta waje,

Waige waige ta fara ko wani ya ganta, wata irin ajiyar zuciya tayi da taga wurin wayam ba kowa, hannayanta biyu ta samu ta fara dukan fuskarta,

Samira gaskiya baki da hankali da yanzu wani ya ganki fa? sai kice mishi mene?

Tayi maganar a zuci, wani irin haushin kanta take ji, ina alkwarin da tayi wa kanta na zata fitar dashi daga cikin zuciyar ta, me yasa tazo wannan trip d'in ma? Ba duk dan ta samu wani ibin shi bane ta samu ta cire shi daga rayuwarta ta sauki, amma yanzu daga ganin shi gaba d'aya ta wani susuce kamar bata tab'a ganin namiji a rayuwarta ba, ji tayi kamar ta rufe kanta da duka,

da rashin kwarin jiki ta fara tafiya sum sum sum ta bar wurin.

Tana shiga side d'insu ta wuce d'akin su da nabila, taga har ta fito daga wanka tana sallah, itama cire kayan jikin ta tayi sannan tayi bathroom, sai da ta gama wankan tsab sannan ta fito, towel d'inta a jikinata da wani daure a kanta, ko da ta fito bata tarar da nabila a d'akin ba, wajan wata bag ta nifa da tazo da ita had'e da akwatin ta, bud'e wa tayi ta d'auki dryer d'inta sannan ta nufi dressing mirror,

Shiryawa ta fara yi a niste, sai da ta gama shafa muyukanta sannan ta k'ara koma wa wajan akwatin ta ta sauke ta d'auko wata doguwar rigar mara nauyi ta saka bayan ta saka undies d'inta, hijab da dauko tayi sallah sai da ta gama tsab har addu'a tayi Allah ya cire mata abudulshakur taga ranta, sannan itama tayi hanyar waje.

Tana fita pallor taga matan dukkan su sun fito, kowa yayi wankan suna zaune suna hira, farida ce ta ajiye wayarta, magana ta gama yi da khalifa sannan ta kalli sauran

"Khalifa yace in muka bud'e store a kitchen akwai food stuff sun ajiye mana kawai girki zamuyi wai dan Allah yunwa suke ji,"

Dariya sauran suka saki sannan suka mik'e sukayi kitchen, ai kuwa khalifa gaskiya ya fad'a da suka bud'e store d'in cike yake mak'il da kayan abinci ba abunda babu, suka bud'e fridge shima haka cike da drinks harda snacks da vegetables nan suka bar bazu, wasu suka fara girki wasu suka fara setting dinning table daman irin family dinning d'innan ne zai iya d'aukar su gaba d'aya, wasu kuma suka fara suya snacks, kan kice mene sun gama daman ba wani abincin zafi sukayi ba, shinkafa da miya ne sai kuma potato salad,

Haka suka zuba abincin a flasks suma flasks d'in abun kallo ne, sannan suka baza su akan dinning,

Farida ce t d'auki wayarta ta kira khalifa ta sanarda shi sun gama, sauran sumun wuri sukayi suka zauna jiran mazan.

$$$$$$$$$$$

Zaune suke a cikin parlor suma bayan abdulshakur ya gama jan su jam'in sallar azahar, wayar khalifa ce tayi ringing duk ta katse musu abun da suke yi, daukan wayar yayi ya amsa can kuma ya kashe, duban abokan nashi yayi yace musu,

"Abinci ya sauka mu kawai ake jira, sunce sun shirya komi a side d'insu," ai kan ya kai ayar zancen sa su al-ameen da nasir har sun mike,  Mubarak ne ya kalle su,

"Sarakan ci, ko d'an ajinan baza kuyi ba"

Al-ameen da nasir suka kalli juna

"Kai dan Allah a ina ka tab'a ji anyi ma abinci jan aji iye?" Nasir ya fad'a

Abudulshakur fashe wa yayi da dariya,  ya nuna su da d'an yatsan hannun shi,

"Ku biyu ko, in har ana so aga zalamar ku to a ambaci abinci"

Khalifa ne ya mik'e sannan yace musu kawai su tafi kada su barsu suna jira, haka ko wannan su ya mik'e amma banda abdulshakur da yake faman danna waya bashi da alamar tashi,

Gaba d'aya zuba mishi ido sukayi, shahid ne ya fara cewa

"Kai baza ka taho bane ko dai azumi kake" ya tambaye shi,

Abdulshakur girgiza kai yayi alamun a'a sannan yace musu "kuje zan taho ai nasan hanya" ko da yayi maganar bai dauk'e idanunshi daga kallan wayar da suke ba,

Kamar dai zasu ce wani abun can kuma suka k'ale shi sukayi tafiyar su dan sun san halinshi sarai.

Yana jin almun ba kowa a pallor d'in yayi wata irin ajiyar zuciya, jingina kanshi yayi da kujera dake jingina a bayan shi sannan ya lumshe idanun shi,

So yake ya tattaro dukan nutsuwar shi kafin ya hallara a wajan, tuna wa yayi da d'azu da yake zaune a cikin garden d'in, tabbas yaji idanu akan shi amma da ya bud'e bai ga kowa ba, ko giftawar wani, ya san tabbas kallon shi akai amma bai san wane ba, ko dai nabila ce ta fara saka mishi k'ahon takura, sam sam bai kawo Samira ba saboda itace mace ta k'arshe a ganin shi da zata yi wannnan abun,

K'ara tunawa yayi lokacin da ya dawo d'akin shi bayan ya buga wa abokan shi wannan k'ofa, Al-ameen, Ismail da khalifa sai da suk shigo tuhumar shi me yasa yayi hakan, ko dai akwai wani abunda da ke damun shi, saboda kwana biyu gaba d'aya ya canza, ga ya rame, bayan kai lefan khalifa kullum suka kira shi su had'u sai ya basu uziri in banda jiya da yaje, Ismail shima kasa daure wa yayi yace, mishi ko amra sai da ta kira ta tambaye shi in ya gaya musu wani abun saboda hankalin mommy da daddy a tashe yake,

Abdulshakur kallon su yayi yai murmushi, baza su tab'a ganewa ba in har ya gaya musu sai ya zama abun tsokana saboda ya bala'in sanin halin su, kuma ya sani sarai duk acikin su ba wanda yake soyayya ba wanda ya tab'a ta saboda dukan su players ne, ko khalifa ya tabbata baya ji da farida a zuciyar shi kamar yadda yake ji da samira, a ganinshi ko kwatan abun da yake ji baya ji dukda kullum sai ya gaya mishi yadda yake san farida,

SO, ya dad'e baiga abunda ya tsana, yak'e ki a rayuwar shi ba kamar shi ba, me yasa zuciyar shi bata ne mi zab'in shi ba ko ta nemi shawarar shi, taje takai kanta inda aka fi k'arfinta,

da shi ne yake da zab'i bazai tab'a saka ta a rayuwar shi ba, bazai tab'a tunkarar kanshi wurin ba, bazai tab'a kai zuciyar shi inda kullum sai tayi kuka tayi rad'ad'i uwa uba ciwo,

Sa hannu yayi ya dafe k'irjin shi, shi kuwa da zai iya sai ya cire zuciyar shi ya jefar saboda ya gaji da wannan azabar da wuyar da take bashi,

Haka yayi d'an raina musu hankali sannan ya samu suka k'alle shi suka kama gaban su.

bayan ya jima a haka da hannu shi akan k'irjin shi, can kuma ya mik'e yayi hanyar k'ofar da zata had'a shi da sashan su samira.

(Wallahi nayi tafiya amma haka na samu na muku typing, Allah yasa chapter d'in tayi muku dad'i)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now