Chapter fifty-one

1.6K 208 9
                                    

Kangon ya cika mak'il da hayak'in shaye shaye, y'an daban suna can a zaune sun saka kayan maye a gaba suna ta d'urawa a cikin, gaba d'ayan su basa cikin hankalin su,,

Samira kuwa har ta gaji da kuka, tayi shiru a wurin, ba abunda take in ba addu'a ba da yin hadda qur'anin ta, jira kawai take suzo suyi mata abunda suke ga dama, ta rugada ta rugumi k'addararta, abu d'aya kawai take dana sani a rayuwarta, rashin gaya wa Abdulshakur tana sanshi, dama zata iya k'ara ganin shi a duniya, in har ta samu ta k'ub'uce daga hannun mugayen mutanen nan dukda tasan abu ne me wuya, tayi al-k'awarin baza tab'a bari ya s'ub'uce daga hannunta ba, zata ruk'e shi ta kama shi gam gam yadda ba wani abunda zai sake raba su ko ya shiga tsakanin su, hawaye ne suka dawo zuba a fuskarta,

"Oga oga"

Muryar wannan d'ayan taji wanda ya mik'owa ma ogan nasu (me suna blade) waya lokacin da za tayi magana da nabila, nabila bama tasan yin tunanin ta, Girgiza kanta tayi ta k'ara d'aga ido ta ganshi ya ruk'o wuyan rigar wani yaro k'arami wanda baifi shekaru sha takwas ba, ko wane hali ne ya saka shi shiga cikin irin wannan rayuwar, gani tayi ya cilla shi gaban ogan nasu wanda ya kame akan kujera yana busar sigari,

"wayar da kace ya cillar ta waccar matar ashe baiyi ba, kashe ta kawai yayi ya b'oye ta a cikin jikinshi, sai yanzu na kama shi a cikin kangon kusa ya kunna ta yana ta danne danne"

Cikin maganar shaye shaye yayi maganar samira ma da kyar ta iya gane me yake cewa, da taji an ambaci wayarta ji tayi kamar ta tashi ta wurta daga wurin su ta kira neman taimako, amma ba hali har yanzu tana k'ulle, ko salla sunk'i barinta tayi, ga yanzu tasan dare yayi sosai duk da bata san k'arfe nawa ba, kawai inda taji dad'i da har yanzu basu tab'a lafiyar jikinta ba, tasan in har suka tab'ata mutuwar wulaqancin da nabila ta fad'a zatayi zata tabbata, zaburar da ogan yayi ya mik'e ce ta bawa samira tsoro, ji tayi ya wan ke shi da wani wawan mari, ta tabbata in har ita ya mara da wannan jibgegan hannun nashi sai ta sume,

"Kai baka da hankali ne, kasan hatsarin abunda kayi, yanzu in har sukayi tracking wayar fa kashin mu ya bushe"

Tsabar yadda yake tsawa tare da maganar ya saka samira had'e jikinta wurin d'aya tare ta langwab'ewa a jikin bango, dan k'atuwar muryarshi abun tsoro ce, in har ka ganta a wurin da koma abun tausayi, ba d'ankwali akanta balle takalmi, rigar ta tayi bud'u bud'u da k'ura, d'ayan ne ya k'ara cewa,

"Banji wayar ta dad'e a kunan harda zai saka su su gano inda muke"

Blade ne ya kalle shi tare da zuk'ar sigari, sai da ya cika bakinshi da hancin shi da hayak'inta sannan ya busar had'e da cewa,

"Ka tabbata?"

D'aga mishi kai yayi, blade ce mishi yayi a yaje ya hukunta yaron dan yayi babban laifi, haka ya k'ara jan yaran wanda yake ta faman kuka yana bada hak'uri a lokacin wani ya sake k'arasowa wurin ya rad'awa ogan nasu wani abu, juyowa yayi ya kalli samira tare da sakin dariya,

"Inajin wanda muke jira ya k'araso"

Gaban samira ne yayi mummunar fad'uwa wa, hantar cikinta ce ta kad'a tsoro ya sake kamata, gani tayi kowa na d'akin ya juya ya fita harta ogan nasu blade, haba jikin Samira ya fara rawa, gaba d'aya ta rikice addu'a ta ci gaba da yi a ranta tare da sunkuyar da kanta k'asa dan bata san ganin wane zai shigo,

"Well, well, look who we have here"

Ismail, abunda tace a ranta kenan saurin d'aga kanta tayi dan ta tabbatar ko shine, tana d'aga kanta kuwa ta ganshi a ga banta yana sakar mata murmushi, zuciyar ta ce ta sake mahaukacin bugawa, shikenan tata ta k'are, wannan la'anan nan ne daman, dad'in da take ji zata mutu cikin mutuncin ta gaba d'aya ya rushe tasan tsinan nan bazai tab'a kyeleta ba, hawaye ne suke sake zubawo daga idanunta, gani tayi ya d'auko kujerar da take kwali d'aya a wajan ya saka a gabanta ya zauna tare da hard'a k'afa, samira k'ara matsawa tayi a jikin bango ta k'ara shigewa ga tsoro da ya cika idanunta da fuskar ta,

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now