Chapter eighteen

1.6K 164 8
                                    

Bada ban baza ta samu abun hawa da wuri ba da ba abunda zai saka ta shiga motar shi, ka ita tata motar bata tashi bata matsala ba sai yau, abun ya bata haushi har sai da ta aika wada motar zagi a k'asan ranta,

Taga yana wani had'e girar sama da ta k'asa kamar baya so ta shiga motar sa, to itama ai bata so ta shiga badan dole ta saka ta ba, shi yasa ma tana shiga motar ta saka earpiece tsabar tak'ai ci, da haushin shi da take ji, ga bata san jin muryar shi, danna wayar ta take tunda ta shiga motar bama ta so ta d'aga kai su had'a ido ta rear-view mirror din motar.

Nabila kad'ai ki magana a motar, baya cewa komai ko ta had'a dashi a cikin zancen ta, wani irin haushin aminyar tata take, duk tabi ta zama wawiya akan namiji da ko kallo bata ishe shi ba, ya wani had'e fuska tunda suka shiga motar, ji yake ba kamar shi a duniya, wani dogon tsaki ta sake jaa a k'asan ranta ta ci gaba da jin wak'ar ta da danna wayar ta.

Ji tayi an tab'a ta, sauri tayi ta cire earpiece din dake kunnan ta sannan takai dubanta ga nabila dake ce mata

"Tun d'azu nake miki magana baki ji ba kin wani saka earpiece, nace bakya jin yunwa?" ta k'arasa maganar da maimaita abunda tace a baya

Samira murmushi tayi mata "ko ina jin yunwa, yanzu dare yayi to 6 fa, kawai ku ajiye ni a gida in naje naci abincin"

Juyawa nabila tayi alamar zata ma abdulshakur magana, samira na ganin haka ta maida earpiece dinta kunnan ta, ta ci gaba da abunda take, ta tabbata in dai har takai duban ta zuwa ga shi harara zata daka mishi ta rear view mirror din motar

Ta dauka gida zasu ajiye ta amma tana daga idanta taga sunyi parking a wajan eat & dine, wani had'addan restaurant a kano wanda sai wane da wane be ke zuwa, da sauri ta cire earpiece sannan ta kalli nabila, da itama kallanta take tayi narai narai da ido,

"Na gaya mishi zamu ci abinci in munje gida yace bega amfanin hakan ba tunda muna kan hanyar eat & dine, kawai mu tsaya, kuma kinsa ni bazan tab'a iya ce mishi a'a ba"

Samira wata harara ta daka mata, sannnan ta kalli driver's seat taga abudulshakur baya nan, ko yaushe ma ya fita daga motar bata sani ba oho, ta dage sai danna waya take, mai da idonta tayi kan nabila,

"Kinsan period nake, kuma banyi changing ba tun dazu, kinfi kowa sanin yadda nake zuba in inayi, so nake kawai inje gida inyi wanka, gaskiya zan hau napep daga nan, ku kuje kawai"

tana gama fad'a tayi shirin bud'e mota ta fita, nabila tayi saurin kamo hannunta,

"Baza mu dad'e ba insha Allah, in har kika tafi bazai ji dad'i ba, kuma ni bana son abunda zai b'ata mishi rai ga nasan zaki dade kan ki sami napep a wurin nan" tayi mata fuskar tausayi,

K'ara jin wani haushin k'awartata ya kama ta, to an gaya miki na damu da abunda zai faranta mai rai ko b'ata mishi ne iye, baya gabana samira ta fad'a acikin ranta, amma a zahiri taga kamar zasu sami matsala da nabila indai bata yarda ta tsaya ba sai tace mata

"Tom naji, amma in naga zai daukar mana lokaci gaskiya zan hau napep na tafi"

Aminyar tata ta saki wani murmushi
"Yauwa bestfriend, shi yasa nake sanki" ta fad'a had'e da bud'e k'ofa dan ta fita,

haka suka fito suka fara takawa cikin restaurant din, hannun su ruk'e da juna suna murmushi.

$$$$$$$$$

Abdulshakur tsaye yake acikin wurin amma dubanshi na wajan motarsa, addu'a yake tayi a cikin ransa Allah yasa samira ta tsaya kada tace zata tafi dan wallahi bai gaji da ganinta ba,

fuskar shi ya had'e sosai  saboda tunda ya shigo wurin mutane ke ta kallan shi sun zuba mai ido kamar zasu cinye shi, shi yasa ya tsani zuwa public wurare,

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now