Chapter ten

1.6K 162 0
                                    

Su samira baje a cikin parlor an gama cin abinci ana ta hira mama da dawo, sai dariya suke ci a wurin gwaggo da ta dage sai basu labari take, ya muazzam da ya sadiq suma suna gefe sai tasu dariyar suke, bayan hirar ta d'an lafa, mama ce ta kalli samira "wai ina nabila ne?, na dauka ai zata zo tarb'a ta" samira jin wuta ta dauke mata tayi, daman tun sanda mama ta shigo take addu'a Allah yasa baza ta tambaye ta nabila ba, da taga maman tana hira shine ta saki ranta da dauka ta manta, mama ta ci gaba da kallan samira tana jiran amsar ta gwaggo ma ita take kallo saboda jikin ta ya bata anya ba wani abu ne ya hada su ba? Kusan sati samira bata ce zata gidan su ba haka ma nabila bata zo ba, kuma tasan basu saba haka ba, da samira taga dai jiran ta suke ta basu amsa tace

"lah ban gaya miki ba?, kinsan tunda hutun mid semester muke sunyi tafiya ita da umma Lagos yin wata siyayya"

mama ta dan kalle ta amma bata ai yana komi a ranta ba

"oh Allah sarki, nifa ince, abun ya bana mamaki da ban ganta ba"

M samira murmushin yak'e tayi sannan tayi saurin canza zancen, ai kuwa aka kama wata hirar, can wajan karfe tara su ya murjanatu suka yi shirin tafiya, hadda iman za'a tafi an gama yaye ga daman samira nan da kwana biyu zata koma makaranta. Bayan kowa ya watse mama itama tayi dakin ta samira itama nata dakin tayi da tunanin an kusa koma wa makaranta dole ta had'u da nabila ko taki ko taso.

Kwance yake a kan gado, ya kafa ma silin din dakin shi ido, kallon sillin din yake amma wani tunani yake yi daban, wayan shi na rik'e a hannun shi, ya dan jima a haka, can kuma ya dauki hab'ar hannun shi ya dora a saman fuskan shi tare da lumshe idanunshi, har yanzu kanshi namai ciwo, a yadda yake yanzu baya jin zai iya yin wani bacci, bayan gaba d'aya jikin shi yana sanar dashi ya kamata ya huta, yana haka zuciyar shi ta ce mishi, to kai ka kirata mana, jin gaban shi ya fad'i yayi, yau ina jan ajin nashi yaje ne? Wai shine yake tunanin kiran wata mace, abunda bai tab'a yi a rayuwar shi ba tunda uwarshi ta haifi shi in banda yayyen shi da k'annan shi sai kuma mommy, zuciyar ce ta k'ara sanar da shi, in har baka ji muryar ta ba kasan baza ka sami nutsuwar da kake so ba, Abdulshakur tashi yayi da sauri daga kan gadon, har sai dai yadan ji jiri ya kama shi, sa hannuwan shi yayi ya ruk'e kanshi tare da girgiza kan da k'arfi wai ko ya sami saukin tunanin da yake, wani takai ci da haushin kanshi ya ji ya rufe shi, ya kawai fita yabar dakin in ba haka ba zai iya aikata aikin da na sani, haka ya fice tare da jefa wayan shi kan gado yayi pallor dinshi, yana zuwa ya dauki remote ya kunna tv ya sami wuri a kan kujera ya zauna, Allah ya taimake shi yau friday gobe weekend bazai je aiki ba da kuwa har mai aikatan shi sai sun gane akwai abunda yake damun shi, kallo yake yi amma kuma hankalin shi baya kan wurin, fuskar samira kawai yake kallo, yadda take murmushi har wushiryar ta sai ta fito, da manyan idanun ta, ita ba wani kyau ba, me yasa duk ta addabi rayuwar shi ne, ita ba irin matan da yake so ba, ko kusa ma, shi da yake san mata farare k'al masu dogon hanchi, da dan jiki, way'anda ko Ina din su ya cika dam masu dan ka'aramin baki, zuciyar shi ce ta k'ara gaya mai, saboda ita ce mace ta farko da tayi treating dinka haka, tuna abunda ta ce mishi a wajan wellcare yayi "sai kuma ka yi" har full lips dinta sai da suka d'an kumburo kamar tana pouting, Abdulshakur wani murmushi ya saka da bai ma san yayi ba, k'ara tuna yadda ta ajiye mishi mouthwash din cikin basket dinshi, kuma alokacin ko juya wa ba tayi ta kalle shi ba, tayi mishi kamar shi ba kowa bane, kara sakar wani murmushin yayi, wai shi ne mace tayi wa haka, wai shi Abdulshakur Yusuf Ashaka mace tayi wa haka, sai kuma can ya had'e fuska, abunne ya k'ara bashi haushi, da ya tuna duk wannan abun da yake ko sunanta bai sani ba, wani dogon tasaki ya ja tare da yin hanyar waje dan zuwa side din mommy, ya gwammace da yaje yayi hira da amal da amra da ya zauna yin wad'annan tunanin.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now