Chapter nineteen

1.4K 173 0
                                    

Abdulshakur driving yake amma gaban shi sai bugawa yake, samira na front seat a motar shi, dad'i da farin ciki duk sun addabe shi dukda har lokacin yana d'an jin haushin ta tsayawa zancen da tayi da wannan yaran, sam a fili be nuna farin cikin shi ba, fuskar shi had'e yadda yake a ko yaushe, tunda suka bar gidan su nabila ya fara tuk'i be juya ya kalli inda samira take a zaune saboda in har ya juya ya ga gata, gashi, zai iya yin komi,

Duk abun nan da yake yana kallanta ta gefan idanshi, tana ta motsi ta kasa zama guri d'aya, ya tabbata yana d'aya daga cikin abubuwan da suka hanata sukuni a cikin motar, shi dai farin ciki yake yi sosai a cikin zuciyar shi, yanzu ya gane yadda zai dunk'a saka samirar shi a idanunsa, yayi alkwarin kullum sai yazo ya dauk'i nabila a makaranta kawai saboda ita, wani murmushi ya sake saka acikin ranshi,

K'ara kallan samira yayi ta gefan idan shi, sannan yayi shirin yi mata magana

"Zaki gaya mun inane gidan ku, ko zaki bari muyi ta tafiya a titi ne"

(Kunji shi, yana yi kamar bai saka usman ya nemo mishi inda gidan su yake ba)

Yanzu juyawa sosai yayi yakai dubanshi ga samira, wacce duk da alamun a matse take da k'ago taje gida, yana kallanta yaga yadda suke kusa da juna yaji k'irjin shi yayi wani irin bugawa, samira bashi take kallo ba gaba d'aya idanunta na k'asa, k'ura mata idanu yayi, kawai yaga hawaye na zuba daga idanunta,

Abdulshakur, a take ya shiga cikin wani yanayi, me akai mata take kuka, me yasa take zubar da hawayen ta, shi yasan lafiya k'alau ta shiga mota bayan sun sauke nabila, cikin tashin hankali baisan lokacin da ya samu wuri yayi parking motar shi, har alokacin samira bata d'ago da kanta ba, hannun shi rawa ya fara, gashi ya saka manta wannan manyan idanun nashi sai kallanta yake,

Sai da yan d'an nutsu, sannan ya sa hanunushi ya d'ago  fuskarta a hankali, juyowa yayi da fuskar ta ya zamana fuskar ta na kallanshi, amma duka idanun ta kulle suke, sai hawayen da yake ta kwarara, yanzu gaba d'aya jikin abudulshakur rawa yake, ji yake kamar ana soka mishi wuk'a acikin zuciyar shi, wani irin zafi da rad'ad'i yake ji, bai daina kallan samira ba da take ta faman hawaye ta k'ame idanunta kamar ma batasan abunda yake yi ba,

Kamo hannayenta yayi masu laushi guda biyun ya saka acikin nashi da ke ta faman rawa, sannan yayi magana a cikin muryar da shi kanshi baisan yana da ita ba, a hankali ya fara ce mata

"Menene kike kuka?, me aka miki?, dan Allah ki daina zubar da hawayen ki, ki gaya mun me aka miki" yayi dukan maganar a lokaci d'aya

Har lokacin samira bata bud'e idanunta ba, hawaye ne ke ta zuba ta kasa controlling dinsu, abdulshakur har a lokacin ya kwura mata manyan idanunshi ta suka canza ta farar d'aya sunyi jaa, ko k'iftasu baya yi, in har ka kalleshi zakayi zatan shima kukan yake yi tsabar tashin hankalin da yake ciki, da yaga tana zubar da hawayenta gwanda a saka shi a d'aki amishi duka, yadda ya tsani mutuwar shi haka ya tsani ya ganta tana kuka

da yaji shiru bata da niyar yi mishi magana, ya k'ara matse hannuwanta a cikin nashi ya fara shafa su a hankali, har alokacin kallan samira yake taki daina kuka,

Sunfi minti biyar a haka, ba wanda yace ma kowa komi, zuciyar abdulshakur ba abinda take yi sai zugi da bugawa, shi kad'ai yasan mai yake ji,

Bai ankara ba yaji ta fisge hannun ta dake cikin nashi hannun, sannan ta fara share hawayenta, duk abunda take yi yana kallanta.

$$$$$$$$$$$$

Tunda ta gane tayi staining a jikin ta ta shiga wani irin tashin hankali, da ah motar ta tayi bazai tab'a damun ta ba, amma tsabar abun kunya a motar wani k'ato, saurayin aminyar ta wanda  tafi tsana a duk duniya, samira batasan lokacin da ta fara kuka ba, tashin hankalinta shine ace ta b'ata har motar shi,

Hawaye ne ke kawai zuba a fuskar ta, yanzu ya zatayi, in har ta tashi daga inda take to tabbas sai ya gane, ga seats din motar cream color, wani sababbin hawayen ne suka k'ara zuba, haka tayi ta kuka ta ma kasa bud'e idonta tsoron kada ta had'a ido dashi, da k'yar ta iya tattara nutsuwar ta sannan a hankali ta bude idanunta,

Kicibis tayi da idanun abudulshakur da ke mata wani irin kallo da ta kasa gane ma'anar shi, idanshi yayi jaa, manyan idanunshi sun k'ara fitowa waje, gabanta ne ya fara harbawa, zuciyar ta ta fara bugawa, idanunta ya sauke a kan hannuta way'anda suke cikin na nashi, ga banta da yake ta faman bugawa,

Me yasa yake ruk'e da hannunta? me yasa yake kallanta haka? kallon da yake mata duk ya sagan mata da gwiwoyi dukada a zaune take, irin wannan kallan yake ma y'ammata? shi yasa suke hauka a kanshi? me yasa take ganin tashin hankali a cikin kwayar idanunshi? Dan Allah ya daina kallanta haka, sawa yake zuciyar ta tana mata zafi,

Samira ce tayi firgit ta kwace hanyanta dake cikin nashi, tayi saurin goge kwallar idanunta, ta gama duk abunda take tsab amma har lokacin tanajin idannushi na kallanta,

"A rijiyar zaki nake, in munje zan k'arasa yi maka kwatance" ta fad'i maganar a sanyaye

Tana jira ko zai bar kallonta ya fara tuk'i tunda ta gaya mishi inda zasu je, amma ina kallonta ya ci gaba dayi, jikin samira rawa ya fara da taga kallon yayi yawa kawai ta fara wasa da yatsun hannunta, addu'a ta fara yi acikin ranta, Allah yayi mata tsari da abdulshakur kada taje ta fad'a sahun sauran mata,

Ji tayi yayi wata irin ajiyar zuciya, sannan ya kunna mota ya fara tuk'i, har lokacin idanunta na kan hanayenta da suke wasa da juna, shiru cikin motar ba wanda yace ma kowa komi har tsawan minti uku,

A hankali ta d'an d'aga idanunta ta kalle shi, hannayen shi taga ni sun rik'e wheel din motar gam gam har jijiyoyin hannuwan shi tana gani, sauri tayi ta kwada kanta, motar shiru har suka isa unguwar su,

Suna shiga ta fara mishi kwatance, yana jinta kuwa yanayin duk inda tace yayi amma ko d'aya bai juyo ya kalle ta ba balle ya bude bakin shi yayi mata magana ba,

Sai da suka isa k'ofar gidan su samira ya sami wuri yayi parking, shiru ta kasa fita daga motar saboda tsoro da kunya da take ji,

Sai can, a hankali ta juya ta kalle shi,

"In rok'e wata alfarma?, dan Allah zaka iya fita daga motar nan na wasu y'an mintuna kad'an" tayi maganar itama a hankali,

A zaton ta, zai juyo ya balbale ta da masifa ko ya gaya mata wata magana ma zafi, kawai sai ya bata mamaki, gani tayi ya bud'e motar ya fita bai dai ce mata komi ba, sannan ta gani ya matsa can daga wurin motar,

Samira sakar baki tayi ta bishi da kallo, anya wannan abdulshakur ne kuwa, gaba d'aya ya canza daga wanda ta sani kamar wata hawainiya, kodai yana da mutanen b'oye? Ta k'ara kai dubanta tagan shi har ya fara waya bayan shi ne ke kallanta,

Ai kuwa tana ganin haka tayi sauri ta dauki wayar ta ta kira safiya, tana dauka ta fara fad'a mata ta fito mata da hijab, ta k'ada omo da ruwa a bowl da dryer yanzu yanzun nan tana waje

Ba'ayi minti biyu ba sai ga safiya, samira na k'ara duba abdulshakur taga har lokacin yana waya hankalinshi gaba d'aya baya wurin ta, wani dadi ne ya kamata, bud'e murfin motar tayi tama safiya nuni tayi sauri,

Safiya na k'arsowa ta kwace hijab din ta saka sannan ta mike daga inda take a kan kujera, ai kuwa tayi staining dinta itama, amma k'ad'an ne, ruwan nan da omo ta saka, ta dauko tissue ta goge, duk abinda take safiya ta saki baki tana kallanta, samira kuwa bata ni ta kanta ba sai dirzar kujera take, sai da taga ya fita sannan ta k'arbi dryer daga wurin safiya ta kunna ta saka akan kujerar kan kice me wuri ya bushe, samira murna fal cikin ta, sai da ta tabbata komai ya dawo normal sannan ta kulle k'ofar motar ta saki murmushi,

kallan inda abdulshakur yake tayi, har lokacin yana waya, k'arasawa tayi inda yake sannan tayi geran murya, juyawa yayi inda yaji muryar ya sauke mata manyan idanunshi, samira murmushi tayi mishi sannan tace zata wuce ciki ta gode sosai da sosai, kan yayi mata wata magana har ta kusa kaiwa gida ita da safiya.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now