Chapter thirty-nine

1.5K 184 5
                                    

Shirya wa yake cikin wani gray jeans da white shirt, a masifaffan gajiye yake tunda basu fi awa biyu daga dawowa daga airport ba, ga kwana biyu kenan baya samun bacci shi kanshi baisan taya ya yake functioning ba, so yake ya huta amma ya zai yi, ya rigada yayi ma zayyan alk'awarin zai had'a shi da wani business partner dinshi wanda yazo nigeria kuma yau zai koma k'asan su flight d'in dare, da badan usman ya siyo mishi sabuwar waya ya ajiye mishi a gida da bama zai san mutumin yau zai koma ba,

Bayan ya gama shirin shi tsab, sai ga zayyan ya fad'o d'akin, sai da ya d'an bama abdulshakur tsoro, kallanshi yayi ya daka mishi harara sannan ya ci gaba da abunda yake, zayyan shi kuwa samun wuri yayi ya zauna akan gado ya zuba ma abdulshakur kallo, shi kuwa baima bi ta kanshi ba, tun jiya bayan ya dawo daga gidan ya zainab abokan shi suka sashi a gaba, ba abunda suke in ba kallan shi ba, kamar suna so suyi mishi wata maganar amma ina ba halin yi, shi yasan maganar bata wuce ta Samira da ismail ba, sun san har lokacin ranshi a mutuk'ar bacce yake bayan yadda suka ga samira jiya ta bar lagos,

juya wa yayi ya kalli zayyan bayan ya gama feshi jikin shi da turararuka shi masu dad'in kamshi,

"Ka tashi muje in ka gama kare mun kallo, kasan meeting din nan da awa d'aya ne"

Yana maganar zayyan yayi zubar ya mik'e tare da zaro mukullin motarshi dan a motar shi zasu je, sannan ya k'ara kallan abdulshakur,

"Wai me yasa har mu sai kayi intimidating ne? Mu da muke friends dinka ka tsaya akan matan su kad'ai ka k'alle mu"

Abdulshakur k'ara dalla mishi harara yayi,

"Ni nace ku dinka ganin kwarjini na?"

Zayyan dariya ya saki tare da nuna ma Abdulshakur hanyar fita, suna fita compound din gidan wurin inda yayi parking suka had'u da mommy ta fito itama zata unguwa, zayyan har k'asa ya tsugunna ya gaishe ta, mommy ta amsa mishi da fara'a tare da saka musu albarka sannan itama tayi gaba abinta, suma shiga motar tasu sukayi dan suyi saurin isa wurin meeting d'in.


Motar zayyan pake take a harabar mak'eken asibitin nan me suna UMC, abdulshakur na gaban motar shi idanunshi nakan wayar dake hannunshi, basu dade da dawowa daga meeting d'innan ba, Allah kuwa ya basu nasara mutumin yayi accepting deal din, yasan abdulshakur ya k'osa ya koma gida amma babanshi ya saka shi a gaba sai yazo ya k'arbi magani a wurin wani cousin d'insu dake aiki a asibitin, shine kad'ai mutumin da yayarda ya siya mishi magani, yanzu dai yayi wa Haisam waya yana jiran yazo ya kawo magungunan,

Kallon Abdulshakur yayi, ya fara mishi magana

"I cannot believe ka cillar da wayar ka iphone 11 pro max saboda kawai kace mun dame ka da kira"

Abdulshakur dake aikin replying emails dinshi yayi kamar bazai amsa ba, can kuma yace,

"To kuna ta kira na nonstop kai da sauran bayan I was trying to focus-"

Bai k'arasa maganar ba zayyan yayi saurin katse shi,

"Focus on what??? Samira???" Yayi tambayar tare da shekewa da dariya

Abdulshakur da idanunshi nakan wayar shi yayi saurin d'aguwa ya dallama zayyan harara

"I was trying to focus on driving" yayi maganar ta cikin hak'oranshi kamar zai kaima abokin nashi duka,

Zayyan me yake in ba dariya ba, sai da yayi mai isar sanna ya kuma kallan abdulshakur wanda ba aikin da yake in ba na aika mishi da harara ba,

"Let me tell, you're not as expressionless as you think you are, kowa ya ganka yasan kana santa, it's all over your face" ya nuna fuskar abdulshakur,

Abdulshakur wani dogan tsaki yaja ya juya ya maida idanshi kan wayar shi, zayyan ya fara bashi haushi, yana ta ambatar Samira baisan fushi yake da ita ba, sosai ta b'ata mishi rai jiya shi yasa baima bi ta kanta ba ko da k'wayen ta suka fito mata rakiya, yana gani ta shiga motar khalifa ita da farida da yake suma sun fito harabar gidan, ko kallon inda take baiyi ba, yana da saukin kai amma in ka mishi ba daidai ba dole ya nuna maka ka mishi ba daidai ba,

Cigabawa yayi da latsa wayar shi ya ajiye tunanin Samira a gefe, ya kuma yi banza da zayyan da yake ta faman tsokanar shi,

"Tsaya waccar ba samira bace" zayyan ya fad'a, abdulshakur bai kula shi ba saboda a zatan shi iskanci abokin nashi ne, ji yayi ya k'ara da cewa "bata da lafiya ne naga an ruruk'eta"

Abdulshakur zubar yayi ya d'ago kanshi da yaji an ambaci rashin lafiya, ya kai idanunshi inda zayyan yake kallo, ai kuwa da gaske ne, samira ce da wani ya ruk'e ta, gabanshi ne yayi mummunar fad'uwa baisan lokacin da ya saki wayar shi ba ya fara shirin bud'e motar zai fito, zayyan ne yayi saurin kamo hannunshi, ya k'ura ma Abdulshakur ido, wanda yanzu hankalin shi ya fara tashi har ya fara canzawa,

"Ina zaka je??" Yayi saurin tambayar shi,

Abdulshakur da yayi mutuwar zaune ya kasa amsa mishi, kawai shima ya zuba mishi ido, zayyan da yaga bashi da lokacin amsa shi yayi sake hannunshi, yana saki kuwa abdulshakur ya fita da sauri zai yi cikin asibitin, gaba d'aya ya fara rikicewa, hankalin shi a tashe, zayyan shima bude murfin motar yayi yabi bayan abokin nashi,

Allah ya taimaka yana shiga cikin asibitin yayi arba da haisam ya fito kawo mush magani, shi kuwa abdulshakur ya tsaya a tsaya ya kafa ma Samira ido wacce take zaune a wata kujera a reception d'in kanta akan cinyoyinta wata a kusa da ita kana gani kasan kanwarta ce,

So yake ya motsa amma ya kasa, so yake ya isa wurin ya yaji me yake damunta, har ya fara takawa wata zuciyar tace mishi shi wane d'inta har da zai shiga cikin sha'anin ta, jan burki yayi ya k'ara tsayawa, tunawa yayi da wulaqancin da tayi mishi a lagos, juyawa yake so yayi ya komawa waje amma ya kasa saboda hankalin shi gaba d'aya ya tafi wurinta, ga zuciyar shi da take faman bugawa kamar zata tsagi daga kirjin shi,

Zayyan ne ya tab'a shi tare da mik'a mishi wayar shi da ya yarda a mota, ya fara shafa bayan abdulshakur wai koda zai d'an sashi samun nustuwa sannan ya fara magana,

"Kada ka damu na saka haisam ya duba ta he's the best doctor a asibitin nan I'm sure he will take good care of her"

Yana fad'a abdulshakur yayi ajiyar zuciya dukda har lokacin idanunshi nakan samira, shi kuwa zayyan ba abunda yake ai yana wa a ranshi irin san da abudulshakur ke mata, anya kuwa abokin shi ne, duk yabi ya fita hayyacin shi a y'an mintuna saboda kawai bata da lafiya, ko da kwana uku da suka wuce aka tare shi aka ce mishi zai so mace ko yayi hauka akan mace, mace kuma kamar samira wacce kwata kwata bata cikin jerin matan da abudulshakur yake kulawa da yayi mugun k'aryatawa, amma gashi yanzu komi a idanunsa yake gudana, ba labari aka bashi ba,

Haisam ne ya tunkaro su, yana isa ya mik'a ma abdulshakur hannu tare da yi mishi sallama, sai a lokacin ya bar duniyar tunanin da yake, ya mik'a mishi hannu shima,

"Zayyan yace mun an kawo budurwar ka, yanzu ita zan gani zaka tsaya for the result ko kuwa zaka tafi sai na kira ka" ya tambaye shi,

zayyan har ya bud'e baki zaiyi magana abdulshakur yayi saurin riga shi,

"A'a zan tsaya" yadda yayi maganar sai da ya bama su haisam dariya, banza yayi dasu ya sami wuri ya zauna, ya cigaba da kallan samira wacce har lokacin bata d'ago da kanta ba, yasan bama tasan yana wurin ba saboda gaba d'aya bata cikin hayyacin ta, ba ayi minti biyar ba sai ga wata nurse tayi wurin su ta misu wata maganar, yana gani suka mik'e wannan kanwartata da wani namiji suka k'ara ruk'eta, shima namiji suna kama wata k'ila wanta ne, haka ya ci gaba da zuba musu kallo har suka bace daga wurin,

Lumshe idanunshi yayi, dama zai iya dawo da cutar kanshi, zayyan ne ya k'ara tab'a shi yace mishi shi dai zai tafi dan yana da abun yi, abdulshakur d'aga mishi kai yayi alamun ba komi, yana tafiya shi kuma ya zaro wayar shi cikin aljihun shi yayi ma usman Waya da yaje gidan su ya kawo mishi mota, ya gaya mishi inda yake, yana kashewa ya zauna zaman jiran result.


(Daman zan daina iya dragging littafin nan, insha Allah na kusa gama shi.

Please vote and share ❤️)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now