"ai ni da naga inata kwada sallama ba'a amsa ba na zaci kana masallaci"

abudulshakur ya gyada kai hade da cewa

"kasan weekend shine ranar hutawa na, so in na fara bacci sai a hankali kaga dana koma bacci bayan sallar azahar ban tashi ba sai 3:30"

khalifa ya kwashe da dariya

"neman kudi wallahi is not easy, kasan maganar da nazo muyi?"

Abdulshakur ya dan zamu daga kan kujera tare da ba khalifa dukkan nutuswar shi

" ina sauraran ka, tunda ka cemun kana da maganar da kake so kayi dani ta waya face to face nasan koma menene it is very important to yanzu gaya mun I'm all ears"

khalifa yadan yi jum na sakwanni kadan hade da kura ma agogan dake manna a jikin bangwan parlor din ido sannan ya juyar ta kanshi ya hada ido da Abdulshakur sannan ya furta a hankali

"aure zan yi"

Abdulshakur be san sanda ya saki baki ba, me kunuwan shi suke jiye mishi?? aure fa yace, yasan khalifa a duk abokanan shi, shi ne player bai taba dating mace guda daya ba kuma inhar idon shi yakai kan macce in dai har tayi mishi to insha Allahu sai yayi dating dinta wani sa'in har wasa suke suce baza suyi aure ba sai sunyi 40, amma yau shine yazo mai da wannan maganar he is speechless, wane irin kyau ne da yarinyar da har tasa abokin shi haukace wa haka?, haka parlor din yayi tsit na tsawan minti uku basu ce da juna k'ala ba sai dai abudlshakur ya tsura ma khalifa wannan manyan idanun nashi ko kifata su baya yi, gaba daya hankalin shi nakan shi, khalifa ne ya gaji da shirun ya fara bude bakin sa danyin magana

"naga kayi shiru ka tsura mun ido, dan nace zanyi aure? most of friends din mu sunyi aure ba wai wani abu sabo bane"

Abdulshakur lumshe idanunu shi yayi hade da girgiza kai abun ne yayi mutakar bashi mamaki he is not going to lie, yace

"kawai abunne ya bani mamaki, nasan ka khalifa kuwa nasan halin ka amma me yasa kayi taking wannan decision din haka??"

can kuma yace " NO WAY kada kace mun kaima ka fola? da gaske kake kana santa"

khalifa dariya ya saki sosai dan abokin nashi yayi mugun bashing dariya, Abdulshakur ya saka ma kanshi cewa mata basa gaban shi tunda yasan shi bai taba dating ko wace mace ba in ba nabila ba, zai ma kira shi da dating?? saboda yasan abudulshakur baya san nabila yana kullata ne kawai saboda daddy dinshi amma sam sam bata gaban shi, ah ranshi yace duk randa SO zai tashi cafke abudulshakur bazai taba yi mishi da dadi ba, kuma yana ji ajikin shi irin su Abdulshakur ne mazan da basu iya san mace ba in dai har ya fara san wata to zai sha mutuk'ar wahala amma kuma baya fatan haka. Khalifa ya ci gaba da murmushi yana fadin

"kasan Allah randa zaka hadu da someone that is that special zaka kawai ji ajikan ka, sonta zaka yi tsakanin ka da Allah, zaka zamana me san duk wani farin cikinta kuma zaka zaman mai k'in duk wani bakin cikin ta, it's very different bazan iya misalta maka ba, da kanka zaka zo wata rana ka bani labari"

Abdulshakur sakar wata mahaukaciyar dariya yayi har da bugbuga kafa da yar kwalla a idon shi dariya yake yi sosai kamar zararre, khalifa kuwa sakar baki yayi ya bishi da kallo sai da yayi dariyar shi mai isar shi sannan ya kai kallan shi ga khalifa da har yanzu bakin shi a sake yake

"tunda mommy ta haife ni ban taba jin abun da ya bani dariya kamar wannan ba, wai ni abudulshakur ne zai so mace haka?? Kai baka ji ya maka wani iri a kunnan ka ba?, to indai har zanyi irinwannan soyyayar toh tabbas bada mutum zanyi ba saboda duk fadin duniyar nan harda larabawa banga kyakkyawar mace da zanyi ma irin wannan son ba"

Khalifa ya tabe baki

"kasan Allah da kafafun ka zaka zo ka bani labari ni kuma in time din yazo zance maka, I told you so"

k'ara sakin wata dariyar yayi sannan yace

"duk abar wannan zancen, yanzu yau she ne bikin?? khalifa daga jin haka ya k'ara gera zaman shi "yauwa daman maganar nake so muyi, I'm thinking of december ending, shekarar nan"

Abdulshakur ya saki murmushi

"kace abun ya zo saboda december nan da wata uku ne, me sunan ta? tana da kyau? ah kuma Ina kuka hadu?"

Khalifa ya dan yi shiru sannan ya fara

"Abdulshakur kyau bashi ne komai ba ina so ka sani kafin kyau akwai kyan hali, zaka iya zuwa ka auro mace me kyau amma ka zamana baka da kwanciyar hankali gaba daya a gidan ka kullum kuma cikin bakin ciki da kunar rai kuma haka zalika zaka iya zuwa ka auro mace wacce bata da kyau, bari nace maka mummuna dan zaka fi gane wa amma kuma tana da kyan hali zata koma ririta ka kamar kwai ta kuma san darajar ka ta k'imar aure"

Abudulshakur yayi saurin katse shi,

"naji naji, way'annan maganganun naka na gaji da jin su "yanzu zaka gaya mun abunda na tambaye ka ko kuma a'a"

khalifa yayi murmushi a kasan ranshi, bai san mai zai ce mishi ba yabar wannan banzar dibi'ar da ya d'ora wa kanshi, kuma abunda ya fada abu ne da ya faru a zahiri, abokin su Mubarak haka yaje ya auro wata me mugun kyau, irin instagram slayers dinnan amma bata tsinana mishi komai ba yabi ya rame ya lallace har sai da ta kusa sami shi hawan jini saboda tashin hankali, sai da kyar aka raba auren amma duk abudulshakur bai gani ba, yabi ya rufa idon shi ya dage akan ra'ayin shi, a dole sai mace mai kayu, wannan wace irin rayuwa ce ya dauko wa kanshi? Abdulshakur mai cikakken ilimi da sanin abunda ya kamata, Allah ubangiji ya ganar dashi. Sannan ya fara amsa mishi tambayoyin shi

"sunan ta farida, ni tana da kyau a guri na amma sanin halinka na tabbata kai ba lallai ta maka kyau ba, tana medicine a buk tana 4th year dinta," sai yayi shiru na yan sakwanni kamar yana wani nazarin can kuma yace "kai tsaya nabila ai medicine take yi a buk ita ma kuma 4th year dinta take anya basu san juna ba?"

Abdulshakur naji an ambaci nabila ya wani sha kunu kamar bai taba dariya ba harda hade girar sama da ta kasa

"to ni mai ruwana kai da abun ya dama sai kaje ka tambaye ta ko kuma ka tambayi matar da zaka aura"

khalifa ya girgiza kai hade da cewa miskilancin ya tashi kenan, in har ma mace me kyau yake so ya aura nabila ita ce dai dai da shi tana da kyau mara misaltuwa kumai nata nada kyau amma shi still bata mishi ba, duk abunda khalifa a kasan ranshi ya fada tare da hada wa da Allah ya kyauta, sannan ya ci gaba da bashi labarin farida har Abdulshakur ya saki ranshi suka dawo wasa da dariyar su kamar yadda suke kullum. Abdulshakur ne yayi ma mommy waya, yace akawo musu abinci side dinshi dan yayi bako shima kuma baici lunch ba, mommy kuwa ta shirya mishi abinci sannan ta bama amal da amra su kawo musu. Khalifa bashi ya tafi ba sai dab da magrib.

Bayan sun dawo daga masallaci shi da daddy, wajan 9:30pm, Abdulshakur na zaune a parlor dinshi yana kallan news, amal ta shigo da gudu dakin har sai da ya dan firgita sannan ya kai idon shi kanta

"baki da hankali ne ji yadda kika fado min daki kamar wani ya biyo ta"

Amal ta saki murmushi

"Allah dan na tsokane ka ne nayi wannan gudun amma I'm sorry"

duk yadda abdulshakur baya sakar ma da mata fuska, bai yi ma kannan shi ko yayyen shi haka yana mutukar san yan uwan shi kullun suna cikin wasa da dariya. Kallan amal yayi ya dan hade rai

" wallahi wasan da nake da ku keda amra kun bala'in raina ni, to zanyi maganini ku a cikin gidan nan"

amal ta saki dariya amma kana ganin ta kasan tana dan jin tsoro saboda ta sanshi sometimes in dai har suka kule shi to wallahi sai ya daka su, tayi saurin cewa

"daddy ne yace yana ne manka, ka same shi a pallor dinshi yanzu yanzun nan"

tana gama fada tayi waje da gudu, shi ko Abdulshakur dan tsaya wa yayi yai jigum na yan wasu mintuna sannan ya tashi ya shiga bedroom din shi dan ya sa riga a jikin shi yaje kiran daddy, ko mai kuma yau zai ce mishi?, Allah dai yasa ba wani fadan bane.

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now