CHAPTER 98 (FINALÉ)

2.3K 196 65
                                    


RECAP
Bayan su yazeed yaron yabi kamin luku yace dole mu kara kiyayewa da alamu yaronnan yanada wayo. Wani lokutan laifin iyaye ke sawa yaransu su baci. Murmushi tayi taja kamatunsa tace for the first time(a karo na farko) ka fadi magana wacce nayi amanna da ita babu musu.

CONTINUATION

A dakin su zayya kuwa sahir yana shiga ya fincikota yace ke wai wace iriyar yarinya ce? Ke bakiga cewa kin girma bane bazakiyi kiyi da sahla ba? Kuka ta fashe dashi tana Jan majina tace toh Dan Allah ni menene laifi na Dan nace inason haihuwa? Ba duk Kaine da lefi banda sanda nace muku haihuwa nakeso amma kujera min fada kaki la taimaka min mu samu da sai kace ni ba matar ka bane.

Dafe kai yayi San yanzu ya gane cewa zayya yarinyace sosai. Dafe kai yayi tare da sauke ajiyan zuciya murmushi ya Mata a hankali ya riko hannunta yayi pecking zaro ido tayi kunya ya rufe ta. Shikam ma dariya ta bashi amma ya rike zaunar da ita yayi anakin gado yace haihuwa kikeso ko? Ta daga kai yace toh zo in baki yana me daurata a cinya.

Bakin laffayar ta taja ta rufe fuska wai ita jin kunya a hankali tace kunya kikeji ta daga kai kamar doluwa. Kamin tana shan hannu idonta a kasa tace ni idan zayya tana kallon film me irin sumba rude idona nakeyi saboda ba kyau. Lakutar hancinta yayi yace AI ba barsa take kalla ba film ne shiyasa ta fiki wayewa. Rufe idonki yanzuma, rufewa tayi kiri daga nan labari ya canja salonsa......

Su yazeed kuwa suna isa suka tarar da kowa an dallara su ake jira. Bude taro da addu'a akayi sannan Alhaji mansur ya fara magana

Ba komai bane ya tara mu anan wajen sai wani abin mamaki da ya riske mu lokaci daya Wanda zaiyi ma wasu dadi wasu kuma bazaiyi musu ba.

Wato alokacin da aka gwada mu domin bawa bushra bargo munyi mugun mamakin yadda akace babu Wanda nashi ya hau da nata hakan yasa likitan a sirrance yayi mana gwanin DNA yayinda ake gwada na sauran yan uwa dukda ko ba'a tsammace ya hau ba.

Ga mamakin mu sai tahau Dana matar ka ya fadi haka yana kallon yazeed. Shiru kowa yayi yaci gaba da cewa ba abin mamaki bane Dan hakan zai iya faruwa amma anfi tsammanin ya dace Dana yan uwanka na jini.

Lokacin sakamakon DNA ta fito amma likita baima nina mana yayi ba saida yayi na kowa inda ya tabbatar mana babu shakku cewa bushra ba yar mu bace yar malam Yusuf ne mahaifin minal. Zaro ido kowa yayi ana kimanin ya haka ta kasance.

Yaci gaba da cewa na gasta ne duba da kamanceceniya da sukeyi sosai idan ba ka lura ba sai ka kasa banbanta su. Wanda run a fari naji mamaki .

Yanzu Abu daya nake son tabbatarwa kallon minal yayi yace shekarunki nawa tace 36 jinjina kai yayi yace rana da wata fa tace 2nd September. Yace tabbas wannan ranan aka haifi bushra. Babu shakku ku yan biyu ne kuma yadda akayi kuka rabu Allah shine masanin. Fatan mu Allah ya hada kanku.

Baban kowa ne yayi godiya bayan sallama yace toh tunda ta tabbata yata ce amma ku kuka rikota ni bazan harbeta ba na bar muku Abu daya de za'ayi dole abi ka'idar manzon Allah ta canja sunan mahaifi amma nikam na bar muku ita tunda har tayi aure ma ba anfanin na karba.

Godiya Alhaji mansur yayi daga nan aka dan jajanta mutuwar safina kamin kowa ya warware. Inna da tsufa ya fara kamata Dan ta dara shekaru hamsin da biyar tace tace ina kishiyar tawa ne akace hajiya zayya AI gida muka barota tana wani aiki. Tace Allah yasa na arziki ne ba shirme ba. Kallon kallo sukayi sukace ameen.

Bayan watanni sahla ta sambado baby girl dinta amma CS aka Mata. Har ta fara zama zayya ta haifo yan biyunta mace da namiji.

Ranan suna bakin kabir har kunne hoto ake ta dauka shida yaja gefe ya tsaya sanda aka gama mai hoto zai tafi yace mai hoto a dakata. Tsayawa mai hotan yayi yayinda hankalin kowa ya dawo kansa dogon kujera ya zauna yana gyara link dinsa ya zaunar da yar sahla a gefensa sannan ya karbo jinjirar ya daura a cinya.

Yace kai me hoto ka daukeki nida Matana sannan ka yi mana irin rantamemen hotan nan domin acan za'a lika. Ya fadi hakan yana mai NUNI da wani fili a garin parlourn

Daya...biyu... uku aka watsa hotan yana me washe wawulonsa yayinda hular nan tayi coroi a tsakiyar ka.

Yace SHEGE NI ME MATA BIYU kowa ya fashe da dariya 😁😁

NOTE

ALHAMDULILLAH! ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA MAI FARIN JINI DA ALBARKA DA FATAN AN ILMANTU KUMA AN NISHADAN TU.

AFITO KWAI DA KWARKWATA HAR MARASA YIN COMMENT AYI MA KURUCIYAR MINAL BAKWANA.

DUBA SAURAN LABARAI NA ME SUNA YARINYAR CE TAYI MIN FYADE, LITTAFI DA BA'A TABA YIN IRIN SA BA. DOMIN SALIN DADIN SA MA DABAN NE. KUMA ZAKU KARU SOSAI MUSAMMAN IYAUE MASU YARA.

KO KUMA YA JI TA MATA WANNAN LITTAFIN BA KANTA KAWAI DAYA TAMKAR DUBU,IN KUKA FARA KARATU KAMAR KAR KU DENA DAN DADI GA ILMANTARWA SOSAI GAMI DA CAKWAKIYA MAI KWANTAR DA HANKALI.

KO KUMA YA JI TA MATA WANNAN LITTAFIN BA KANTA KAWAI DAYA TAMKAR DUBU,IN KUKA FARA KARATU KAMAR KAR KU DENA DAN DADI GA ILMANTARWA SOSAI GAMI DA CAKWAKIYA MAI KWANTAR DA HANKALI

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

MEET THE AUTHOR miss untichlobanty

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty 💕

6th June,2020.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now