CHAPTER 63

3.4K 228 24
                                    

Cikin jin kunya minal ta gudu ta Koma ciki yayinda yazeed ya tsare kamar ba abinda ya faru ya nufo inda su Jamal suke. Mashkur yace ai bansani akwai free cinema a Nigeria ba, suka yazeed yakai masa yace Allah ka fita Daga idona in rufe.

Dariya suka fashe dashi yazeed yace dallah malamai Ku wuce muje ! Wani dariyar suka kuma fashewa dashi yarda buga kafa.

Tsaki yaja ya Koma ciki domin kiram su mom.

Tattarawa suka farayi domin wucewa FIRST CLASS MULTI SPECIALIST HOSPITAL Inda zakiyya ta damka amanar yaranta a hannun minal sannan ita ta zauna domin ta kula da ayush.

Dakyar suka samu suka Shiga dakin da ummi take saboda tsabar yadda Yan dubiya suka cika corridor din Suna Shiga aka fara gaggaisawa. Inna na fading tayi kewa yazeed da yanda yake shanye mata zobo.

Ummi kam sai murmushi takeyi domin taji dadin ganin iyalinta da abokan arziki cikin farin ciki.

Yazeed ne ya fara Jan rigar Laila wacce Keta dariya saboda jokes din da minal keyi.

Da Hannu ta mai alamar miye? Ba tare da ta bari kowa ya gani ba Dan ta fahimci bayason aji

Alamu ya mata da ta dauki wayarta zai mata sms.
Message ya tura mata a take ta bude taga an rubuta sako Kamar haka

Yazeed: ke ina matan gayennan?

Laila: wanne fa?

Yazeed: lukman mana

Laila:oh zaliha kake nufi ai ta fita siyo abinci ne Dan acici ce Kamar matarka.

Harararta yayi afili tayi masa alamun ko karya Nayi?
Numban minal yayi joining ya zamto su uku zasu iya message
Yazeed:baby kinji me Laila ke fadi kuwa.

Wayar minal ce tayi haske Dan haka ta Duba reply tayi

Minal:me take Cewa?

Yazeed: Wai keda kawarki acici ne

Minal:😮kut shiyasa tun da bama shiri saboda rashin kunyarta.

Laila: ke kuma kin fiya son girma ba.

Minal:ban girmeki bane?

Laila amma ai 'ya'yanki zan aura kinga kokirana yaya dole😜

Minal: typing.....

Yazeed:Inda mijinki Waye babba?

Laila : Kaine

Yazeed: Toh ta girmeku ke da mijin naki.

Minal: I love you..

Laila left

Yazeed:what?!

Minal : yes

Yazeed: ni bana sonki ai yanzu

Minal: typing......
Minal: typing......
Minal: typing......

Yazeed:what are you typing ne?

Minal: zansha ruwa

Yazeed: seriously?

Daga kai yayi ya kalleta yaga hawaye nabin fiskarta zaro ido yayi domin shi wasa yakeyi. Dan yasan irin son da yake mata.

Daidai lokacin wayan lukman ya fara ringing fita yayi tare da dauka....

Da gudu minal ta fice ganin yazeed na kokarin zuwa kusa da ita.
Kallo kowa ya bisu dashi kamin suka table baki tare da ci gaba da huldodin gabansu sha'anin mata da miji ka Shiga kaji kunya.

Lukman na Daga wayan yace salam

Yorubanci yaji an fara masa nan yayi bayanin Cewa wrong number ne sannan ya kashe wayarsa zai juya ya Koma kenan ya hango zaliha tana tunkaro ward din ita da wani saurayi kuma zalihan tana dariya baisan sanda kafunshi suka nufosu ba ya danki kwalar saurayinnan ya surface masa mari tau kake ji take yayi adungure sallar mage bakinsa ya fashe da Sauri zaliha ta hankadeshi tare da farin miye haka ? Ya Daga ganin mutum zaka hau dukansa?
Saurayin na mikewa yasan Inda dare yamai yayinda zaliha taci gaba da farin ai bansan tababbe aka aura min ba fincikota yayi zuwa wani daki a ICU din dakin babu kowa. Huci yake Kamar zaki yace nine mahaukaci ko ? To bari kiga belt ya fara cirowa tace wallahi kasa ka sake ka tana zalihatu inba rainin hankali ba Daga ganina dashi zaka wani rufesa da duka Toh mai Saida recharge card ne dariya yayi yace wow what an awesome story shiyasa naga har murmushi kuke mai.
Dariyan itama tayi tace fadi kanka tsaye kace kishi ke damunka ba ka tsaya kana nuku nuku ba
Tsaki yaja tare da fadin kishin wa ? Allah ya tsareni yo ni me zanyi dake wani Abu Kamar an goge bayan tukunya, yo ke anace miki bakar mace wani Kyan gareta da har zanyi kishinki ? Naga dai kina nema ki tsallake min igiyar aure Kiyi wani abin ne Idan bakisan darajarta ba ni na sani.

Ashar ta danno tace me kake nufi kana nufin ni yar iska ce. Tabee baki yayi yace wa ya sani Abu a duhu a bakin Leda?
Kwalarsa ta riko idonta ya cicciko da hawaye tace ni ? Ni kake kira da yar iska? Ni zaliha ?

Hankadeta yayi aiko suka tafi tare.

🌹🍀🌹🍀...............

Yazeed ko yana fitowa ya janyo minal jikinsa yace menene? Kokarin turesa ta fara yi tare da fadin kasake ni tunda baka so na.

Kuka ta fara masa Kamar yarinya yace shhhh Kiyi shiru Kiyi hakuri wasa nake miki Allah ina sonki wallahi Allah ina sonki ki dena kuka yana tana mina zuciya na gaba tawan gaba amaryar yazeed murmushi tayi kamin ta soma sana'ar shagwaba

Turo bakin tayi tace aini Nayi fishi ma tunda sanda ka sani kuka tukun kace kana sona.

Yazeed being a drama king ya taba zuciyarsa tare da fadin my chest wallahi karki kara Cewa baki sona. Gwaliyo tamai yaja hancinta suka fashe da dariya tare da rungume juna cikin farin ciki da kauna juna.










































































(Su o'o andauka ya Kare Toh da saura)

Daidai lokacin suka hango lukman yana janyo zaliha kamin ya wulla ta adaki.

Da Sauri suka karasa bakin dakin  amma nasu Shiga ba tunda ba sha'aninsu bane sunjene ma ganin yanda gaba daya lukman din ya canja Kamar kace hi ya kasheka duk idonta yayi jaaa jijiyoyin kansa sun tashi.

Sunji duk abinda suka fada minal na tsaye a gaba yayinda yazeed ke rungume da ita ta baya hakan yasa ya fara mata magana a rada

Baby dole fa mu Shirya aminanmu kinga dai yadda suke fada. Gyada kai tayi suka cigaba da lekensu dai dai lokacin su zalihan suka fadi murmushi yazeed ya sakarwa minal tare da pecking gefen wuyanta.

Kallon kallo su lukman suka tsayayi kamin zaliha yaja tsaki ta hankadeshi tare da fadin dalla malan Daga ni.

Tashi yayi cikin borin kunya yace sekace wani abar zanji a kashinnan. Murkuda baki tayi tace a hakan dai aka danneni aikin banza dadai lokacin lukman ya lura dasu yazeed Dan shi yake facing kofa hakan yasa ya janyota ya rungume ta kam yana shinshinanta Kamar romance suke Dan a tunaninshi lokacin su yazeed suka zo ganin zata kwace yasa ya kara kankameta abinda be saniba kuwa zaliha wani Yan ayi ta fara Shiga saboda margin sha'awarta Dan har tafi minal dukda minal dinma ba'a barta a bata ba.

A kunnenta ya rada mata su yazeed Suna kallon mu so act.
Jikinta ya sake Dan haka ta kasa reacting ma balle ta masa taurin kai ko ta bijire.
Sakan jikinta tayi tare da kamo fuskarsa ta fara kokarin sunbatarsa Dan tama manta Waye a wajen.

Minal ne ta kwalka ihu a take suka zabura hard a yazeed Wanda ya shagala da kamshin jikin minal din.

Yace minene? Tace cinnaka ne ta cijeni janyeta yayi suka bar wajen Inda aka bar zaliha da borin kunya tsaki taja tare da fadin Dan iska kawai biyota yayi ta fice a guje yace zan kamaki yar renin hankali kuma tare zamu tafi gida.

Juyowa tayi tace me ? Yace kwarai tace kana nufin yau zan tare yace tarewan ma taci ub*nsa daganan sai gidana kimaji da Wai.

Tattarowa sukayi suka Koma gida bayan sunyiwa su ummi sallama mom sai dadin ganin yanda yazeed dinta ya canja take. Ya Koma ainihin yazeed dinsa me faran faran kamin rasuwar dad dinsa.

Inna ko sai tsiya takewa su luku wai daga ganin nina sun kasa nakuru a tare ma su zasu tare. Sai dariya ake kamin aka rabu.

Godiya dubu ga dunbin masoya na da kuma masu sharing littafinnan Allah ya saka muku

Wannan page na sadaukar dashi ga fans dina baki daya

Ina kaunarku sosai! Takuce karamarsu babbarsu.

Miss untichlobanty💕

12 January, 2020

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now