CHAPTER 2

5.5K 301 23
                                    

BAYAN WANI LOKACI DA RUBUTA JARABAWAR MINAL

Morning
Minal rike da sakamakonta a Hannu miftahu (kanin hannatu zamu ganta a gaba #chapter 8 ) yace manya manyan Yan boko har an karbo sakamakon kenan da fatan wannan karan ma ba'a dauko ajinba. Cukumosa minal tayi ta naushi bakinsa tace aiko Ba Komai ni nane makarantar wasu a yawon banza za'a kare. Daidai lokacin sani (yayan bilkisu itama zamu gantaa gaba #chapter 8) ya wankawa minal mari juyowa tayi tace buhun bala'i bai ankareba yaga an nunashi wa sama an nana da kasa suka minal tamai jina-jina sannan tasa yara sukabuleshi da kasa.

Evening

A guje yara suka rugo Suna oyoyo baban kowa oyoyo baban mu! dama ya saba Dan haka yasa kullum baya rabuwa da tsaraba, hanjin ligidi mai yawa acikin bakin laida ya ciro ya basu suka karba Suna godiya kamin suka raba, wata yarinyace tace baba yau wani tatsuniya zaka mana yace tatsuniyar gizo bakin barawo zan muku.
Lado ne ya shinfida masa buhu Kamar yadda suka saba sannan Suma yaran suka zazzauna nan dattijonnan ya soma musu ta tsuniya......

🌹.............

Wasu samarine zaune Suna busa sigari wayan dayansu ta soma kara daukowa yayi yaga karfe alarm dinsa na large hudu ne take ya kashe sigarinsa yace kai yau fa alarm NASA mana aradu lokacin dawowan tsohonnan yayi,dariya suka fashe dashi wani yace Ba mamaki ya tsaya yiwa yara tatsuniyane. Sukace Ba shakka amma fa tsohonnan yana yiwa mutane cikas ka duba abinda yar b*ra ub*an yarnan tasa tayi dazu.
Daidai lokacin baban kowa ya karyo kwana,a take suka karkade jikinsu tare da wulla alewa a baki Dan kar yaji warin sigarin tasu.

Nufosa suka farayi Kamar abin arziki shima da murmushinsa yaje nufosu domin yaune karo nafarko dabai kamasu Suna busa sigari Ba.

Saide kash suna motsowa kusa dashi ya jiyota aiko take annurin fuskarsa ta dauke sukace babanmu sannu da zuwa Suna masu durkusawa

bata rai yayi yace Duba su Kamar da haske Kamar mutanen arziki, Wai Ku fi sabillilahi bazakuyi wa kanku fada ba, Kamar da gaske nadau kunyi hankali Ashe da sauran Rina a kaba,

Bakusan cewa wannan shaye shayen naku yana janyowa iyayenku Bacin sunaba?ko kunaso duniya tazagesu ne?girgiza kai sukayi sukace ayi hakuri baban mu Insha Allah zamu daina.

murmushi takaici yayi domin Indai wannan alkawarinne to an karyasa tun kafin adaukesa yace Allah ya bada ikon dainawan,kuna batawa kanku rayuwa ko bakusan Cewa duk abinda mutum yayi yana kuruciyar shi zai bishi har girma ba ko kunaso idan kun hayayyafa acewa yaranku kun taba busa wiwi ?girgiza kai sukayi yace Idan yaranku suka sha Ku ya zakuji hada baki sukayi wajen Cewa bazamuji dadi ba yace Idan Baku sani bama Ku sani wannan shaye shayen yana haifar da tabin hankalin,lalacewar koda da zuciya kuma tsaf zai kashe mutum. Ku a haka zaku hadu da Allah? Kuma kuna tunanin Idan an tafi a haka ba matsala?Ba Arabic Ba bokon?Allah ya Shirya....

Tafiyarsa ya cigaba dayi yana mai fada akan yadda matasa ke bata rayuwarsu.

Majalisar su malam yakubu zai wuce sukace salamu alaikum baban kowa barka da war haka murmushi ya soma musu sannan ya mika musu hannu sukayi musabaha.
Malam isa mai wankin hula ne yace ya naganka haka ne ? baban kowa yace kaide bari yaran yanzu basu rabuwa da kayan bakin ciki yanzu na.....

Malam saminu ne yazo yana girgiza kai alamun alajabi jikinsa a sanyaye ya zauna
Baban kowa yace haba malam saminu ya haka zakazo ka zauna bako sallama? inkai kayi haka 'yan'yan mu kuma yaya zasuyi ?

Malam saminu ne ya cire hularsa ya ajiye kana yace wato wani abune yayi mugun jijjigani, Wai yar gidan malam ado salma akayiwa fyade saboda sakacin maihaifiyarta. fita tayi bayan magariba ba'a saniba uwar kuma da bata ganta Ba bata nemeta Ba sai da taga kusan goma ya wuce shine ta Sanar da malam adon. neman duniya an mata ba'a ganta Ba yau da asuba aka yadda ita koda aka kaita asubiti likitoci nata kokarinsu amma ina. yanxu yanzunnan rai yayi halinsa,Allah ya mata rasuwa!

Shiru wajen ya dauka kamin caaan malam sambo Wanda tun dazu baiyi magana ba yace Wai salma dai guda Dana sani yar shekara 6?itafa wannan salmar dai inji malam saminu
Salati suka rafka jikin kowa yayi mugun sanyi kamar an musu duka.
Allah sarki salma yarinya mai hankali da Shiga rai. Allah yaji kanta bari anjima sai mu hadu muje muyi masa ta'aziya nan dai suka Dan tad'a kamin malam Yusuf yayi gidansa.

Koda yake tafiya a hanya sai surfo masa gaisuwa ake ta ko'ina manya da yara. Atakaice de baban kowa mai jama'a ne.

Yana isowa kofar gidan sa, basheer mai shago yace baban kowa ina wuni,Lpy klau basheeru ya shagon?basheer yace Alhamdullah baban kowa yace masha dafatan dai yauma minal bata taba kowa Ba Dan yau da safe tace Mani Wai tun jiya akace suje su karbo sakamakonsu. Basheer yace Gaskiya baban kowa yau minal bata yi hayaniya da kowa Ba hasalima ko fitowanta bangani wadda nima abin ya bani mamaki da alamu dai kawattamu ta natsu(haka basheer din ke kiranta domin ya kasance abokin ya abubakar ne tun yarinta shiyasa ma yayiwa baban kowan karya Dan kar yasa wa ransa damuwa sosai)
Baban kowa yace to Masha Allah haka akeso ai ni bara in Shiga Daga ciki ko? Allah yayi albarka basheer yace amin.

Minal na zaune tana yanka kubewataji sallamar mahaifinta hantar cikinta ne ya kada da gudu ta mike har tana tuntube a 360 ta fada daki,garin sauri ta barar da yakuwar da take yankawa innace ta haba er lele lafiyarki kuwa zaki barar mani da......

Bata ida maganar ba baban kowa ya shigo yana cewa inata sallamma Baku amsa ba Kamar ba kowa a gidan inna tace yi hakuri malam sannu da dawowa Wlh wannan yarinyarnance ta fada daki da gudu har tayi Mani bari banjika ba yi hakuri bara na kawo ma ruwa
Takalmin sa ya cire ya zauna a tabarmar dake shinfide a tsakar gidan yana Cewa halan wayanta aka kira take wannan gudu , inna dake shirin bude randa domin sachet watern su ya kare tace anya kuwa?hira fa muke daga jin sallamarka ta rusa da gudu Kamar taga aljani,baban kowa najin haka jikin sa yayi sanyi bayason irin faduwsrnan da yarda keyi a makaranta domin Hanson tayi karatu ta inganta rayuwarta

Yace takarbo sakamakon jarabawar tasu kuwa inna tace eh ta karbo dazu gasucan yana kan yana kan taaga(window),tashi yayi jiki babu kwari ya dauko ya Duba aiko Kamar yadda yace ne ankuma na 48 tazo acikin su 52 a Dan fusace yaje kofar dakin yace aminatu me kikeyi acikin dakin nan,minal tace Riga make canjawa yace inba so kike na Shiga Ba maza ki fito tace baba aradu Babu Riga ajikina wanka make shirin yi yace Kamar da haske rabon da Kiyi wanka keda kanji Ba tare da dance Kiyi Ba yanzu shekaru 6 kenan amma shikenan ni bara in dubo sakona waje.

26th April 2019

Oya show some love
By voting,
liking,
sharing
and
commenting

Tnxs for reading

Mzz untichlobanty💕

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now