CHAPTER 69

3.1K 186 25
                                    

Zakiyya kam koda ta gama kukanta fitowa tayi domin ta dauki golden morn dinta amma sai taga abinda akasha har wuce rabin Wanda ta dama kuma Idan zata iya tunawa cokali 3 tasha, tabe baki tayi tace may be ban lura bane shiyasa.

Shanyewa tayi kamin takai kitchen. Dakin da ayush take ta shiga ta duba ta sannan tayiwa nurse saide safe saide ta lura kamar akwai abinda ke damun nurse din amma sai ta basar.

Koda ta koma daki taga 2 missed calls from summy wannan friend dinta yar lesbian.
Calling back tayi ringing 2 ta dauka gaggaisawa sukayi tayi Mata Jaje sannan ta sanar Mata cewa mom dinta batada lafiya jibi zatazo ta dauketa sai ta duba ta. Zakiyya tace toh amma sai ta fadawa yazeed.

Koda gari ya Waye registration nasu jamb da WAEC and NECO akayiwa minal bakinnan har kunne. Bayan sun dawo minal tana Yan tattare tattare a dakinta sai ga zakiyya. Gaisawa sukayi tace toh mu fara ko. Minal tace toh bari na gama Dan tattare tattare nan. Hannun zakiyya tasa sukayi tare bayan sun gama suka nufi toilet minal tace toh tayi Mata alwalar yadda ta iya ta gani sai ta Mata gyara.

Abinda ya bawa minal mamaki shine ta iya tace Mata to ai kin iya ma. Murmushi kawai tayi akayi Salah ma gyara kadan aka Mata. Bayan sun gama har su azkar minal tace toh aunty zakiyya duk kin sani ma ai gyaranki kadan ne. Murmushi tayi tace thanks to my father lokacin da muke yara.....

Wani mutumi ne me kimanin shekaru 45 tsaye a tsakiyar parlourn gidanshi da alamu an bata masa rai duba da yadda yaketa huci kofar wani daki ya kalla tare da cewa ummi! Zakiyya! Idan na shigo dakinnan zaku gane kuranku. Wata budurwa me kimanin shekaru 15 ce ta fito tana zumbure zunbure. Wani kallo ya bita dashi yace kede ummi kinji kunya babbar banza kawai ke bakisan cewa Ilimi shine gatan mace ba da makarantar boko ne kinfi kowa rawar kai wato shine kika fara hurewa yar uwar taki kunne ko.

Kauda kai gefe tayi tare da zura hijabin islamiyarta. Yarinya me kimanin shekaru 11 ne ta fito tare da cewa abba kayi hakuri hijab Dina na rasa. Murmushi yayi yace ba komai AI nasan ki zakiyya ta badai himma ba wajen karatu dama ke na sawa me sunan mamana ba wannan babbar kwabon ba. Kallon ummi yayi yace Allah ya shirya ta tabe baki.
Mota suka shige ya nufi islamiyarsu. Koda suka isa yace toh ummi Allah yasa muga alkhairi wannan karan. Indai sakamakon nan da zaku karbo yayi kyau to zan sayo miki wannan takalmin Kema zakiyya Allah yasa kinyi maintaining position dinki. Ameen tace cikin ajin dadi kamin ta dauki Jakarta. Naira biyar biyar ya basu yace ga wannan ku rike ko? Godiya zakiyya tayi tana mai jin dadi yayinda ummi ta yatsine fuska ta karba sannan ta fice ba ko godiya.

Suna shiga ummi ta finciko zakiyya tare da lafta Mata tafi tace shegiya irin ke yarinyar arziki shine harda wani godiya ko toh saina fadawa mommy dama nice me sunan maman mommy ba ke ba. Hankadeta tayi ta fadi tare da gurje hannu. Kuka ta fara yayinda ummi tayi shigewarta cikin clique dinsu Dan itace leader suka nufi aji ana shewa.

Mardiyya best friend din zakiyya ce  ta zo ta dagota tareda bata hakuri suka wuce ajinsu suma. Kuma duk abinda ke faruwa ummi na kallo yatsa ta  cije Dan haushin mardiyya takeji wai ita ke mayar da kanwarta yar kauye. Murmushi tayi saboda wani makirci data hado musu.

Koda su zakiyya suka shiga aji tana ganin Umar ta fara murmushi tana sauke kai ita a dole sonshi take. Shima dai a nashi bangaren hakane saide ko magana basu tabayi yi wa juna ba. Sai satan kallo. Ganin tana dingishi yasashi zuwa wajenta da sauri ya riko hannunta tare da cewa zakiyya me ya sameki. Kunya ne ya rufeta ta kasa magana. A hankali ta janye hannunta ta zauna a tabarma Dan lokacin ko private school ba ko wanne keda benci ba. Benci 5 a ajin 2 na Mata 3 na maza.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now