CHAPTER 47

2.9K 199 8
                                    

Da safe jiki babu kwari minal ta fito ta fara aikinta koda ta kammala,tayi wanka sannan lokaci zuwa lokaci takan sauko ta Duba dinning table ko yazeed ya sauko domin ta share dakimshi tunda yace bayason ya kara ganinta.

Komawa tayi dakinta ta zauna Jim kamin ta janyo wayarta sai alolacin ta tuna batada numbern zaliha kawai sai kawai taje gaban madubi ta shafa powder da lipstick saboda rage lokaci Kuma tayi kyau Ba laifi.

Fitowa tayi daga dakin aranta tana Cewa Nasan ya fita ma tunda safe kuma ko na hadu da shi ma nuna masa zanyi ina fushi dashi muga yadda zaiyi. Murmushi tayi kamar wata shashasha ko yadda yara keyi Idan sun kulla wani abin.

Laundry room ta Shiga ta dauko kayansa set 2 data goge dazu ta nufi part dinsa koda ta Shiga Ba kowa kuma parlourn nasa ma da duhu alamun babu kowa tace Ahe duk jirannan danayi na banza ce bayanan ma.

Ta bangaren yazeed kuwa Kamar jira yake ta Koma daki sai gashi ya sauko, kitchen ya nufa ya dauko hollandia yoghurt plain flavour saboda na fridge din parlourn sa ya kare sannan ya dauki cup ya fita.

Dakinsa ya Koma yasha yoghurt dinsa Dan baya mood din cin abinci. Kwantawa yayi abinsa ruf da ciki yana mai kashe wutan dakin sannan ya rufe idanunsa once in a while yana murmushi.

Da confidence dinta ta tura kofar dakin Dan ba'a rufe kirif take ba sai ta dauka ko ya bar mata ne Dan tayi shara Kamar yadda yasaba bari Dan haka bata kawo Komai cikin ranta Ba ta shigewarta.

Hijabin dake jikinta ta cire tayi cilli dashi akan gado sai kan fuskar yazeed Wanda dama tun dazu yaji takunta kuma yasan ta shigo dakin amma ita batasan da zamansa Ba. Baice uffan Ba balle ya motsa yayi luf cikin bargonsa sai kansa dake waje wanda yanzu yake lullube da hijabin minal. Tunani yake aransa yarinyarna badai sa hijabi Ba kam. Allah yasa da kyakkyawar niya ce.

Ajiye kayan tayi akan stool kamin ta dafe goshinta da hannunta tace ni yanzu ya zanyi ? Kullum yananan yana budemin wannan yar iskanci kofar dakin kayan nasa to yau kuma bayanan.
Kicin kicin tayi da ido tace Idan na kamo yaya yazeed dinnan sai na naushi bakinsa. Sai kuma ta kyalkyale da dariya tace Wai wayaganni na danne ya yazeed sai jibgarsa nake.
Wutan dakin ta kunna kamin ta dauko kayan aikinta. Ganin bargon NASA a wargaje yasa tace kai Ashe ya yazeed dinma kazami ne fadin jumlar tayi daidai da janye bargon aiko atake ta kwala ihu zata arta a guje yayi saurin wantsalota ta fado jikinsa kokarin tashi take tanata tuttureshi amma ya riketa gam hannunshi ta fara mintsini tana Cewa ya yazeed ni ka sakeni nifa Ba yar iska bace. Bai kulata Ba illa ma tashi da yayi zaune sannan ya ajiyeta akan gadon couch ya Koma ya zauna sannan yace rosy cheeks gyara gadon kizo in fada miki wani Abu. Dan hade fuska tayi tace me zaka fadamin? yace sirrine a kunne ma zan fada miki tace toh..........

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Zakiyya zaune a parlourn gidansu Amarya tana oiling ma ayush din gashi Wanda Ba yabo Ba fallasa.
Wayanta ne ya fara ringing ta dauka kamin tayi magana akace madam the boutique has been on fire mun kira fire service sun kashe but we couldn't retrieve our goods.
Zakiyya da batasan sanda mike Ba tace what?how comes? Are crazy? incoming call taji hakan yasa ta Duba ganin sectary dinta ne yasa ta datse da gaggawa tana mai Cewa hello maryam wani irin nonsense nakeji Wai boutique ya kam..........

Bata karasaba Maryam tayi Sauri Cewa Ba nonsense bane ma munyi gobara, the came out of no where. Yanzu haka ina hospital saboda na none a gefen hannuna amma Ba wannan Ba new boutique dinma an Shiga an kwasge kayan tas sanna aka rusa ginin.

Take zakiyya ta yanki jiki ta fadi kasa sumammiya. Ace sukiyar da tayi shekara kusan 5 tana Tarawa cikin minti 5 babu su?ina impossible.

Inda Allah ya taimaka baki nasu wani hallara Ba tunda har yanzu saura 4 days a fara shagalin bikin ma Dan haka akayi asibiti da ita.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now