CHAPTER 90

2.1K 157 39
                                    

DAN ALLAH KARKU MANTA DA FOLLOWING DINA SECOND BIYAR KACAL ZAI DAUKA.

RECAP

Yafe Mata kowa yayi daddy yace batun na aura miki Wanda naso bai taso ba ki naimo miji dai amma kafin nan ya kamata nasani SHIN KIN TABA YIN ZINA A YAWACE YAWACEN KI?

CONTINUATION

Shiru parlourn ya dauka kowa ya tsime yana jiran Ansar da zata bayar girgiza kai tayi hakan yasa kowa ya saki numfashin da basu San sun rike ba.

Alhaji yace toh masha Allah ai abun yazo da sauki. Mikewa tayi zata tafi inna ta kalli bushra tace uwani baki ga baki bane? gaishesu tayi zata fita sabir yace ABBA inada magana.
Daddy yace toh muna jin ka. Yace dama idan babu matsala ni naji na gani inason in aure ta. Kallonsa kowa yakeyi daddy yace ka tabbata ? Yace eh. Daddy yace toh ke kinji kina sonsa? Tace ABBA indai ya maka nima yamin daddy yace toh kai sai ka turo manya ko? Yace ABBA AI banida su yaya mace kadai gareni. Daddy yace toh fa toh yanzu yaushe kake ganin za'a daura auren? Caraf bushra tayi tace yanzu ma yayi. Salati inna ta rafka tace riko sai jalla jalalu. Toh AI shikenan.

Atake a wajen aka daura auren akan Rabin albashin sa wato 10K yazeed ne yace ni kuwa kamar na sanka ko? Yace kwarai kun sanni. Ai nine............

Bayani ya tsara masa yazeed yace Allah sarki Allah ya tsare na gaba ya saka maka. Sabir yace no wonder lokacin da naga yar uwa naji kamar na San ta.

Daddy ne yayi ma mama magana a kunne fuskarta ya Dan canja amma da ta kalli mom sai ta sauke ajiyan zuciya ta gyada kai alamar yarje wa.

Kallon yazeed yati yace Alhaji yazeed idan BAZAKU damu ba naga auren nan gwanin ban sha'awa zan so nima inyi wuf da mahaifiyar ka.

Dariya kowa ya fashe dashi abin kamar a wasa suma a zaman nan aka daure su Alhaji sai washe baki yake yi wai shima a dole ango.

Sahir ne yace toh wai nifa ban gane ba naga sai overtaking akeyi anata aure aure toh kawai ayi namu a huta mana zayya tace kasan dalilin da yasa nake sonka? Girgiza kai tayi tace saboda kanka yana ja sosai. Maketa inna tayi. Akace toh marmarza sahir da safwan ku ciro duk abinda ke aljihun ku ku ajiye. Daga nan aka daura auren daddy yace a Nemo nana da kayai lemo ayi yar karamar shagali.

Inna ke ta kokuwa da cinyar kaza Dan ya Abubakar yace kakus kawai ki hakura da naman nan kin tsufa fa sai kin cire hakori kizo ki hanamu bacci da daddare. Dariya aka yi tace haba mai gida (yaron me sunan baba ne) harda kai ake haduwa aci mini mutunci?
Safwan yace kakus karya kikeso yayi?

Yazeed ne yayi gyaran murya yace inada magana yanzu dai zan bar kowa anan domin banaso ayush tasan cewa mun dawo hankalin mu Dan haka daga ni sai matata sai sahir da safwan da iyalan su ne zamu tafi Jamal kaima zamu tafi tare tunda dama tun da a gidan mu kake amma kar kayi kuskuren nuna kauna ko tausayi ga zakiyya sauran kuma abar mana ni da ita(wato minal).

Sai bayan la'asar sannan suka nufi gida bayan anyi hotuna ran kowa wasai duniya tayi musu dadi.

🌹🍀🌹🍀

Ayush zaune da uwar ta a parlour hankalin su kwance suna kallon film Dan basu da Aiki sai kallon fina finan horror da vampire da BL da GL da sauran su.

Safina ne ta fito taci leshi tana taku jikin nan yana motsawa ta ko ina tace an dai ji kunya. Duk wannan shagali da kuke dazu harda tara kawaye aikin banza ne Dan ko ajikina bari kuji. Kitchen ta shiga ta dauko madara da Kofi.

Sallaman su yazeed yasa hankalin su yayo bakin kofa. Dum dum kirjin su ke bugawa. Cikin tsoro ayush ta hau bari ganin minal biye da yazeed. Mummy ce tayi kokarin cewa son har ka dawo kenan ? Ashe ma tafe kake da amaryar.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now