CHAPTER 89

1.9K 139 85
                                    

RECAP

Mom kuwa kamar yar gida haka ake Mata taci leshinta fess sannan ba'a wani sata aiki sosai. Suna zaune a dakin mama ana hira irin ta manyan Mata mom tace wai ni kam WANENE angon ne naji ana an daura auren Amma banji sunan sa ba. Mama cikin fadada murmushi tace yazeed ABDULMAJEED Umar ne atake mom ta Mike tana fadin shine wallahi shine. Akace shine me? Tace Dana shine Dana. Daidai lokacin bushra ta shigo dakin tana fadin mama ayiwa kawayen wannan yar rainin hankalin magana su fita a daki na. Yau kwanana biyar bana nan daga dawowa za'a bata min rai? Mom tace minal me kikeyi anan? INA YAZEED?

CONTINUATION

A saman ido take kallon mom kamin tace dalla dubata, wacece ke kuma da zaki wani kirani da sunan wancan yar rainin hankalin ? Mama ne ta gwabe Mata baki yayinda mom ta fita ta nufi part din da aka ajiye su ko da ta shiga wajen yazeed ta nufa mama na biye da ita. Rungume shi tayi tana kuka tana fadin yaro na ka tashi, mahaifiyar ka ta dawo gare ka. A firgice ya bude idon sa yana fadin minal! Minal ! Mama ne tace a cewa sabir ya Kira minal.

Dakin sabir aka je amma me kwance shima aka samesa shame shame dan haka aka ciccibo sa aka hada dashi. Kururuwar kawayen amarya akaji suka fito a rikice akace faduwa tayi ko? Suka ce taya akayi kuka sani? akace kawai su dauko ta su kawo side din lokacin yazeed ya tashi ya makale mamar sa kam kam babu abinda yake sai kwalla kamar yaro.

Daya bayan daya haka suka dinga tashi saide babu Wanda yace komai. Bayan wani lokaci baki suka watse yayin da kowa ya tashi ya war tsake. family ne zaune baki daya parlourn ya dauki shiru yazeed ya rungume minal kam babu ruwan sa da cewa ana ganin su. Shirun ne ya katse lokacin da zayya da sahla suka fado cikin ankonsu na lace sunsha kyau saide fuskar duk ta baci da hawaye sahla na fadin ummi wai da gaske uncle Dan gayu ne baban mu? Gyada kai minal tayi dadi suka faraji suna tsalle da rawa sai zayya ta tsaya. Sahla tace menene sis? Shagwabe fuska tayi tace kenan sahir yaya na ne babu aure a tsakanin mu? Da sauri ya janyota ta fado jikinsa ya rankwashe ta yace kaji ta a wajen. Ni ba Dan daddy bane amma yayi dauke ni a matsayin Dana tun muna yara, Kinji dadi? Washe baki tayi ta rungumeshi kam kam sahla ne tace sis Allah ya isa na. Kowa ido ya zuba ga mamakin da zayya ta basu ta makale sahir ita kuma wannan tana Allah  ya isa? Ko na menene?

Kafeta da ido sukayi cikin Sosa keya tace bafa komai bane kuke kallo na, idan ba neman magana ta ba shine zata je ta zauna a cinyarsa Dan ni banida saurayi ? Gwaliyo zayya ta Mata yayinda sauran suka rafka Salati cikin annashuwa sukace ikon Allah yaran zamani ba kunya ko kadan. Safwan ne yace nima fa zanyi Allah ya isan nan. Kallon yazeed da sahir yayi yace haba daddy da bros ku duba yanda kuka wani makale a jikin matan ku, kuka barni ni daya  bayan kunsan cewa akwai wata zukekiya Baku fada min nima nayi wuf da ita ba? Dariya aka masa.

Alhaji yace yanzu dai ayi mana Karin bayani domin an barmu a duhu. Yazeed ne yayi ajiyan zuciya ya sassauto rokon da yayi ma minal yayi kudubatul Haja sannan ya nuna mom yace ABBA.... wannan da kake gani itace mahaifiyata, minal ya nuna yace wannan kuma matata ce kuma ga yarana na kamar yadda kuka sanar dani. Sahir da safwan kuwa tun kamin wannan Lamari ya faru ba daukesu a matsayin yara na. Sun kasance yaran marigayiya yayar tsohuwar Mata ta zakiyya kuma matar Jamal a yanzu. Ya fadi hakan yana nuna Jamal yace Jamal kuma Dan kanin mahaifiyata ne.

Yace akwai aminiyar minal tare wato zaliha da kuma aboki na lukman suna kasar waje amma na tabbata yanzu haka suma sun tuna komai dukda cewa dama basu mantani ba matata suka manta. Sai kuma akwai Wanda har yanzu yake Kaduna toh shima dai bai mantani ba matata ta ya manta.

Alhaji mansur yace toh naji bayanin ka amma me hadassa wannan mantuwa naku ? Yace wannan ne banida amsa bansa ko akwai Wanda ya sani ba....yauwa sannan a gida akwai mahaifiyar zakiyya da kuma kanwata ayush Wanda na dauka kanwata da mahaifiyata ne. Ture shi minal tayi cikin zafin rai tace ko sunan su ka kara Kira ban yafe maka ba. Shin bakasan cewa wannan tsohuwar kalakin ba mahaifiyar zakiyya bace mahaifiyar ayush ce? Ko baka San cewa ayush ce tasa kuka mantani ba? Ko bakasan cewa ita taso ta haukatar maka da mahaifiya ba har ta kaita gidan mahaukata. Shin baka gane cewa dukiyar la takeso ba? Shin bakasan hassada da San abin zuciya su suka sakata aikata wannan aiki ba? Shin bakasan cewa shedan yana alfahari da
Ita ba? Wannan tsinanniyar ko taro za'ayi shedan bai samu halarta ba idan taje an gama. Lokacin da ta kawo nan kuka take sosai janyota jikinsa yayi yana bata hakuri. Zaburowa tayi ta zauna tace ina zakiyya? Karkace min sun kasheta? Yace tananan saide kuma bata iya yin komai ko kinsan dalilin hakan tace allura suke yi Mata. Jiyoyin kan Jamal sunyi tashi zuwa lokacin idon sa sunyi ja mikewa yayi akayi saurin rikosa yace ku barni ku barni inje in kashe wancan shaidaniyar matar wallahi sai na kasheta tunda ta bakasa min Mata.

KURUCIYAR MINALΌπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα