CHAPTER 46

2.7K 228 9
                                    

Wasu hawayenne suka kuma zubowa Daga idanun ayush sannan ta girgiza kai tace sister zakiyya karki bani fake hopes Dan Allah kinsan namiji abin tsoro ne ta iya yuwuwa yanzu haka yana tare da amaryarsa ya manta dani.
Shafa kanta zakiyya tayi cikin murya mai laushi da nuna Cewa ta damu da yanayin da cousin dinta ta Shiga tace little sis have faith kinji ? I know that you are brave, ko sanda parent dinki suka rash you were so brave right ? Gyada kai ayush tayi zakiyya tace Toh kin bani you can go through it and kinyi trusting lukman dinki ko? Ayush ta kuma gyada kai tare da Cewa eh kamin wani hawayen ya silalo zakiyya tace good since have trusted him and you are sure that he loves you then there is nothing to worry about dago da manta tayi ta kalli zakiyyan tace are you sure?zakiyya tace 100% sure now give me a smile kinji?

Murmushin dole tayi zakiyya tace ko Ba ke bafa now tashi muje kick abinci.

Girgiza kai tayi tace banajin yunwa, hararanta zakiyya tayi tace zaki tashi ko yaya? Mikewa tayi tana Cewa sis wannan kallon ai sai ki cinyeni dariya suka fashe dashi kamin suka wuce dinning area domin cin da'am.

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

What!? Minal me kike nufi me zaisa in kasheki? Harara minal ta aika masa kamin tace abubuwa dayawa. Wato dama duk wannan abubuwan dakake min kanayine saboda in na mutu kar a zargeka?minal ta fadi hakan tana mai daga murya.

Tsawa yazeed ya daka mata ya daka mata yace banson hauka fah kodan kings ina Daga miki kafa shine zaki kawo mini rain in hankali ? In da inason na kasheki ne da tuni na kasheki.

Hararar sa tayi da rinannun idonta muryarta na rawa alamun zata iya fashewa da kuka at any moment tace amma wallahi bantaba nadamar aurenka Ba irin yau Nayi kuskure Dana yarda dakai Ashe Dama kai me kisan kaine? Ashe kasan abinda ka tanada shine harda cemin Wai mu zama abokai,Dama zaka iya min haka? zuciyata ta raurawa har yanzu na kasa yadda Cewa kanason ka kasheni, ya yazeed ka tasheni kacemin mafarki nake Ba dagaske bane,Ba kasheni kakeson yi Ba.

Tsintsiyar hannunta yazeed ya kama ya jata har izuwa bakin kofar dakinsa sannan ya wancalar da ita yace Anyi kokarin kashekin Kiyi abinda zaki yi sannan ya rufe kofarsa.

Wani irin zafi zuciyarsa ke masa Wai yau shi YAZEED ABDULMAJEED UMAR aka Cewa yana kisan kai? Da alamu sakarwa yarinyarnan fuskar da yakeyi ya janyo masa matsala.

Zaiyi kokari ya nisanceta ko tayaya ne domin ta fahimci kuskurenta sannan ta fada hakuri kamin ya yafe mata.

Wata zuciyar tace uhm tunda kuke da zakiyya ta taba baka hakuri ne inba tanada wani agenda ba.

Sai alokacin ya tuna da zakiyya yace ko ina ta Shiga oho bako waya? I will call her tomorrow.

Da sake sakennan ya fara bacci tare da aiyana irin azabar dazai ganawa Jennifer harsai ta fada masa Wanda yasata wannan aika aika.

.................

Minal ko yana rufe kofarsa ta fashe da kuka. Sanda tasha kukanta ya isheta sannan ta mike taja kafafunta jiki a sanyaye taje dakinta. Itakam ta Shiga uku da rayuwarnan da badan kartayiwa Allah butulci Ba da tace inama ta mutu Dan wallahi sanda wannan abun ya farune ta fahimci ta fada tekun son yazeed dukda ko bata tana yin soyaiya Ba amma dai ai tasha jin abubuwa akanshi gashi ita Ba takaddun Hausa take karantawa ba, wannan sai zaliha wani ajiyan zuciya ta sauke me nawi tunawa da zaliha da tayi ko yanzu a wani hali take oho, sai yanzu ta fahimci ciwon da zaliha keji.
Yanzu da ace ya yazeed ne ya zatayi? Dukda ko yayi kokarin kasheta wallahi itanasonshi a hakan ma. To kode tayi kuskurene? Kode bashi yakeson ya ya kasheta ba? Kode wani zancansa daban yakeyi ? Kai ya cancanta ta bashi hakuri sannan ta nemi Karin bayani tunda ko a musulunci babu kyau zato.

Kallon sama tayi tace astagfirullah Allah na tuba,nikam naga takaina karfa in mutu yau mijina na fishi dani.

Mijina? Kai Ahe ban taba kiransa da mijina ba ta fadi hakan tana Washe hakora Kamar ba ita ta gama drama yanzu ba.

Kai Gaskiya bani iya bacci in banbashi hakuri ba ta fada a magana zuci. Saukowa tayi Daga gadonta tare da Cewa gadona kar kayi kewata yanzu zan dawo kaji ? Kamar gadon yana jinta (typical me😂 yeah I have that kind of connection with my bed and phone.)

Sautin tafiyarta Kadai ke tashi saboda yadda gidan yayi shiru. Koda ta iso kofar dakinsa knocking tayi a hankali taji shiru ta sake knocking still shiru

Murda hannun kofar take shirin yi sai alokacin ta lura Cewa Ashe kofar batada Hannu sai wurin saka pin ta ciki ne akwai handle.

Nambobi ta fara daddannawa amma koda tayi sai uku duka wrong sai kofan yace bazata iya sa'a ba sai after 15 second itako da ba ganewa tayiba taci gaba da dadaddanawa.

.........................

Yazeed kwance a dakinsa har bacci ya fara daukarsa yajiyo taku na kara matsowa kusa da dakinshi kuma Idan ba kuskure yayi ba takun minal ne tayaya ta Shiga side dinsa ? Gush Ashe ya manta be rufe koda ba thank goodness kofar dakinsa in a rufe ba'a iya budewa ta sake sai ansaka pin da ace ba minal bace fa ?
Dawowa yayi daga tunanin da ya shiga jin minal ta fara knocking kamin kuma ta fara daddanna pin.

Yanaji machine din nata dit dit dit dit dit zu! Har sai uku alamun pin din ta is wrong amma yaji minal ta cigaba da daddanawa.

Tasowa yayi yazo bakin kofar yadda zaiyi magana ta jishi ba sai ya daga murya ba saboda girman dakin.

Yace ke dallah kibar nan wurin karki batawa mutane kofa aiko minal tanajin yayi magana tace ya yazeed Dan Allah ka bude Dan Allah baice Komai ba ya Koma yayi kwanciyarsa.

Minal ko jin shiru bai kara magana ba yasa ta jingina da kofar kamin tace Dan Allah kayi hakuri Nasan Nayi kusukure Dana zargeka ta fadi hakan tana shirin zubda kwalla.

Mamaki ne ya cika yazeed Wai hakuri ta bashi kuma ma da wur wuri haka ? Chabdi ai inda zakiyya ne wallahi saide ya mutu.

Baice Komai bayayi kwanciyarsa,can yaji Kamar shesshekan kuka wani zafi yaji zuciyarsa tamaisa amma ya daure wajen Cewa in kin gama kukan kibarmin side dina sannan karki sake ki kara zuwa inda nake.

Kuka ta fashe dashi tace Dan Allah karkayimin haka ya yazeed kayi hakuri bazan karaba.
Jin shiru yaji kulata yasa ta Koma dakinta zuciyarta cike da damuwa yanzu ita ta yaya zata bashi hakuri bayan yace bayason ya kara ganinta? Wani kukan ta kuma bingirewa dashi har bacci barawo ya saceta.

Good morning na cika alkawari,please make sure you spread a smile on my face comment and vote fah

Have a good day bye

Miss untichlobanty💕

28 November, 2019

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now