CHAPTER 32

2.9K 232 4
                                    

Sama ya haura direct dakin minal ya Shiga ya sameta tana ajiyar zuciya yace follow me

Ta dago idanunta ta kallesa domin neman karin bayani wani electric shock sukaji dukkansu biyu kamin ya waske ta hanyar Cewa ko bazaki iya zuwa bane kin kafeni da inu munafuka?

Shiru still tayi ya fice itama ta bisa subul subul tana mai gyara zaman yellow hijabinta
Koda ta shigo dakin akan coach ta samesa zaune ya daura daya akan daya yace bazaki iya karasowa bane?
Ahankali ta tako a tsure dukda bata bayyana hakan Ba ta tsaya a Dan gefensa
Yace closer tare da mata alamu da hannu ta Dan kara matsowa harara ya buga mata tare da Cewa cinyeki zanyi ta girgiza kai tana mai karasowa da Dan Sauri tsayuwa tayi a kansa
Ya kamo bakin hijabinta ya janyota kasa
Dan kara ta saki domin hijabin ya Dan kurji gefen wuyanta kana visa kuskure ta Dan taka kafarsa kamin ta zube,yace Dan kaniyarki haka zaki tsaya akan yayanki ta girgiza kai yace bakida baki ne tace a'a

Harara ya kwada mata yana mai hadawa da rakwashi kwas a tsakiyar kanta yace bakisan in antaka mutum hakuri ake basa Ba?girgiza kai tayi alamu tasani tana rarraba idanu Dan rankwashin ya shigeta

Janyota yayi ya matse cute pinky lips dinta  yana kalla yace wato gani sarkin mahaukata ko ina magana kin bawa banza ajiyata

A hankali hannunta na rawa ta daura akan nashi alamun ya sake bakin zatayi magana idanunta ko ya cicciko da hawaye saboda radadin da bakinta ke mata shikuwa wani yaaaam yaji Ba shiri ya saki bakin kana ya kauda kansa gefe domin jin bananarsa na kokarin kawo masa raini

Ahankali cike da in'ina tace kayi hakuri na taka ka,tsika jikinsa suka mike gabadaya yayinda hawayen da taketa boyewa ya samu nasarar saukowa

Ba tareda ya kalleta Ba yace nace miki kimin wanki shine Dan kin rainani ki kamin jika jika ko?

Muryarta na rawa tace wallahi me kyau Nayi kaga hannuna ma ta nuno masa gefen hannunta yadda yayi jaa Kamar ka taba jini  ya fita tsabar yadda ta dirji kayan

Tsaki yaja yace raguwar banza dan kin wanke singlets 3 da boxers 3 Wanda nasa jiya shine zakina wani nokewa Kamar marainiya

Batasan lokacin da tace aide nafi wasu juyowa yayi adan zabure Dan baiyi expecting ta mayar masa da magana Ba
Hannu yasa ya bige bakinta yace zaki tashi kibar gefena ko saina maujeki in canja miki halitta.

Da Sauri tabar dakin tana mai zubda kwalla,lallai tayi kuskuren amincewa da zancen auren Ba tareda ta saurari ko Waye su baba zasu aura mata ba sai a yanzu ne take kara ganin wautarta

Dakinta ta koma ta tsaya agaban madubi tana kallon yadda tayi kyau dukda kuwa ko petroleum jelly bata shafa Ba balle powder amma idanunta sundan fada ciki sannan ta zama kalar tausayi babu walwala a tattare da ita.

Haka rayuwa taci gaba wa minal yanxu har tayi wata 3 a gidan captain  tanayin aikinta Kamar kullum once in a while sukan hadu da zakiyya inta gama banbaminta minal kawai ce mata take Allah ya baki hakuri sannan ta wuce itako zakiyya babu abinda ta tsana Kamar tayima rashin mutunci ka nuna bai dameka Ba Dan haka sai tayita kumfan baki tana cika tana batsewa

Minal ko gani takeyi Kamar zakiyya taci noti kuma tana bukatan Sabo hakan yasa bata tanka mata har tayi ta gama

Aunty fauzy ta kawo mata ziyara har sai biyu Inda take kara jaddada mata girman aure da kuma yadda zata zauna da abokiyar zamanta lafiya. Ita dai minal kunne kawai ta kasa Cewa komi aranta ko tana Cewa cab ai bakisan halin abokiyar zaman tawa da mijinta ba da ko zancenta bazakiso muyi ba.

Yau saura 3 days auren zaliha Inda gobe ne za'ayi kamu
Minal nason tambayar captain izini tun last 2 weeks amma tsoro take yau kam shahada tayi ta turo kofar dakin da yar sallama a bakinta aiko abinda ta gani shi ya Daga mata hankali captain ne ya fito Daga wanka Daga shi sai gajeren wando fari kal da bathrobe Wanda ya barshi haka ba tare da ya daure igiyan ba wanda yayi sanadiyyar Nuna dukkan ilahirin faffadar kirjinsa mai dauke da gashi kwance luf luf Wanda keda laushi hamar gashin kan jariri.

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now