CHAPTER 73

3.4K 211 61
                                    

Haka duka dinga musu daga karshe zakiyya tace taji ta yarda ta dan fara sonshi amma kar minal ta fada ma kowa.

Da daddare minal na dakin yazeed tana  hada kayan tafiyansu domin karfe 2 dare jiginsu zai tashi yazeed yace baby kin taba hawa jirgin sama girgiza kai tayi yace tab ai kina hawa ki fara tunowa da Allah Dan idan ba ragewa da addu'a kukayi jirgin kifawa zai daku yayi adungure sallar mage. Zaro ido tayi tace kace Allah? Dariya yayi yace zan miki karya ne? Girgiza kai tayi kayansa ta hada masa kaf shiko ya cigaba da game dinsa can yaga kamar  bata saka nata kayan a box din yace a wani akwati zakisa kayanki ne girgiza kai tayi jiki a sanyaye. Alamu ya Mata da tazo, ta taho kafafunta na hardewa. Zaunatta yayi a tsakanin kafafunsa yace ya akayi ? Danshi yama manta da cewa ya tsokaneta dazu.

Muryata na rawa tace na fasa tafiya ne. Tace kamar ya kin fasa tafiya ? Me yasa? Kuka ne ya kwace Mata tace ba kai kace jirgi zaiyi adungure sallar mage dani ba? Dariya ce taso kwacewa yazeed amma ya matse kwantarta yayi a jikinsa yace ai ba kowani lokaci bane yake kifawa sai idan masu zunubi sunyi  yawa a ciki, bakiji nace kiyi addua ba? Kallonsa tayi tana goge kwalla tace nidai gaskiya bazan shiga ba kawai mu fasa tafiyannan. Zaro ido yayi yace ku fasa kuma? Idan mun fasa toh ya batun babies dinmu ? Alamun tunani tayi yayinda yaketa kunshe dariyarsa. Tace toh ka tafi kai daya, turo baki yayi yace dama bakya sona? Girgiza kai tayi tace toh tare zamu tafi. Wani kwalla ne ya sake tsiranyowa daga fuskarta har tausayi ta bawa yazeed. Haka ta hada kayanta tana kuka dan gani take daga daren yau sunanta gawa. Tunanin zucin da take ne ya baiyana. Tace oh su nima an zama labari, Dariya ce ta kufcewa yazeed yayi saurin mayar da ita tari.

Haka suka kwanta tare da saita alarm din karfe 12:00am minal kam ta kasa rintsawa sai juyi take tana lissafa abubuwan alkairin da tayi wanda take iya tunawa,ajiyan zuciya ta sauke tace da sauki ma ko na mutu ina sa ran shiga aljanna. Yazeed yana Jinta domin shima baiyi bacci ba Dan sai nuku nuku take a jikinsa ga ruwan hawaye dake jika masa Riga. Haka alarm ya kada suka tashi suka shirya minal sai kuka take tana fadin ni banason injeeee😭😭!  Koda sukaje yiwa mom sallama taga yanda idon minal ya kumbura tace lafiya ko bakida lafiya ne? Shiru tayi tana tsittsilla ido kamar mara gaskiya yazeed yace cikinta ne yadanyi Mata ciwo amma gashinan dai yanzu tasan warke. Mom tace toh Allah ya kara sauki a ya stare hanya haka kowa ya taso akayi musu rakiya har airport bayan anyi clearing dinsu kamin su wuce ne minal ta kebe da zakiyya. Suna shiga toilet din zakiyya tace lafiya minal tace don Allah zakiyya kin taba shiga jirgi ko? Zakiyya tace sosai ma kuwa wani abin ne? Tace wai da gaske ne yanayi 'kolin 'koli da mutane ya 'kwala da kasa. Zakiyya tace wa ya fada miki? Idonta ne ya ciko da hawaye tace yazeed ne. Zakiyya ta gane franking dinta yayi shiyasa tace ehhh toh bai fiya yi ba amma dai id.....

Kuka mai karfi minal tasa hakan ya hana zakiyya karashe maganarta, nan fa tahau lallashi ana cikin haka yazeed ya Kira wai suna inane? za'a fara boarding.
Koda suka zo kasa kasa da murya zakiyya tayi tace Allah kaide yazeed bakada Kirki dubi yadda kabi duk ka ruda yar mutane. Dariya yayi kasa kasa tace zakiyya kenan babu ruwanki media kice na tuna miki da sanda na tsoratar dake akan tsaka. Dariya sukayi a tare tunowa da yadda zakiyya ta rude lokacin hannu ta daga zata makeshi kamin ta tuna da cewa ba mijinta bane. Hakan yasa dariyar fuskassu ta dauke murmushi tayi tace Allah ya kiyaye hanya make sure idan zaku dawo ku dawo da mai dadi, ku tafi ku biyu ku dawo ku uku. Jinjina kai yayi yace da izinin Allah daga nan ya kamo hannun minal suka wuce.

Koda fa minal taga jirgi da girmansa sai hankalinta ya kara tashi. Cije wa ta fara yi yazeed yana janta yace ke menene haka wai? Hawaye na  dawafi a fuskarta tace nace na fasa, wallahi na hakura. Dafe kai yayi yace AI ba komawa yanzu kina komawa za'ace ke yar boko haram ce. Tace toh ai ni matarka ce kuma ai soja bazai zauna da yar boko haram ba. Yace toh ai karin matsala kenan cewa zasuyi na kasheki a take kawai a huta kuma kinsan bazan iya ba kinga za'a ce mun hada baki sai akashemu duka biyu kinaso a kashemu? Tace a ah yace toh maza muje haka suka shiga kirjinta na duka dib! dib!! dib!!! dib!!!! dib!!!!! dib!!!!!!

KURUCIYAR MINALWhere stories live. Discover now