CHAPTER 64

3.9K 259 28
                                    

Koda suka shigo gidan zaliha na kokarin fita Daga motan luku ya riko hannunta kyam wani yar sukaji amma bai saka ba saima harara daya banka mata. Kiciniyar takeson masa ya mata rikon maza mom Suna fita ya zama saura su biyu ya lafta lock. Wancalar da hannunta yayi yace Menene ma wannan tsiyar hannun naki Kamar muruci? Tsaki taja tareda fadin dalla malam budemin mota na fita.
Banson wulakanci baza'a kwana a gidan naka ba ana dole ne?

Take motar yayi Wanda yayi sanadiyyar da yasa zaliha fasa baki tare da Kwandale kai a window kicin kicin tayi da ido kamin tace kane bala'i na rantse da Girman wallahi Bashi Idan ba saina rama ba me nake.

Daidai lokacin suka iso Dan haka ya fice yana fito kallon part dinsu zaliha ta tsaya yi ba karya ya hadu. Ko nasu minal saide ya Nuna musu girma da tsadan kayan furniture amma saboda hali irin nata tabe Baki tayi tare da fadin saboda wannan tsiyar gidan aka raboni Dana iyayena.

Shrugging yayi yace Aike rayuwarki tsiya tsiya ne iyayenki ne kawai na arziki.

Tsabar tsiya sadakarki aka bani kuma na kawoki matsiyacin gida zaki kare matsiyacin rayuwarki acikinsa tareda matsiyacin mijinki. Ya fadi hakan yana mai mata murmushi.
Iya shaka kam ta shaka kuka ta fara tare da fadin Allah ya isa na nikam an cuceni wallahi da aurenka gara Lauren kolo. Wannanta wuce bazar bazar ta mangajeshi ta fada wani Daki yace jeki dama nanne dakinki. Leka dakin yayi ya ganta kwance kan gado tana kuka yace my wife dagowa tayi tana aiko masa wani harara kiss yayi blowing  Mata tare da cewa kayanki na wardrobe ayi kuka lafiya sannan ya fashe da dariya. Tasowa tayi kamar zakanya. Yayi saurin rufe Mata kofa dadai zai fita daga side dinsu yaga minal tana shirin shigowa hannunta rike da sahir da safwan....

🌹🍀🌹🍀🌹🍀🌹🍀

Su minal suna Shiga gidan su suka labe suna kallon abinda su zaliha keyi dafe kai yazeed yayi yace gosh wai ace bazasu taba yin shiri ba ? Dole ne mu hada kansu. Miko Mata hannu yayi yace plan karba tayi sukayi musabaha tace yes plan.

Daughter! Daughter! Mom ke kwalawa minal Kira tana fadin zoo ki tayani kunce kayana in baki tsarabarki. Zata tafi yazeed yayi saurin rokita kamin tace mom zatazo anjima yanzu ina bukatar matata.

Lekowa tayi ta sama tace iyeeee mai mata manya. Umm Nide kada ka riketa dayawa yafi awa daya Dan yunwa mukeji kuma abincinta mukeso. Zaro ido yayi yace mom bafa haka nake nufi ba magana zamuyi fa sai in danji duminta. Dariya mom tayi tace zama kayi bayani Nide na fada maka.

Sannan ta Koma tana mai jinjina halin rashin kunyan yazeed don atunaninta wani abar za'ayi.

Yazeed ko minal yaja zuwa kitchen wadda duk kunya ya rufeta saboda ganin da mom ke mata.
Fuskar yara ya mata yace babe kiyimana pancake dinki muci please.
Gyada kai tayi ta fara hado abubuwa sai murmushin jin kunya take yazeed ko daya hau kan island ya zauna tareda dauko wayarsa yanata daukar  hotonta tana aiki saide duka fuskarta bai fito ba.

Ajiyan zuciya yake sauke wa yawunshi har tsinkewa yake yace kai nikam ataimaka min na fara cin nawa. Zuba mai tayi ta bashi zata Koma taci gaba da suya ya riko hannunta cikin shagwaba yace ni kibani a baki.

Hannu tasa ta taba goshinsa da wuyarsa ba zafi. Yace yadai tace na dauka bakada lafiya ne naga kana Abu Kamar baby. Yace aini Babyn ki ne kashe gas cooker din tayi ta dawo ta zauna a gefensa bayan ta dauko juice da honey da lemon. Tace da wanne kakeson honey ko lemon yace lemon dinde saboda tsami tsami.

Haka tayi ta bashi sunaci Suna hada plan din yadda zasu hada kan su zaliha da lukman da kuma yadda zasu gudanar da bikin su Abubakar Dan sun dano taragonsu.

Saide kash bansamu Dakar mina  abinda suke Cewa ba saboda ina can ina satar pancake dan  Nasan ko na tamabaya yazeed bazai bani ba tsabar santi Dan naji lokacin dayake Cewa in so samune minal ta bashi duka pancake din sai ta dafawa su mom wani abincin.

KURUCIYAR MINALМесто, где живут истории. Откройте их для себя