🌷Shafi na 18🌷

Start from the beginning
                                    

Seat belt din da ke jikinta Jasmine ta cire ta matso idan Alamin yake, Chocolate din ta kai daidai bakinsa tana kallon fuskarsa tace "Have it,"
Bude baki yayi ta saka masa ya ɗan gutsura sannan ta saka daya hannun nata tana goge masa chocolate din da ya goga a gefen bakinsa. Hankali Alamin daukewa yayi daga kan tukin da yake dan bai san sanda ya cika wheel din motar ba tayi gefe da sauri ya taka brake din motar ta tsaya.

Lumshe idanunsa ya yi ya jingina kansa a jikin kujerar motar. A hankali ya bude idanunsa ya kalli Jasmine ta zaro idanu tana kallonsa " Are you alright?" Ya tambaye ta.

Gyda kai tayi ba tare da tace komai ba, suka cigaba da tafiya.

"I'm sorry," Jasmine ta furta a hankali kanta a kasa.

Juyowa yayi ya kalleta yace "It's not your fault,"

Shiru tayi bata sake cewa komai ba tana tunanin ita ta janyo accident din da suka kusa yi. Ganin babu walwala a fuskarta yasa Alamin cewa "Ya naga kin yi shiru, kodai boredom din ke danunki?"

"Aa, bana son na sake distracting dinka ne,"

"Uhm.. Amma idan kika yi shiru kuma ai bazan ji daɗin tafiyar ba,"

Murmushi Jasmine ta yi "Alright, toh muyi 20 questions mana." ta juya tana kallansa.

"Meye twenty question?" ya tambayeta.

Zaro idanu tayi ta bude baki tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba, juyowa Alamin yayi yace mata, "Meya faru?"

"Wai da gaske kake bakan san twenty questions game ba," Ta tambayesa.
"Yeah." Ya bata amsa.

"Well it's a game, kaman true and dare game. Sai dai wannan babu dare kawai zan tambayeka 20 questions ne kaima zaka tambayeni that's it, amma dole ka fadi gaskiya kuma banda yin shiru ko ka biya."

Murmushi Alamin yayi yace "If that's it, I'm ready." Ji yayi yana son game din saboda shima yana son ya san wasu abubuwan game da ita.

"Okay, Tambaya ta farko wacce kasa kafi so a cikin duk kasashen da ka taba ziyara." Ta tambaye shi.

"Saudi Arabia, kefa?" Shima ya tambayeta.

"New Zealand, I won't mind living there forever," Ta bashi amsa.

"Whoa, have you ever been to KSA?" Ya tambayeta, dan shi babu kasar da ke burge shi kuma yake sha'awar rayuwa a ciki kamar Saudiyya. Dan a idanunshi ta fi kowacce kasa da ya taɓa ziyara kyau da kwanciyar hankali.

"Ban taba zuwa Saudiyya ba, but In na son zuwa watarana in the nearest future." Ta bashi amsa.

"Wait, kina nufin baki sauke farali ba. Yasmine, I'm curious why?" Alamin ya tambaye ta cike da mamaki.

Lumshe idanunta Jasmine ta yi ta bude sannan tace "Allah ne bai yi zan je yanzu ba,"

Gyda kai Alamin yayi "Hakane," juyawa yayi ya kalleta yace"Amma how many countries have you been to?"

"It's actually 50 countries. Kaifa," Ta bashi amsa.

"120," Ya bata amsa.

Zaro idanu tayi tace, "Ka kusa zagaye duniyar,"

"Ni na isa," ya faɗa yana dariya.

"Next question."

"Nina manata ma we area doing what did you call it."

"Twenty questions," Ta bashi amsa tana masa dariya saboda ya manta. "Any phobia?"  Ta tambaye shi.

Dariya Alamin yayi yace, "Actually yes, amma lokacin ina yaro neh, yanxu bani da wata Phobia. Kinsan wannan dolls din da mata ke wasa dasu?" Ya tambayeta.

Gyda kai tayi alamar eh. Sannan ya cigaba da magana. "Lokacin muna yara Yaya Hafsat tana da su da yawa and a lokacin ina da Pediophobia (fear of dolls)." Murmushi yayi dimple dinsa ya fito sosai "Kinga idan Mummy nason hana ni abu tofa da dolls dinnan take tsorata ni. Watarana muna faɗa da Yaya Hafsat ta dauko wannan ugly dolls din nata tana shuna min, ni kuma tsabar tsoro na yanke jiki na faɗi, tun daga ranar Abba yasa aka zubar da duk dolls din gidan sai teddies kawai aka siyo mata ta koma wasa da su, amma har yanzu bana son dolls, sai dai bana tsoronsu."

Cikin dariya Jasmine tace, "Oh my goodness, The great Alamin Attah na tsoron yar tsana."

Yar karamar dariya Alamin yayi yace, "Kin sami abun tsokana ta ko? To ke mece taki Phobia?"

"Astraphobia(fear of thunder and lightning), shiyasa lokacin ruwa bana fita saboda tsawa."  Ta bashi amsa. Sannan tace, "Next question, meye favorite Color dinka."

Murmushi Alamin yayi yace, "I love four colors, White, Green, Blue and Black color."

Shiru ta ɗan yi, fuskarta dauke da murmushi tace "Favorite colors dinka daya da Matthew, ni na rasa meyasa maza keson Black and Blue haka Jamal ma."

"Waye Matthews?" Ya jeho mata tambayar kamar bai san waye Matthew din ba.

Murmushi ta danyi "He's mt Best-friend and Boyfriend, shi zan Aura."

"Matthews," ya maimaita sunan "Kaman Christian name ko?"

"Yeah, he's a christian." Ta bashi amsa ba tare da nuna damuwa ba ko kadan.

Shiru Alamin ya danyi lafin yace "Anya ko kinsan cewa babu Aure tsakanin Mace Muslima da Christians." Alamin ya faɗa hade da zayyano hujjojins cikin Alqurani da Hadisi. Sannan ya kalleta yace "Meyasa kike son sabawa mahaliccinki Yasmine, ya kamata ki sani matukar bai musulunta ba, babu zanchan aure tsakaninku."

"Muhammad I don't want to talk about this. This is my personal life, let it go."Jasmine ta faɗa a dan fusace domin tasan abinda ya faɗa mata gaskiya ne, babu Aure tsakaninta da Matthews sai dai idan zai musulunta, duk da irin soyyayyar da sukewa juna.

 
Cigaba da tafiya sukayi shiru babu wanda ya kara cewa komai, Alamin ko kokarin yi mata magana bai sake  yi ba saboda ya fuskaci ranta ya baci tunda yayi mata maganar Matthews. Duk da yasan ko da da addini ya bata damar auran Matthews shi ma bazai iya rabuwa da ita ba.

Jasmine gabaki daya hankalinta komawa yayi kan Matthews, gabaki daya rasa sukuni. Tasan dole idan ta koma UK sai sunyi wannan maganar da shi, abunda take gudu dole ya faru.

Dan tasan yin wannan maganar daidai yake da alakarsu na lilo a ko da yaushe zata iya kifewa ta faɗi. Tafi kowa sanin halin masarautar Ingila, ko da yana son ya chanja addinin baza su bar shi ba.

Merry Christmas and Happy New Year in advance to all who celebrate.

May your hearts be filled with love and happiness.

Amiratuoo

Much love ❤️

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now