🌷Shafi na 18🌷

3.1K 208 28
                                    

Gari yana waye wa Jasmine ta sauko kasa da gudu har tana tuntube, ta tuna cewa yau su Basma zasu koma Kano tana son ta bisu sai dai kuma jiya shaf ta manta bata gayawa Alamin ba, a bakin kofar Gym room dinsa ta tarar da shi yana fitowa sauran kadan ta bige shi saboda irin saurin da take ko gabanta bata gani dan yayi baya da sauri ne da sunyi karo.

"Saurin me kike haka, ko dai kasar zaki bari ne." Alamin ya tambaye ta.

"Garin nan dai," Jasmine ta bashi amsa sannan ta cigaba da cewa, "Mantawa nayi jiya ban gaya maka ba, yau su Basma zasu koma Kano and tare nake so mu tafi da su." ta faɗa cikin sauri "Gashi morning flight ne."

"Sun kira ni dazu when you didn't picked their call, su riga sun tafi." Alamin ya fada yana kallonta.

Kanta ta dafa tace "Ya Sallam, meyasa baka kirani ba,"

"Lokacin kina bacci and I can't just wake you up,"

Nufasawa tayi tace "Okay, zan kawai bi evening flight ko kuma can I use your jet," 

"Why not na kaiki a mota mana, tunda kinga daman ba sanin gari kika yi sosai ba sai ya zama kaman sightseeing. It will be an adventure." Ya faɗa yana kallonta.

Shiru Jasmine ta dan yi sannan tace "Long drive kenan, I am in. Daman na dade banyi tafiya mai nisa a mota ba, it will be so much fun but not with this grumpy mood of yours." Jasmine ta faɗa tana dariya tare daga yatsa ta nuna fuskarsa da babu fara'a akai tace masa "Smile, ya kamata ka ringa yawan murmushi, you look handsome when you do. But that grumpy face babu inda zan bika."

Murmushi kawai yayi yace mata "Ki je ki shirya, mu tafi da wuri."

****

A booth din Prado Moji ta saka ma Jasmine kayanta ta rufe itama Jamine ta shiga cikin motar. Har Alamin ya kunna motar tayi saurin tsayar da shi  tace "Kana da cash a hannun ka amma Naira? Please."

"Yeah." Kawai Alamin yace sannan ya bude wani dan compartment a cikin motar cike da bandirbandir din kuɗin Naira da dollars yace mata "Dauki adadin da kike so,"

Murmushi Jasmine tayi ta dauki bandir biyar na Naira dubu sannan ta fita daga motar, Mojisola ta kira tace ta kira mata sauran ma'aikatan gidan, su jira ta a wajen motar zata je ta dawo. Bangaren su Mama taje ta yi masu sallama  dan tasan ba sake dawowa zatayi ba, sannan ta dauki dubu dari uku ta bata. Tana dawowa kuwa tarar da  Moji ta tara mata ma'aikatan gidan, su hudu ta dauki dubu dari biyun da ya rage a hannunta ta basu su raba.

Tana shiga mota Alamin ya ja motar suka yi gaba. Bayan sun fara tafiya ne Jasmine ta bude jakar ta ta dauko Five hundred thousand dollars a ciki  ta mikawa Alamin tace "Ga kudinka." Murmushi yayi ya kalli kudin sannan yace mata "Kin ko san nawa ne wannan kudin a Naira."

"Aa." Ta bashi amsa a takaice.
"Toh ki rike abinki zasu yi miki amfani watarana." Ya faɗa kansa a kan titi yana tuki.

"Wait, wai kana nufin baza ka karba," Jasmine ta tambaye shi tana kallonsa.

Murmushi kawai yayi yace "It's just 500k not a big deal, and na san kyauta zaki yi da su shiyasa, Mama kika bawa right."

Cikin harshen spanish tace "Ella es una buena mujer la extranare" (Mutuniyar kirki zan yi kewarta)

"Por esmi madre la ama, pero ella es halbladora pero hablas mas que ella como un loro,"  (Shi yasa Mahaifiyata take sonta, sai dai akwai ta da Magana ko da yake kema ai kamar aku kike)
"Ai koh bani da surutu Jamal ne ya faɗa maka ina da surutu ko." Jasmine ta faɗa tana turo baki.

Murmushi gefen baki ya dan yi sannan yace "Sai an faɗa min bayan ga zahiri ina gani, Yasmine baza ki iya 30 minutes ba tare da kinyi magana ba fa."

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now