🌷Shafi na 16🌷

2.8K 192 19
                                    

Karfe 10:00pm daidai driver ya sauke Jasmine a gida, shiga ciki tayi tana taku a hankali dan a gajiye ta dawo saboda irin yawon da sukayi da su Basma. Bayan sun bar wajen taron gidansu Safna suka koma achan sukayi wanka suka chanja kaya, Basma ta ara ma Jasmine doguwar riga ta saka, suna cin abinci suka fita yawo, basu su suka dawo ba sai wajen karfe 7:45pm na dare, a nan suka ci abincin dare suka yi sallah sannan suka dasa wata sabuwar hirar, har dare yayi sosai Jasmine bata koma gidan Alamin ba saboda hankalinta gabaki yana kan hirar, da kyar ta tashi taho ba a san ranta ba, Alamin ba kula ta yake ba bare suyi hira haka zata zauna ita kadai sai yan aikin gidan. Yanzu ba daman ta zauna a gidansu Safna cikin kawayen saboda kawai ta auri Alamin ranta a bace ta shiga cikin gidan.

A falo na biyu Jasmine ta tarar da Alamin zaune da wayarsa a hannunsa, sallama tayi ya amsa mata a hankali ba tare da ya dago ya kalleta ba, shige shi tayi bata kara cewa komai ba bayan sallamar zata hau sama, maganarsa ce ta dakatar da ita ta dawo baya don har ta fara taka stairs din "Daga Ina kike?" kallonsa tayi taga har yanzun bai dago kansa ba, idanuwansa suna kan wayarsa.
"Taron Breast cancer awareness muka je." Ta bashi amsa a nutse.

"Sai yanzu aka gama taron kenan," ya faɗa har yanzu kansa a kasa bai dago ba.

Bata rai Jasmine ta dan yi tambayoyinsa sun fara isharta "Daga nan munje gidansu Safna ne and other places." ta bashi amsa.

"Other places? Ni ban ma san zaki fita ba ai, meyasa baki gaya min ba?" Alamin ya tambayeta.

"Is that necessary? dan na fita ban faɗa maka ba ai ba wani abun bane, beside naso na gaya makan ma amma baka nan," Ta bashi amsa fuskarta babu walwala.

"Okay, shigar da kika fita da ita kuma fa?" ya kara tambayar ta,
Shiru tayi masa bata bashi amsa ba hakan yasa ya dago kansa ya kalleta, ita kuma ta kau da kanta tayi banza da shi kamar bata ji me ya ce ba. Sanin ba zata yi magana ba ya saka shi ya cigaba da cewa "Jasmine wai meyasa bakya son yin dressing decent ne, you're a Muslim for God sake."

Turo baki Jasmine tayi sannan tace "Jeans, Shirt and a P-cap ni banga wani abun a kayan da na saka ba, it's just a casual dressing ba fa bum shorts da crop top na saka ba, kuma ma ai naga ba ni kadai bace nayi irin wannan shigar ba a wajen, they're many others."

Shiru ya danyi yana kallonta domin ya fuskanci itama tana dan kamshin gaskiya a maganar tata, tunda a UK ko USA dressing dinta is casual kowa ma haka yake yi baka gane Muslim and Christians daidaiku musulumai ke sa zama hijabis a cikin turawa sannan itama baturiyya ce kuma a haka ta taso, sai dai ta kasa fuskantar cewa yanzu a Nigeria take kuma ita musulma ce ba Christian ba, kallonta ya sake yi a hankali ya cigaba cewa "Yasmine, nan ba UK bane, yanzu a africa kike Nigeria, a Nigeria ma Arewacin ta a nan aladar da addinin mu na da karfi, akwai abubuwa da yawa da bama yi anan ko da ko halak ne a addini saboda Al'adar mu, balle kuma babu aladar da yarda da fidda tsiraici, and ko me kika yi anan ni duniya zata zaga coz I'm your husband."

"No entiendo lo que quieres decir, qué tipo de país es este,"  (Bangane me kake nufi bah, wannan wani irin gari ne). Jasmine ta mayar masa cikin harshen Spanish.

Wayarsa ya mika mata, ta kalli wayar ta kalle shi sannan ta karba, tana karba yace mata " You've been trending online akan shigarki a Twitter, Instagram and Facebook, you can see for yourself."

Tashi yayi ya haye saman bene ya barta da wayarsa a hannunta tana ganin irin abubuwan da mutane ke faɗa a kanta, wasu na zaginta wasu kuma na kokarin kareta, wasu na cewa yar gayu ce ita suna yabonta, wasu kuma Alamin suke soka akan ya bar matarsa ta fita da irin wannan shigar, wasu kuma cewa suke daman ai addini na talakawa ne domin masu kudi ba bin dokokin addini suke ba, wasu kuma cewa ma suke ita ba musulma bace tunda daman da Jasmine Alejandro take amfani kuma bata sa Mahmoud a sunanta, wasu har hutunan ta da tayi a chan England da Spain suka ringa dorawa saboda irin shigar da tayi a cikin hotunan, maganganu gasu nan kalakala, bloggers sai posting suke yi akanta, gani tayi wasu har tarihinta ma suka binciko, Dan har wasu na cewa daman Babanta arne ne bai dade da tuba ba, ita duk cikin maganganun nasu ma babu wacce tafi damunta da bata mata rai kamar wadda suka sako Babanta a ciki.

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now