🌷Shafi na 53 🌷

164 18 1
                                    

   Jasmine na zaune a kusa da Basma akan lallausan carpet din da ke falon Marigayi Alhaji Yunus, suna jiran Alh Muaz ya shigo. Gabaki daya ahalin gidan na falon harda su Hajiya Saratu, mahaifiyar Nadia da ya'yanta, da ma sauran yan'uwa da suke zaune a gidan.

Shigowa Alhaji Muaz yayi tare da Alamin. Bayan sun zauna Alh Muaz ya bude taron da sallama tare da yi adduo'i sannan ya fara zayyano dalilin tara su da yayi akan makomar Gidan da halin da ke cikin Gidan.

Ya fara magana akan rigimar da Hajiya Saratu take yawan jayowa. Yana fara maganar Hajiya Saratu fara kokarin kare kanta, taso yin chachar baki da Alh Muaz amma yaki biye mata bayan ya sanar mata da cewa zai shigar da ita karaa muddin ta sake tada hatsaniya acikin Gidan tunda bata da gadon Gidan, sannan ya bata yan kwanaki kadan ta kwashe kayanta ta bar gidan ko kuma su hadu a kotu.

Alh Muaz ya kara sanar da cewa kafin Alh Yunus ya rasu ya bar wasiyyar cewa wannan Gidan da suke ciki bana gado bane gidane dan ya gina shi ne saboda Mahaifiyarsa, Ya'ayansa da yan'uwansa da ma marayu kowa zai iya zama acikin gida muddin bashi da muhalli. Bai yarda a siyar da Gidan ba ko kuma a sashi acikin rabon gado. Sannan ana gama hada dukiyar Alh Yunus za'a rabata ga magadansa.

Da yawa daga cikin yan'uwansa mazauna cikin gidan suyi farin ciki matuka da jin wasiyar Alh Yunus saboda kusan duk marayu ne, yayan yan'uwansa ne da su ka rasu da kuma wayanda ma iyayensu basu da karfi sosai. Addu'a Alh Mu'az yayi sannan ya sallama kowa banda Nadia da mahaifiyarta, Hajiya Saratu, Anty Hafsah da Alamin. Har Jasmine ta tashi zata fita Alh Yunus ya kira ta, ta dawo ta zauna.

Idanunsa Alh Muaz ya dago ya kalli Nadia, juyawa yayi ya kalli Alamin. Alamin ya mike ya fita dan ya gane me kawun nasa yake nufin. Bai jima da fita ba sai gashi nan ya dawo da tare da Sabir a biye a bayansa.

Nadia tana ganin Sabir gabanta ya yake ya fadi sai dai bata nuna hakan akan fuskarta ba, mazewa tayi ta sa a ranta babu abunda zai faru tunda ai ba yau Sabir ya saba zuwa gidan ba.

Bayan sun zauna Alh Muaz ya kalli Nadia yace "Nadia menene alakarki da ke tsakanin ki da Sabir?"

Zaro idanu Nadia tayi ta hadiyi miyau rashin gaskiya "Babu komai Kawu," ta bashi amsa kanta a sunkuye.

Hannu Alh Muaz yasa a Aljihunsa ya ciro bandir din sabbabin kudi guda biyu ya mikawa Nadia yace "Ungo, karbi wannan." hannu biyu tasa ta karba sannan yace "Kudin sadkin ki ne, dazu da safe waliyyan Sabir su zo, mun tattauna dasu bayan sallar Asr za'a daura muku aure."

Da sauri Nadia ta dago idanunta tana kallon kawun nata baki a buda saboda tsabage mamaki ko motsi kasa yi tayi. A take idanunta suka ciciko da kwala cikin yan mintuna ta fara kuka mai karfi.

Tsawa Alh Muaz ya daka mata sannan ya dakatar da Hajiya Saratu da ke kokarin shiga cikin maganar tare da tunatar mata da cewa ita fa yanzu bata cikin ahalinsu, daman chan kuma Alh Muaz da Hajiya Saratu ba shiri suke sosai ba.

Bakin ciki ne yasa Hajiya Saratu ta tashi ta fita daga part din bayan tayiwa yar'uwarta mahaifiyar Nadiya signal. Tana fita mahaifiyar Nadia ta mike tsaye tana cewa "A gaskiya ba a yiwa ya'ata adalci ba ta yaya za'ayi mata auren dole, a aura mata mutumin da bata so jibi yadda take ta kuka,"

A hankali Alh Muaz ya daga idanunsa ya kalleta bai ce mata komai ba ya juya yacewa Jasmine "Ya'ata bata yarinyar nan ta,"

Zaro idanu Jasmine tayi tana kallonsa ya kara cewa "Bata ya'arta."

Ba tare da tayi musu ba Jasmine ta mike ta nufin Nadia ta mika mata ya'arta ta karba sannan ta koma ta zauna.

Bayan Nadia ta karbi Ayesha Alh Mu'az ya kalleta yace "Zaki gayawa mahaifiyarki mahaifin yarinyar nan ko sai shi ya faɗa mana da bakinsa,"

Jasmine Baturiyya ceUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum