🌷Shafi na 50🌷

241 22 3
                                    

Heidelberg University Hospital

Babu abunda suke in banda sintiri a cikin hallway din asibitin suna jiran likitocin su fito daga dakin da aka shigar da mahaifinsu. Ga kujeru sosai a hallway din amma duk sun kasa zama.

Ba'a jima ba likitocin suka fito daga cikin dakin, gaba dayan su suka nufi dakin har rige rige suke a bakin glass window dakin suka tsaya. A wance suka hango Alh Yunus, idanunsa a rufe kamar yana bacci an jona masa wasu wayoyi wanda suke hade da Cardiac monito din da ke gefen gadonsa.

Fitowa daga asibiti suka yi saboda hana su shiga dakin da aka yi, Jamal ne ya maida su Anty Hafsat, Basma da Nadia gida. Alh Muaz kuwa zama yayi a asibitin.

Jasmine ce ta kwankwasa kofar office din Dr Stephen.

"Come in," taji ance.

Juyawa tayi ta kalli Alamin sannan ta sa hannu ta bude kofar office din suka shiga. A zaune suka tarar da shi yana duba wasu takardu yana ganinsu Dr Stephen yayi murmushi ya mike tsaye “You were distracted earlier I couldn’t speak with you,” hannu ya mikawa Alamin suka gaisa sannan ya koma ya zauna suma suka zauna akan kujerarun da ke gaban tebirinsa.

“Yeah, that’s why we are here,”

Shiru Dr Stephen ya dan yi ya mika hannusa ya dauko wani file ya bude sannan ya fara cewa “He is stable but he is still uncouncious, he had a myocardial infraction again for the second time in a year, he was getting better with the therapy but then this, how did it happen?” Juyowa Dr Stephen yayi ya kalli Jasmine yace “You know how serious this is,”

Girgiza kai Jasmine tayi “Yeah, but don’t you think it has something to do with AFP and Rocuronium that was misused on him, because he has no history of Hypertension before he had AFP,”

Shiru Dr Stephen ya danyi yana nazarin maganar Jasmine kafin yace “It can could be possible they are related, because diplegia can affect other bodily functions like breathing and heart rate." Shiru Dr Stephen ya dan yi sannan ya cigaba da cewa "We are going to run some tests and Dr Morris will check on him too, he is a Cardiologist,”

Hannu Alamin ya sa ya shafo gashin kansa, a hankali yace “Can you stop with the medical terms and tell me exactly what is wrong with him,”

Jasmine ce ta juya ta kalleshi tace “Heart Attack ne again, and muna tunanin it have something to do with magunguna da Allurar da Dr Abdul yayi masa tunda bashi da hawan jinni kafin yayi Paralysis,”

Gyra zamansa Alamin yayi “What are we going to do?”

“He is on medication and we are going to run some test, I hope he will get better. But we will try everything we can to see that he doesn’t have any attacks again,”

Godiya suka yiwa likitan suka tashi suka fita daga office din. Suna fitowa Alamin yace mata “Muje na maida ki gida,”

“Aa, zan zauna a nan tare da kai,”

Girgiza kai Alamin yayi “Jasmine, you need to go and rest, gobe da safe sai ki zo,”

“Aa, ni gaskiya bazan tafi na bar ka ba,”

Rintse idanunsa yayi yana mamakin irin taurin kai na Jasmine, kallo daya zaka yi mata kasan a gajiye taje amma taki ya yadda taje ta huta, “Fine, idan ni na barki su ai baza su barki ba, kinsan mutum daya ake bari,”

Murmushi Jasmine tayi “Zasu bar ni, I know a few people here,”

Murmushi Alamin yayi yace “Okay, you can stay “ Hannunta ya riko yana kallon cikin idanunta yace “Thank you,”  

A zaune suka tarar da Alh Muaz akan doguwar kujerar da ke cikin dakin “Me likitan yace?”

“Kawu, Heart Attack ne amma yanzu he is stable sannan za su yi masa wasu yan gwajegwaje domin suga me ya kawo hakan,” Alamin ya bashi amsa.

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now