🌷Shafi na 9🌷

2.8K 212 9
                                    

Alamin bai sauke Jasmine a koh ina bah sai a bangaren sa. Ya na shiga falonsa ya zaunar da ita akan kujerar falon. Tafiya yayi ya dauko mata ruwa a fridge tare da kofi ya zuba mata a kofin ya mika mata sannan ya ajiye bottle a kan dan karamin table din da ke kusa da ita ko zata kara ruwan. Samu waje yayi nesa da ita ya zauna, shiru yayi yana kallonta tana shan ruwan har ta gama  ba wanda yace wa kowa uffan a tsakaninsu.

Sunkuyar da kanta tayi ba tare da tace komai ba amma a cikin zuciyarta babu irin tambayoyin da bata yiwa kanta ba domin sam bata fuskanci abinda yake faruwa ba. Ko dai Nadia ta gano abunda ke faruwa wato gayawa Jamal da tayi Nadia na dauke da juna biyu, duk yadda aka yi ma maganar ce ta fito shiyasa suka yi mata haka.

Anty Hafsat ce tayi sallama sannan ta bude kofar falon ta shigo, kai tsaye taje kusa da Jasmine ta zauna.

A hankali ta kamo hannunta  tace "Jasmine Kanwata, Dan Allah kiyi hakuri abinda su Nadia suka yi miki kinji. Nasan sai ta yi nadamar abinda ta aikata, fushi ne kawai ya ɗebe ta kasa amfani da hankalinta har hakan ta faru."

Murmushi takaici Jasmine tayi sannan ta ce "Ni fa ba da niyar cutar da ita nayi hakan ba ko dan na bata mata rai ko suna, I just wanted to help her and...." Kafin Jasmine ta karashe maganar Alamin yayi saurin tsayar da ita, cikin harshen Spanish yace mata "Ellos no saben sobre eso, No les dije.” (Ba sun san wannan zancen ba fa, ban fada masu bah)

Cikin Mamaki Jasmine ta dago ta kalle shi sannan tace "Then why did they act all rabid on me, Meyasa suka fara duka na?"

Anty Hafsat ce ta dan yi karamin murmushi sannan tace "Yarinta kenan, Jasmine, Saurayinta fa kika aura ranar da za'a daura masu aure aka daura da ke ba dole tayi kishi ba, duk da dai abinda tayi bata kyauta ba,"

Jasmine shiru kawai tayi tana kallon Anty Hafsat don itah sam bata gane me take nufi ba da an daura da ita, kamar yaya? gani take kamar wasa Anty Hafsat ke mata amma sai taga ba alamar wasa a tare da Anty Hafsat.

A hankali Jasmine ta zare hannunta daga na Anty Hafsat domin kuwa ta fahimci ba wasa take mata ba, juyawa ta yi a hankali ta kalli Alamin tare da yin wata yar karamar dariyar takaici ta gyra gashin da ya zubo mata a fuska, ta maida shi bayan kunnenta tace "A tunanina, a yanzu na gama iya hausa but sadly I am wrong ,because ni ban fahimci abinda ta fada ba."

Alamin shiru yayi tamkar bai ji ta ba kuma ba tare da ya nuna wata alama a fuskarsa ba ya juya ya kalli Anty Hafsat tare da yi mata alama da ido na ta basu waje.

Tashi Anty Hafsat tayi zata fita karaf taci karo da Jamal wanda ke tsaye a bakin kofar, dan kuwa ya dade awajen, karasowa ciki ne kawai bai yi saboda shi kansa bai san ta yadda zai yi wa Jasmine bayyani ba. Anty Hafsat da Jasmine ce kawai basu san yana wajen ba, amma Alamin ya sani.

Ganin Jamal ya shigo yasa Jasmine mikewa da sauri tayi wajensa ta rungume sa tare da sakin wasu zafafafan hawaye suka zubo akan kumatunta, dan ja da baya  tayi sannan ta dago fuskarta tana kallonsa tace "Is it true?"

Shirun da taga yayi mata ne yasa Jasmine ta dan tsorata da sauri ta ja da baya ta matsa daga kusa da shi, kamar wacce zata kone idan ta taba shi, kara tambayar sa tayi "is it true? Jamal, Abunda suke fada gaskiya ne?" Kallon da yayi mata ne ya tabbatar mata da gaskiya Anty Hafsat ta fada, ja da baya ta fara yi har sai da bayanta ya daki bangon falon, ita abun ma mamaki yake bata tamkar a mafarki ko cikin littafi daga taimako. Ita sam bata yi zaton za'a fasa auran ba domin tasa a chan UK inda ta baro ana daura aure da ciki wani zubin ma da yara a tsakani kafin a yi auren, sannan a nata tunaninta ba'a  aurar da mutum batare da yardarsa ba amma sai ta tuna yanzu fa a Nigeria take ba a United Kingdom ba, komai na nan yasha bambam da na chan.
Jamal ne ya fara matsowa kusa da ita a hankali, amma tayi saurin daga masa hannun tace "Karka kuskura ka karaso kusa da ni."

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now