🌷Shafi na 15🌷

2.8K 225 7
                                    

Jasmine da kyar ta tashi tayi sallar asuba domin ji tayi duk jikinta na mata ciwo saboda dan aikin da tayi jiya, tana idar da sallar ta koma bacci, ba ita ta tashi daga baccin ba har sai karfe 9:10am na safe, tana tashi ta tarar da tarin missed calls a wayarta, tana dubawa taga Basma da Khadija ce su ka kira ta, cikin hanzari ta kira Basma tayi ta ringing har ta katse bata dauka ba, sake kiranta tayi har sau uku amma sam bata dauka ba, sai layin Safna ta kira taci sa'a tana kira Safnan ta amsa. Safna ta faɗa mata sun shirya tun dazu, ita kadai suke jira gashi basu san inda take ba bare su zo su dauke ta, fada masu tayi cewa tana gidan Alamin na Abuja, amma kaf cikinsu babu wanda ya san inda gidan  yake sai kasa ta sauka tasa aka kwatantawa driver da zai kawo su inda gidan yake.

Tana gama wayar tayi sauri ta koma sama da gudu ta shiga bathroom tayi wanka dan su Basma sun taho, tana fitowa tayi sauri ta dauko kayanta,  dogon wandon jeans crazy ta saka tare da farar riga vest, ta zauna tana jiran su kawo mata T shirt din kungiyar da zata saka yau domin su hallaci taron ranar yaki da ciwon cancer Mama ta duniya (Breast Cancer awareness day) da ake yi duk shekara ranar 27th October a Abuja, daman halartar wannan taron ne ya kawo su Abuja, da duk shekara su Basma na halarta, wannan shekarar kuwa gayyata ta musamman aka yi ma Jasmine tana cikin guest speakers a taron a matsayinta na likita.

Styling din gashinta Jasmine tayi in curls ta sake shi ya sauko har kugunta sannan ta dauka yar karamar jakarta ta zuba abubuwan da zata bukata sannan ta saka sneakers dinta. Jasmine saukowa kasa tayi tana gyra Iwatch din da ke hannunta, ganin rana ta kwalle yasa ta bude jakarta ta dauko sunscreen dinta ta kara shafawa sannan ta saka bakin glasses da p-cap. Ma'aikatan gidan ta fara tambaya inda Alamin yake bayan ta gama shiryawa amma babu wanda yasan inda yake a cikinsu, hakan ta hakura da neman sa ta fito farfajiyar gidan domin tambayar Ma'aikatan waje koh ya fita, tana fitowa taga bakar Range Rovers ta shigo cikin gidan, Khadija ta fara bude motar ta fito sannan su Basma suka biyo bayanta.

Cike da fara'a Jasmine ta karasa inda suke tana zuwa kuwa Basma ta rungume ta "Wallahi nayi missing dinki Jas."

Dariya Jasmine tayi "Kai Basma, jiyan jiyan nan fa muka rabu."

"Toh ba'a missing din mutum na kwana daya ne, naga ana fara missing din mutum mah in less than an hour," Basma ta mayar mata tana dariya.

Murmushi Jasmine tayi "Indan na koma London wallah zan yi missing dinku, mu shiga." Jasmine ta ja su cikin gidan suka zauna a livingroom bayan sun bata rigarta taje ta chanjo cikin hanzari domin ba dadewa zasuyi ba saboda har an fara taron ma, lema kawai Jasmine ta dauko suka fita.

Kallon da Khadijah ke wa Jasmine ne yasa ta tambayeta "Lafiya Khadijah?"

"Amma Sis zaki saka hijab koh?" Khadijah ta tambayeta.

"Hijab? Meyasa?" Jasmine ta mayar mata da tambaya.

Safna ce tayi murmushi tace "Tab, kinsan halin Yaya Alamin kuwa, Allah dai yasa kar ya ganki a haka, dan muma bah tsira zamu yi ba a haka balle ke da kike wifey dinsa."

"Amma ai wannan casual dressing ne, it's just jeans and a shirt and zamuyi tafiyar kafa." Jasmine ta fada tana kallon kayan jikinta.

Suna zuwa kuwa basu dade ba aka kirawo Jasmine tayi nata bayanan, Dr Jasmine Mahmoud Alejandro, mutane da dama sun ganeta musamman lokacin da aka kira cikakken sunanta har da na mahaifinta duk da bata amfani da sunansa ita family name dinsu Alejandro take amfani da shi. Mr Mahmoud Alejandro yayi tashen Arziki sosai a duniya lokacin yana da rai domin sai da ya rike matakin mai arziki na daya Uk kafin rasuwar sa, sannan auren Jasmine da Alamin yayi tashe a Nigeria saboda yadda videos da hotunan bikin suka ringa yawo a social media, news papers da magazines. Kowa albarkacin bakinsa yake fada akanta awajen domin wasu cewa ma suke christian ce ita saboda yanayin shigarta tunda tana da aure, wasu ko kyawunta suke yabawa, wasu kuma burgesu take a ganinsu irin shigarta wayewa ce duk da tana da aure kuma musulma ce ita.

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now