🌷Shafi na 42🌷

948 101 21
                                    

Cambridge, England

Tunda Jasmine ta sauko daga kafar jirgi take ji wani iri a jikinta kamar wani abu ne zai faru amma ta rasa me nene. Juyawa tayi ta kalli baby Ayeesh da ke dauke a hannun Rahma, murmushi ne ya ziyarci fuskarta dan cikin sati biyu nan da tayi da ita jinta take tamkar yar da ta haifa a cikinta.
Satin biyu Jasmine tayi tana jiran dawowar Alamin gida, amma tunda ta baro shi a office dinsa bata sake sa shi a idanunta ba, baya kasar ma kwatakwata bare taje inda yake, Visar su  Ayesha da Nanny ta na fito ta tattara kayanta baro Nigeria dan ba zata iya cigaba da zaman jiransa ba, ba waya bare sako.

Suna tafiya a cikin Airport din ta fara jin hayaniyar wajen ta fara karuwa, gani tayi gaba daya hankalin mutanen ya karkata zuwa wani bangare na Airport din, tana juyawa taga mutane suna bawa wasu mutane hanya, karkata kanta ta tayi taga waye dan tasan bazai wuce wani celebrity din ne ba ganin yadda mutane suke ta daukar hotunansa yana tafiya .

Zaro idanu Jasmine tayi ganin mutum da ke tsakiyar bodyguards din ba kowa bane face Matthews. Me yake yi a Airport din nan?  Tambayar da tayiwa kanta kenan.

Tana gani ya tunkaro inda take tayi sauri ta juya dan bata son ya ganta "Wuce muje, da sauri," ta faɗawa Rahma cikin hanzari.

"I am sorry," murya Matthews ce ta tsayar da ita. Idanunta ta rintse dan tasan yau ta kade daga ita har ganyenta. Dan duk soyayyar da suke ita da Matthews a siri suke yinta, basu taba bari paparazzi ko wasu an jaridar sun gano abunda ke tsakaninsu gudu surutun jama'a, soyayyar su iya makusanta su ne kawai suka sani, dan ko kaɗan Jasmine bata da sha'awar ganin hotunanta kullum a jaridu da blogs kawai dan tana soyayya da wani. Tana gudun kar abinda ya sameta lokacin tana tare da Karl Rodriguez ya sake faruwa, yan jarida suyi ta binta duk inda ta shiga ya zamo babu wani sirri a rayuwata.

Hannuta ta damke sosai tana addua kar Matthew ya aikata wani abun dan rabuwar da suka yi ta karshe ba a cikin jin dadi bace. "I Love You Jasmine," taji ya faɗa da karfi.

A hankali ta juya ta ganshi tsaye a bayanta, gabaki daya mutane da ma ma'aikatan Airport din kowa tsayawa yayi yana kallon su, masu recording nayi, masu kunnawa live a social media dinsu ma na yi.

"I am so sorry I misunderstood you," Matthew ya faɗa tare da takowa kusa da ita.

Jasmine ji take kamar ta nitse a kasa "What are you talking about Matt, stop this nonsense right now. You're making a scene," Ta faɗa a hankali tana kallonsa da bata son ya cigaba da wannan surutan banza, idan Alamin ya gani tasan shikenan kuma musamman yanzu da yake fushi da ita.

Murmushi Matthews yayi ya kamo hannuta yace "It's not nonsense darling, I know you did what you did to help a friend in need and I forgive you,"

Bude baki Jasmine tayi ta rufe dan ji tayi gabaki daya bakinta ya bushe, wato yasan aurenta da Alamin ba na gaske bane. Kara matsowa kusa da ita Matthews yayi yana kallon cikin idanunta yace "I am sorry," a hankali dan ita kadai ta ji kafin ya fara magana da karfi kowa yana jinsu "Jasmine, You're my best friend for over 13 years, The Love of my life for over 4 years, I have known you for half of my life which felt my whole life, you're everything I ever wanted and need," A hankali ya duka da kafa daya a gabanta yasa hannu a aljihu ya ciro wannan dan karamin akwatin zoben da ya so yayi mata proposing da shi ya bude zoben yana kalli ya rike a gaban ta "Jasmine the love of my life and my everything, will you grant me the honor of being your life partner, Husband and best-friend forever."

Jasmine ji tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi a jikinta, gaba ki daya gabobin jikinta kasa motsi suka yi, da kyar ta iya daga kanta ta kalli dinbin mutanen da suka zagaye su kowa ya daga waya yana recoding din su, duk jiran amsarta suke. Da ace shekarun baya da suka wuce ne koma watanni 8 da suka shige da ta amshi zobensa cike da farin ciki saboda a lokacin babu kowa a zuciyarta sai shi amma yanzu komai ya chanja.

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now