🌷Shafi na 34 🌷

1.3K 127 33
                                    

Kamshin girki da Jasmine taji ne yasa tayi hanyar kitchen dinsu. Tana shiga ta tarar da Alamin a gaban gas cooker yana zuba kwai acikin frying pan. Murmushi tayi ta karasa inda yake sannan tace "Good morning,"

"Morning Love," Amsa Alamin ya bata bah tare da ya juyo ba.
"Girki kake yi?"

Fuskarsa dauke da murmushi ya juyo ya jingina a jikin counter kitchen din sannan yace mata "Yeah, I wanted to suprise my wife with breakfast,"

Girgiza kai Jasmine tayi tana murmushi tace "That's so nice of you, lallai kana ji da matar nan taka. Me kake dafa mata?"

"Pancake, toasted bread and omelettes, daga wannan na gama." Ya bata amsa yana juya wainar.

Setting din dinning table Jasmine ta taya Alamin sannan taje ta hada fruit juice din zata sha. Suna fara cin breakfast din Alamin ya tambayeta "Do you like it?"

Murmushi tayi tace "I love it, yayi dadi sosai and you have finally convinced me ka iya girki,"

Dariya Alamin yayi yace "Da ma baki yarda da kwarewata?"

"Ina? ba haka nake nufi ba, kawai dai ka kara tabbatar da kwarewar taka ne." Jasmine ida maganarta tare da kurbar ruwan lemonta sannan ta kara cewa "Yau zan koma Hospital wajen su Khadija, I was thinking about girka masu abincin rana na kai masu tunda na san an riga da an kai masu abinci safe,"

Girgiza kai Alamin yayi yace "Hakan yayi, karfe nawa zaki tafi sai muje tare, kinga daman yau Doctor yace za'a sallami Khadija,"

"Okay, daman ita bata ji ciwo ba sosai. wajen karfe sha biyu 12:00 haka zanje na kai masu da wuri,"

"Okay, Yaushe zakiyi girkin na taya ki ko ba kya so taimakon kwareren mai girki," Alamin ya tambayeta cikin zolaya.

Daga gira daya Jasmine tayi tana kallonsa, cikin tsokana itama tace "Wato dan Allah ya taimake ka kayi pancake ba tare da ya kone ba shine ka zama kwareren Chef?"

"Wato dai kin janye maganarki ta dazu,"

Dariya tayi tace "Something like that," ajiye fork din hannuta tayi ta cigaba da cewa "And Ina tunanin chan bangaren zanyi girki saboda da dan yawa zanyi, zan kaiwa sauran patients  din ma."

"Hakan yayi kyau," kawai Alamin yace sannan ya cigaba da cin abincinsa bai kara cewa komai ba.

Dago idanunta Jasmine ta kalleshi ya cin abinci tace "Yau baza ka wajen aiki bane?"

"Kin gaji da ganina ne?" Ya tambayeta tare da saka idanunsa acikin nata.

Kasa Jasmine tayi da kwayar idanunta tace "Aa, I'm just asking naga da safe kake fita,"

"Well, yau babu inda zani I want to spend the day with my lovely Wife,"
Murmushi tayi ta ajiye glass cup din da ke hannunta sannan ta mike tare da daukar plate dinta sannan tace "Kash, sai dai lovely Wife din taka tana da aikin yi yau,"

"Ina zaki," Alamin ya mike tsaye shima yana kallonta.

"Ka manta aiki girki zanje na fara,"
"Tun yanzu? Bai yi safiya ba," Alamin ya tambayeta yana hade girarsa.

"Aa, karfe 9:30 fa," Ta bashi amsa tana duba Iwatch din da yake hannunta.
Alamin bai samu damar taya Jasmine aikin girkin ba saboda a bangaren su Hajiya Kaka taje yin aikin sannan ba ita kadai tayi aikin ba ma'aikatan Kitchen din na tayata yin girkin. Haka yayi ta zama shi kaɗai yana jiranta.
Daman ya ki fita aiki ne da niyar ya zauna a gida su wuni tare, abunda ya dade bai yi ba tunda ya fara gina kamfaninsa kusan shekara tara 9 kenan. Gashi  Allah ya daukaka masa kamfanin yanzu, shi kansa yana son hutu sai dai bashi da damar hutawa saboda yawan ayuka, mussamman da ya fara kula da kasuwancin mahaifinsa ayukan sun kara yi masa yawa, bayan ya hade business dinsa da na mahaifinsa sun koma daya ayyukan sun ragu ta wani fanin sannan sun karu ta wani fanin. Meetings guda uku ya soke saboda ya zauna a gida tare da Jasmine duk da ba ranar karshen mako bace. Alamin ji yake akan Jasmine babu abunda ba zai iya rabuwa da shi ba da tsaf zai iya bada duk abunda ya mallaka muddin Jasmine zata zauna tare da shi.

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now