🌷Shafi na 39🌷

1K 109 30
                                    

     A falon sama su Alamin suka zauna suna jiran Antinsa da suka zo wajenta, ruwa, lemuka da snacks  aka kawo masu kafin ta fito. Wata kyakyawar budurwa ce ta zo ta gaishe da su ta zauna suka fara hira, Jasmine kuma na yiwa yan biyu wasa. Ruwa Jasmine ta deba acikin glass cup ta kurba tana murmushi saboda abinda budurwar ta faɗa.

"Wato dai sai yau ka ga damar kawo min Amaryar taka na gani ko, ina yar tawa take," Muryar da Jasmine ta ji ce tasa ta juyar da kanta inda sauti ke tahowa.

"Lalala yau ɗana na ya tuna da  Mummy sa,"

Dariya Alamin yayi yace "Haba Mummy, Wallahi aiki ne kemin yawa shiyasa bana zuwa, kuma ai ba kya kasar,"

"Hakane, amma ai kwaki ka je kasar da ne amma ba nemeni ba, wata nawa yanzu amma sai yau ka ga damar kawo min Amaryar taka na gani ko, ina yar tawa take," Muryar da Jasmine ta ji ce tasa ta juyar da kanta inda sauti ke tahowa.

Murmushi Alamin yayi yace "Toh ayi min affuwa Mummy,"

Dariya Anty Kaulat tayi tace "Hakane, amma ka wanke kanka tunda ka kawo min diyata,"

Juyawa Jasmine tayi domin ta gaishe da Anty kaulat amma sai ta kame chak  tamkar wacce aka sakawa pause saboda Anty Kaulat  da ta gani a gabanta, a hankali ta mike tsaye tana kallonta itama matar tana kallonta, glass cup din da ke hannunta ne ya zame ya faɗi tas a kasa saboda dauke wuta da kwakwalwar ta tayi a lokacin. Mamanta Mahaifiyarta ce a gabanta, wasu zafafan hawaye ne ke zuba a idanunta lokacin da ta tunkari matar tana tafiya a hankali tamkar wacce aka zarewa laka. Rufe idanunta tayi ta sake bude su domin ta tabbatar ba mafarki take yi ba.

Mikewa Alamin yayi, yayiwa kanwar Jasmine alama itama ta tashi suka sauka kasa tare da yan biyu suka bar Jasmine da mahaifiyarta a tsaye suna kallon juna. Wasu zafafan hawaye ne ke zuba a idanun Jasmine har ta karasa gaban mahaifiyarta bata iya cewa komai ba sai hawayen. Anty Kaulat daga hannu tayi ta taɓa fuskar Jasmine a hankali tace "Bethlehem,"
Girgiza kai kawai Jasmine take yi da kyar ta iya cewa "Mami,"

Hawaye ne suka fara zubowa a idanun Anty Kaulat lokacin da Jasmine ta daga hannu ta taɓa fuskarta dan ta tabbatar da gaske mahaifiyarta take gani, a hankali ta kara cewa "Mami,"

Da sauri Anty Kaulat ta janyo Jasmine ta rungumeta tana kuka itama Jasmine na kuka. Sun fi minti uku a haka kafin Jasmine ta zare jikinta a hankali tana kallon mahaifiyarta. Wani dogo saurayi da bai wuce shekaru goma sha takwas bane ya shigo falon, tsayawa yayi yana kallon su Jasmine kafin yace "Mummy lafiya? wace wannan?"

Shiru Anty Kaulat tayi sannan tace "Kai baka iya gaisuwa ba, to matar Yayanku Alamin ce, jeka ka bamu wuri," da sauri Jasmine ta daga kai ta kalleta idanun cike da mamakin kin fadar gaskiyar da Mahaifiyarta tayi, a hankali Jasmine ta zame daga jikin mahaifiyarta tana kuka ta tsaya tana kallonta, lafiyarta kalau sannan da alamu babu wata matsala da ke damunta, to meyasa bata nemeta ba? Tambayar da ta yiwa kanta kenan. A hankali ta tace "Why?"

Shiru Anty Kaulat tayi kafin ta mayarwa Jasmine da tambaya "Which one?" Ta faɗa a hankali itama hawayen yana kwaranyo daga idanunta.

"Everything," Jasmine ta bata amsa murya a sanyaye "Why did you abandon me and Papi? Meyasa baki taɓa nemana ba? Ko a waya? Ko ba kya sona ne? Meyasa kika bar ni Mami?"

Lumshe idanunta Anty Kaulat tayi sannan ta bude su a hankali tare da share hawayen da ke kan fuskarta, "Bethlehem," a hankali ta furta sunan Jasmine sannan ta tace "I made a mistake and covered it with another mistake, I cannot undo what I did,"
Ita kanta Jasmine bata san tana matsawa baya ba dan ji tayi gabaki daya kamar ba ita ke sarrafa jikinta bah. Abunda Jasmine tafi tsoro shine ya faru wato mahaifiyarta ta san inda take amma bata nemeta ba, wato bata son ganinta kenan ko kuma bata damu da ita ba kwatakwata. Ƙasa tayi da kwayar idanunta tace "Am I the mistake?" 

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now