🌷Shafi na 11🌷

3.1K 218 16
                                    

      Jasmine tafiya take a hankali tana taku tamkar sarauniyar tare da Basma a gefenta har suka fito daga bangaren Alamin. Tsayawa suka yi a bakin kofar da suka hango Alamin da Jamal sun nufo su, Alamin yasha manyan fararen kaya babbar riga da hularsa, shima ba karamin kyau yayi ba yana tafe masu daukar hoto suna biye da su a baya. Idanunsa na kan Jasmine domin ba karamin kyau tayi ba, dan kasa dauke idadunsa daga kanta yayi har ya isa idan take.

Hannunsa ya mika mata ta saka nata a cikin nasa tana murmushi ta matso kusa da shi Jama'a ko sai video ake masu masu daukar hoto ma suna tayin na, su ko babu abunda suke sai murmushi tamkar wayanda suka yi auren soyayya.

Cikin gida suka koma inda Jama'a ke ta zuwa suna hotuna da su, yan datijai da ƙawayen Hajiya Kaka  sai tsokanar Alamin suke bare ma abokan wasansa (cousins), shiko bai ce masu komai sai murmushi kawai da yake yi.

Daga cikin gidan Mota su suka shiga wacce zata kaisu gurin reception din, suna shiga cikin motar komai ya chanja tunda driver ya fara jan su gabaki dayansu hade rai suka yi suka koma tamkar basu san juna ba, Jasmine kuwa matsawa tayi chan gefe tana daddanna wayar ta, shiru suka yi a cikin motar ba wanda ya kula kowa har suka iso wajen reception din.

Kofa aka fara budewa ta bangaren Jasmine, har zata fita Alamin ya rike mata hannu sannan yace "ki tsaya."
Komawa ko tayi ta zauna saida aka bude masa tasa kofar  yah fito sannan ya zagayo bangarenta ya mika mata hannun ta karba ta fito.

Hotuna ko har Jasmine ta gaji da shi saboda duk takun da sukayi photographers na biye su suna dauka, ita kawai adduar da take yi a zuciyarta ita ce Allah yasa kar Matthews yaga hotunan saboda ita sam bata ma san tayaya zata fara yi masa bayani ba.

Wajen Reception din yayi matukar haduwa ado aka yiwa wajen na ban mamaki da flowers da candles, idan ka shiga ciki baza ka taba gane cewa da rana ake party ba domin kuwa wajen mayar dashi aka yi tamkar dare, kallo daya zaka yi wa wajen kasan lallai kudi yayi aiki a wajen kuma bikin na masu hannu da shuni ne.


Saida suka shiga cikin hall din suka je wajen zamansu sannan Alamin ya saki hannun Jasmine ta zauna, bayan ta zauna ya ɗan gyra mata rigarta da take jan kasa, Sannan shima ya zauna kusa da ita.

Events din aka fara, Mc ya fara gabatar da taron, inda aka fara kiran masu nishandantar da mutane da aka gayyata comedians Bovi, Basket mouth da Bushkiddo, bovi ne ya fara gabatar da nasan wasan sannan bushkiddo inda suma suka rika tsokanar Alamin da yaba kyawun Jasmine. Alamin murmushi kawai yake yi, itako Jasmine dariya ta rika yi inda aka faɗi abun dariya kuma ta gane me suka faɗan wani kuma bata ganewa saboda hausar tata ba kwari ne da ita sosai ba sai dai kawai tayi murmushi.

Ana ta gudanar da events, yan rawa ne suka fara gudanar da nasu wasan, mutane sai liki suke musu. Jasmine ji tayi wuyanta ya bushe tana jin ishirwa sosai domin rabon ta da ruwa tun safe lokacin da suka baro gida, ɓata rai ta ɗan yi ta rasa yadda zata yi, gashi tana gani ana ta serving din Jama'a da drinks su kuma table dinsu babu komai sai flowers akai, ba abun tayi magana ba saboda batason tayi wani abun da ba daidai ba tunda bata taba attending din wani bikin hausawa ba balle ta san yadda suke yin abubuwa, dan taga al'adun bikinsu da na nan ba iri ɗaya bane.

Alamin ko yana kallonta yaga yadda tayi da bakinta ya fuskanci ishirwar take ji, alama yayiwa wani waiter da hannunsa, waiter ya kawo masu drinks kan table dinsu da yake cike da flowers. Bayan waiter ya ajiye ne Alamin ya dauki glass-cup guda daya ya zuba ruwan aciki, ya daga ya kaiwa Jasmine bakinta,  mamaki ne ya hanata sha. Tayaya ya gane tana jin ishirwa, tsayawa tayi tana kallonsa sai da ya dan yi mata murmushi sannan ya kalli wajen da  jama'a suke da idonsa sannan ta gane itama tayi murmushi ta sha, Handkerchief ya dauko goge mata gefen bakinta ta jambakinta ya dan shafa da tana shan ruwan sannan ya kara daga mata tasha.

Jama'a ko sai burge su suke keyi saboda irin yadda suke nuna soyyayarsu ga juna a fili. Hotuna ko an musu sufi dubu haka bidiyo ma sai yi masu ake....

*******

Nadia ko har su Alamin suka tafi wajen Reception din bata daina kuka ba, Hajiya Saudat ko har ta gaji da bata baki, shiru kawai tayi mata tana kallonta domin ita ma takaici duk ya isheta.

Ƙawayen Nadia ko sai tsinewa Jasmine suke suna jin haushin bata masu shiri da tayi, sun ci burin bikin Nadia sosai amma gashi ana bikin amma babu damar suje duk kashe kuɗin da suka yi da tsara bikin da su ka yi, sai dai su zauna kamar wayanda aka yiwa rasuwa suna jimamami.

******

Mc kiran Jasmine da Alamin yayi suka fito waje sannan yace kowanne acikin su yayi wa dan uwansa wani alkawarin da bazai taba karyawa ba, ta kan Jasmine aka fara inda ta fara dariya domin ita bata ma san me zata faɗa ba, a hankali ta karbi mic din tana murmushi cikin harshen Spanish tace "Prometo nunca lastimarte y siempre te haré feliz para siempre." Dariya Mc ya fara sannan yace "Amarya munki wayon nan fa dole ki fassara mana abunda kika cewa Angon naki domin muma muji."
Murmushi Jasmine tayi sannan tace " Nayi alkawari banza cutar da kai ba, zan kasance mai saka ka cikin farin ciki na har abada." Tafi zama'a suka fara yi ana dariya, sannan Jasmine ta mikawa Alamin mic din, ya karba ya dan yi shiru, idanunsa ya daga ya sasu a cikin na Jasmine sannan ya fara magana "Nayi alkawarin zan kasance mai saka ki farin ciki, bazan taba bari ki kuka da ni ba, zan kasance tare da ke har abada, In sha'a Allah," Yana gamawa ya zura hunnunsa cikin aljihunsa ya dauko wani hadaddan diamond ring yana kyali ya kamo hannun Jasmine ya zura mata.

Zoben Jasmine ta ƙalla ta kalle shi ji tayi karamar kalaman nasa da gaske yake yi ba wasa ba, saboda yadda yayi maganar da irin kallon da ya ke mata babu wasa ko kadan a ciki.  Lumshe idanunta tayi ta bude su a hankali tana kokarin kwantar wa da kanta hankali, murmushi tayi masa tace "Thank you," daga hannun nata yayi ya sumbata fuskarsa dauke da murmushi shima.

Tafi aka fara yi masu sosai saboda abun ba karamin burge su yayi ba, Mc ne yasa aka kara yi shiru sannan yace a sakawa a Amarya da Ango waka domin su zasu fara bude filin rawar.

Cool music aka saka musu inda suka dan taka dan Alamin bai iya rawa ba kasa yi yayi haka suka koma suka zauna. Mawakan da aka gayyata ne suka  fara fitowa suna nuna tasu bajintar, Buzu ne ya fara fitowa yana tasa wakar. Safna, Khadija, Basma da kawayensu ne suka fito filin rawar sai tikar rawa suke yi domin sune suka zama ƙawayen Amaryar.

Daga baya su Classiq, Olamide da lil kesh suma suka nuna tasu banjintar, sai da suka saka Jasmine ma ta dan yi rawa.

Ba'a tashi daga taron ba sai da da kiran sallar magrib inda aka bada damar yin hotuna da Amarya da Angon daga nan kuma aka tashi daga wajen Reception din.

A hanyar dawowarsu ma babu wanda ya kula kowa kamar yadda suka zo, kamar basu neh a suka ringa nunawa juna kulawa ba acikin Reception din.

Bayan sun isa gida ma shi ya fara fitowa daga motar sannan ya riko hannunta ta fito, sakin hannunta yayi har ta juya zata tafi  ya ce mata " Take care."

Girgiza kai kawai tayi ta bar wajen dan ta gane me yake nufi, saboda itama tasan Nadia na jiranta domin tabbasa tasan bata huce ba.




Late update, tuba nake wlh abubuwa ke min yawa I hardly find time to write, amma ga wannan bah yawa 🖤🖤.

Kar ku manta Inason jin ra'ayoyin ku game da wannan shafi.

Karku manta da dan Star ⭐️ dinnan da ke kasa ku dana minshi yayi haske 😁.

Xoxo 💋
Instagram @amiratuoo
Twitter @AminaUmzak
Facebook Amina Umzak
🖤🖤🖤🖤🖤🖤

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now