🌷Shafi na 20🌷

3.6K 199 21
                                    


Wata daya kenan da tafiyar Alamin kasar Germany tare da Mahaifinsa domin nema masa lafiya, sau uku kadai suka yi waya da Jasmine, wayar da bata fin ta minti uku ba, dan ko lafiyar Alh Yunus zata tambaya sai dai ta kira Dr Stephen. Kamar yadda Dr Stephen ya faɗa mata  jikin Alh Yunus yayi sauki sosai domin kuwa har ya fara magana da zama da kansa, tashi da tafiya ne dai sai an rike shi.

Jasmine tana ta kokarin neman mahaifiyarta sai dai har yanzu bata gano wani abu ba hatta mutum da ta dauka aikin binciken babu abunda ya gano face wacce take tunanin ita ce mahaifiyarta ta Dr Halima matar tsohon gwamnan Kano, ba ita bace ba dan har gidanta taje. Duk da kuwa  tsohuwar first lady na matukar kama da mahaifiyarta sai dai Jasmine na zargin  ko dai Dr Haliman na da alaka da mahaifiyarta saboda kamanin sun ɓaci. 

Duk da Jasmine bata tare da Matthews tafiyar Alamin ta kara jawo su kusa domin kuwa kullum sai sunyi waya babu abinda Matthews bai sani ba game da zamanta a Nigeria. Abu daya ne har yanzu ta kasa sanar da shi shine aurenta da Alamin. Duk da tasan auren ba na gaske bane amma gani take kamar cin amanar Alamin take idan suna waya da Matthews sam bata iya sakewa kamar da shi kamar da.

Hajiya Saudat kuwa gabaki daya  daina fitowa daga bangarenta gabaki daya duniyar tayi mata zafi, kullum cikin fargabar bayyanar abunda ta aikata take, duk da tasan babu wanda yasa abunda ta aikata daga Jasmine sai Alamin.

Jasmine na zaune a babban falon gidan tare da su Hajiya Kaka suna hira. Sai dariya suke suna fara'a, suna ta tsokanar Hajiya Kaka. Sallamar da suka ji ce ta katse masu hira. Suna amsawa Muktar daya daga cikin ma'aikatan gidan ya shigo da akwatin guda biyu a hannunsa. Khadija ce ta yin saurin tambayar ma'aikacin "Akwatunan waye wannan?"

Amma kafin ya bata amsa Nadia ta shigo da tana tafiya da kyar cikinta ya tasa sosai. Steps din shigowa falon ta fara takawa zata shigo sai ta zame zata fadi, cikin sauri Alamin da ke biye da ita ya rikota kafin ta faɗi. Baya Nadia tayi ta fada jikinsa sannan ta ski wani makirin ihu ta makalkale Alamin kamar wacce taga wani abun tsoron.

Rike Alamin yayi ya dan matsar da ita daga jikinsa yace mata "Are you Okay?"  Shiru Nadia tayi bata bashi amsa ba sannan bata cika shi ba. Juyar kanta tayi suka hada ido da Jasmine ta sakar mata wani makirin murmushi.

Murmushin itama Jasmine ta mayar mata sannan ta kashe mata ido daya, duk da kishin da taji ya kamata. Daga mata  ɗan yatsanta na tsakiya tayi sannan ta dauke kanta. Dan ta gane zamewar karya tayi saboda tasan Alamin zai rikota zai bari ta faɗi ba, duk dan ta bata mata rai.

A hankali Alamin ya zame jikinsa daga rikon da Nadia tayi masa sannan yace mata "Muje, amma ki kula da steps dinnan kar ki kara zamewa."

Murmushi Nadia tayi masa  ta rike hannusa gagam kamar me tsoron wani abu, a hankali suka sauka daga matattakalar suka shigo cikin falon. Hajiya Kaka ce kawai tayi masu sannu da zuwa, dan Khadija da Basma kallo kawai suke binsu da shi ganin yadda Nadia ta rike hannu Alamin kamar idan ta cikashi zai bacce, kuma bai hanata ba sannan bai ce mata komai ba. A hankali suke tafiya har ya sama mata waje a falon ta zauna sannan shima ya samu waje ya zauna. Jasmine yi tayi kamar bata gansu ba duk da irin kallon da Alamin yake mata yana jira tayi masa magana.

Hajiya Kaka ce ta fara magana "Mai gidana ya naga ka dawo da ita a haka? me yasa baka fada mana zaku dawo ba, gashi ko girki ba'a yi maka ba." ta karashe maganarta tana kallon Jasmine, tana tunanin ko tasan da dawowarsa amma bata sanar da su ba.

Murmushi Alamin yayiwa Kakarsa, sannan ya juya ya kalli Jasmine yace "Ai ko kamar kin san yunwa nake ji," nufasawa yayi ganin Jasmine taki kallonsa ya cigaba da cewa "Nadia taki zama a asibitin, tunda taji zan dawo ta daga hankalinta sai ta dawo gashi har BP ta ya hau, shiyasa likitanta ya ce na taho da ita kawai, tunda kinga jikin nata yayi sauki, zai duga kira kawai idan an samu wani complications kuma a maida ita chan."

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now