🌷Shafi na 47🌷

1.6K 126 65
                                    

A tsaye Alamin ya tarar da ita rike da kofi a hannunta tana waya a lounging area da ke cikin suite dinsu, karasawa wajen yayi ya zauna akan kujera yana jiran ta gama wayar. Tana kashe wayar ta juyo tana kallon fuskarsa da ke dauke da murmushi, a hankali tace "Good morning M,"

Turbune fuska Alamin yayi yace "What is good about this morning, bayan kin bar ni ni kaɗai a ciki,"

Dariya maganar tasa ta bata ganin yadda yayi maganar kamar wani karamin yaro, "Amma what was I suppose to do, na tashi daga bacci me zanyi kuma akan gado,"

Jingina Alamin yayi a jikin kujerar da ya samu ya zaune yana murmushi "I can think of a thousand things," ya faɗa hade da kashe mata ido daya.

Girgiza kanta kawai Jasmine tayi ta dauke fuskarta dan boye murmushin da ke kokarin fitowa, a hankali ta daga kofin da ke hannuta ta kurbi hot chocolate din da ke ciki sannan tace "Yanzu dai, what do you want for breakfast?" Sannan tayi nuni da wajen cin abinci da ke suite din "Though nasa an kawo mana English breakfast,"

Mikewa Alamin yayi yana kallon kofin da ke hannuta yace "I want that?"

Kofin da ke hannunta ta daga tace "Hot Chocolate?"

A takaice ya bata amsa "Eh," sannan ya kara matsowa inda take yasa hannunsa ya janyota kusa da shi.

"Is it nice?" ya tambayeta yana kallon hot chocolate din da ke hannunta.

Girgiza kai Jasmine tayi tace "Uhmm," tana mismis ta bakinta, tana kara kurba Alamin ya haɗe bakinsa da nata, a hankali ya dago kansa yana tsotsar bakinsa kafin yace "I love it, zan kara," yana kallon bakinta.

Kallonsa kawai Jasmine ta tsaya tana yi ta kasa cewa komai, "I want more," ya kara maimaitawa. Hannu a sanyaye Jasmine ta daga kofin ta mika masa.

Girgiza kai yayi yana kallon kofin yace "Nope, you are going to feed me,"

Sakin baki tayi tare ta juya kwayar idanunta tace  "You are not serious,"

Mumushin nan na gefen baki yayi yace "Trust me love, I am," Juyawa Jasmine tayi zata bar wajen yasa hannayensa biyu ya rike ta.

Murmushi tayi tace  "Let me go M, and stop acting like a baby,"

"But I am your baby," ya bata amsa yana dariya.

Dariya Jasmine tayi amma kafin ta bashi amsa ya jata suka nufin dinning area din suite din. Kujera Alamin ya janyo ya zauna sannan ya janyo ta ta zauna akan cinyarsa, kokarin mikewa tayi ya riketa.

"Come on M, ka cika ni mana I want to sit,"

"You are sitting," ya bata amsa tare da sa hannu ya cire mata rubber band din da ke rike da gashinta.

Turo baki Jasmine tayi tace "Amma, I am not comfortable,"

"Ouch, that hurts," bata rai Alamin ya dan yi na wasa "Don't tell me kin fi son kujerar nan akai na, I am softer,  cuddly and fluffy,"

Tuntsurewa da dariya tayi tace "Fluffy sai kace wani cotton candy,"

Sautin dariyar ta ce ta sa shi murmushi a hankali ya sumabaci gefen fuskarta sannan yace "Speaking of candies reminds me, ina Ayeesh?"

Karkatowa Jasmine tayi tana kallon fuskarsa tace "Lallai, father of the year, sai yanzu ka tuno da ita."

Murmushi mai sauti ya saki yace "Father of the year, come on." 

"Eh mana, yaushe rabon da ka ganta amma ko tambayarta baka yi,"

"Shikenan, I am sorry Mama bear zan rika tambayar ta. Yanzu tana ina?"

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now