🌷Shafi na 45🌷

1K 78 18
                                    

Wani irin kayataccen murmushi  ya saki ganin kayan da ya aika mata ne a jikinta. Ba karamin kyau kayan suka yi mata ba fiye da yadda yayi tsammani, ji yake kamar ya tafi da gudu ya rungumeta dan ba karamar kewarta yake ba, mussaman yanzu da yake kallonta a kusa da shi bai fi taku goma ne a tsakaninsu ba.

Ya daga kafa kenan zai fara takawa inda take ya hango wani bature ya riga shi zuwa wajenta, murmushi ya ga tayi wa baturen shi kuma ya karbi hannunta ya sumbata sai kuma suka bige da hira, tsayawa yayi yana kallonsu yana kokwanton ya je ko kar yaje wajenta.

Abunda James ya faɗa ne ya bawa Jasmine dariya tace “Goodness I missed a lot when I was in Nigeria,”
Murmushi James yayi ya mikawa Jasmine hannu yace “May I have a dance,”

Hannunta Jasmine ta sa a cikin nasa tace “Sure,” sannan suka nufi filin rawa inda mutane ke rawa tare da patners dinsu, suma suka fara rawar a hankali.

Suna cikin rawar James yace “I need your help Jas,”

“Okay,” Daga nan James ya fara faɗawa Jasmine kudirinsa na son yayi proposing ga kawarta Charlotte dan sun dade suna soyyaya, Jasmine shawarwari ta ringa bashi suna rawar suna tsara yadda zai yi abun ya zamo bazata a wajen charlotte.

Alamin yana tsaye yana kallonsu babu abunda yake in banda mugun kallon da yake aikawa James duk kishi ya bi ya lullube shi, ji yake kamar yaje ya  fincike James daga wajen mussaman da yaga ya faɗawa Jasmine wani abu ta daga kai tana dariya cike da nishadi. Abu daya ne ya hanasa karasawa wajen baya son yayi abun kunya a wajen tunda su awajensu turawa hakan ba wani abu bane amma shi duk abun yabi ya dame shi. Hannu Alamin ya ji an dora masa a kafadarsa ya juya yaga Jamal ne yake kallonsa, “Har ka gama yaudararta ta?” Alamin ya tambaye shi tare da juyawa gaba ki daya daga inda zai dunga hango Jasmine.
Murmushi Jamal yayi yace “Ba yaudararta nake ba, we were just catching up,”

Irin Murmushin nan na gefen baki Alamin yayi yace “If you say so,”

Girgiza kai kawai Jamal yayi bai ce komai ba sai kuma ya kalli bayan Alamin ya hango kanwarsa tana rawa da saurayin Charlotte James, muryar a dan kasa Jamal yace “You know you can get her away from him rather than standing here sending him daggers with your eyes,”

Juyawa Alamin yayi ya kalli Jasmine yaga har yanzu murmushi take, sannan ya juyo ya kalli Jamal yace “How?"

Yar dariyar mugunta Jamal ya danyi sannan yayi gyran murya cikin tsokana kafin ya fara magana “Well, first zaka samo dancing partner ku fara rawa awajen idan kunzo kusa dasu sai ka nemi kuyi swapping partners. Simple”

Wani rin kallo Alamin yayiwa Jamal kafi yace “Kafi kowa sanin bana rawa da matan da ba muharramai na bane,”

“I know,” kawai Jamal yace kafin ya kara da “That’s your first and polite option, da other one is a bit rude which is ka tafi kai tsaye and ask to dance with her….” Kafin Jamal ya gama rufe bakinshi Alamin yayi gaba. Yana isa inda Jasmine da James ke rawa ya taba kafadar James yace “May I dance with the beautiful Lady please?" 

Murmushi kawai James yayi ya cika Jasmine sannan yace mata “It’s a great pleasure dancing with you,” sannan ya bar filin rawar.

Dan karamin murmushi Jasmine tayi sannan ta juya ta kalli Alamin, tafin hannunsa ya bude ya miko mata yana kallon fuskarta, dan jim kaɗan tayi kafin ta saka hannunta a cikin nasa. Kusa dashi ta matso kadan sannan ta dora hannunta akan kafadarsa. Hannunta da ke kan kafadarsa ya kalla sannan ya juyo a hankali yana kallon fuskarta, shima yasa hannunsa a bayanta dayan hannunsa kuma rike da nata. A hankali suka fara takawa suna bin sauti instruments din da ake playing a wajen, juya ta Alamin yayi ta jingina da bayansa, a hankali ta daga kanta ta kalle shi sai kuma ta dauke kanta. Kamshin turaren gashinta da ya shaka ne ya sashi lumshe idanu tare da sakin ajiyar zuciyar, a hankali ya daga hannunta ya juya ta, ta maida hannunta kan kafadarsa suka cigaba da rawar. Babu wanda yace kala a cikinsu har masu playing instruments din suka tsaya. Ganin kidan ya kare amma Alamin bai cikata ba yasa Jasmine cewa “Kidan ya tsaya fa,” juyawa tayi ta kali gefe da gefen su taga mutane sun fara barin filin rawar amma bai cikata ta ba, kawai ya tsaya yana kallonta. Bata rai tayi, sai kuma taji sabon kida ya fara tashi har wasu mutanen sun fara tunkaro filin rawar suna haduwa da wayanda suka rage a ciki.

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now