🌷Shafi na 18🌷

Începe de la început
                                    

Juyowa gabaki daya Jasmine tayi tana kallansa tare ta dora hannunta akan kirjinta tace "OMG, irin shaidar da kayi min kenan, toh shikenan bazan sake magana bah har mu kai Kano." Ta karashe maganar hade da juya mai baya tana kallon window motar.

Yar karamar dariya Alamin yayi yace "Naji, ni ko one-hour kika yi ba tare da kin yi Magana ba zanyi miki ko in baki duk abunda kike so I promise."
Juyowa Jasmine tayi da sauri ta zaro manyan idanunta tana kallonsa  tace "Komai fa kace."

Murmushi yayi yace "Eh, komai."
Dariyar mugunta tayi tace "Shikenan ga wayata bari na saka timer." Kunna timer wayarta tayi  tace "Yauwa lokacina ya fara."

Juyowa Alamin yayi ya kalleta da murmushi gefen bakin nan a fuskarsa sannan yace "To ai har yanzu bakiyi shirun ba."

Yatsunta guda biyu taja a saman bakinta alamar ta rufe bakin sannan ta juya tana kallon hanyar da suke shigewa ta window motar.

Ko minti 20 ba'a yi ba Jasmine ta gaji dayin shirun, dakko wayarta tayi da earpie zata saka a kunneta , da sauri Alamin ya karbe  yace "This is cheating, banda amfani da waya."

Bata rai Jasmine tayi har ta bude bakinta zata yi Magana sai kuma tayi shiru kawai ta kyale shi, cigaba da tafiya suka yi ba tare da Jasmine tayi magana ba har suka zo zuma rock, subutar baki tayi tace "Wow, ni ban taba zaton akwai irin wannan rocks din a garin nan ba." Tana juyawa Alamin ya daga mata wayarta takali timer da ta kunnan saura minti 10 lokacinta ya cika tayi magana, Dariya Alamin ya fara yi mata sannan yace "Wrong timing."

"Ni gaskiya ban yarda ba ehen, wannan ai ba surutu nayi ba tambaya ce." Jasmine murtuke fuska.

Cikin dariya yace mata "Tambayar ita ba magana bace kenan."

"Eh." Jasmine ta bashi amsa tare da juya masa baya.

Murmushi yayi yace "Shikenan duk da kin fadi ki zabi abu daya kawai and I will do for you."

"Da gaske kake?" Jasmine ta juyo tana murmushi.

"Yeah." Ya bata amsa a takaice, shiru tayi bata ce mai komai ba sai ya kara da "Anything on your mind, ki faɗi abunda kike so."

Murmushi mugunta Jasmine tayi  tace masa "Ba yanzu ba tunda dai kayi alkawari ka bari sai naga abunda nake son tukun."

Shima murmushi yayi yace mata "To ai shikenan." ya maida hankalinsa kan tukin da yake.

Shiru Jasmine tayi ta dauki wayarta ta saka earpies a kunnenta ta kunna waka sannan ta bude data ta fara danne danne awayarta basu sake cewa juna komai ba har kusan awa biyu ya shige.

Cire ear piece daga kunnenta tayi sannan ta juyo ta kalli Alamin tace masa "Wai kai baka gajiya da yi shiru ne."

Murmushi yayi yace "Yeah, kin gaji neh."

"Sosai ma and the drive is boring da ma da su Basma ne." Jasmine ta faɗa tana kokarin mayar da wayarta jaka.
Juyo da kansa Alamin ya danyi sanna yace, "Are you indirectly saying that I am boring to be with."

"Eh to, kawai dai ka fiya shiru da yawa," Chocolate ta dauko a jakarta ta bude ta fara sha.

"Well, to kiyi magana mana, ai ina sauraron ki,"

"Tab," taɓe baki tayi "Wato ka sake ce min talkactive,"

Murmushi yayi yace "I won't say that," dan juyowa yayi ya kalleta yaga tana sha Chocolate yace "Yanzu dai nima a bani Chocolate na sha,"

"Guda daya ce ta rage sai dai idan wannan zaka sha,"

Dariya Alamin yayi "Ki ce dai baya surutu ke marowaciya ce,"

Jasmine Baturiyya ceUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum