🌷Shafi na 15🌷

Start from the beginning
                                    

Bayani tayi sosai cikin harshen turanci  sosai domin british accents din baya buya, sai kuma ta dan yi bayani da harshen hausa wanda ba ƙaramin burge hausawa wajen tayi ba, video  mutane suka ringa yi mata da hotuna.

Bayan ta sauko daga kan stage din ne aka fara tafiyar ta motsa jiki wato fun walk, tunda suka fara tafiyar da su Basma mutane ke ta zuwa suna selfie da hotuna da ita akan hanyar, Jasmine zama tayi tamkar wata celebrity a wajen duk da akwai celebrities sosai awajen suma sai hototuna ake dasu, harda matan gomnoni da masu mukami da ma marasa mukami, yan gayu sosai an cika a taron kuma manyan mutane sunje sosai.

Bayan sun dawo daga tafiyar suna tsaye Jasmine ta gama hoto da wata da tazo suyi hoto, ta juyo zata dawo kusa da su Safna ta ji an taka mata kafa da sauri ta dagowa ta ga wanda ya takata, amma kafin tayi magana yarinyar tayi saurin cewa "Dan Allah kiyi hakuri ban kula bane."

Murmushi Jasmine tayi mata ganin ta bata hakuri tace "It's fine." Tsayawa Jasmine tayi tana kallon yarinyar dan ta gane ta, ita ce yarinyar da take kama da Mamanta wacce aka ce mata yar gidan tsohon gomnan kano ce wato Neehla Kabir.

Murmushi Neehla tayi sannan tace "Kamar mun taba haduwa koh?"

"Aa, sai dai me kama da ni," Jasmine ta faɗa hade da murmushi.

"Kina da Yaya ne ko karamar Kanwa?" Neehla ta tambaye ta.

"Aa." Jasmine ta bata amsa a takaice.
"Ikon Allah, amma wallahi ganin nake kamar na sanki." Neehla ta kara faɗa
Murmushi Jasmine ta sake tace "Kinsan daman haka Allah yake Ikonsa, maybe wata relative din tawa kika gani,"

"Hakane, I'm Neehla Kabir, it's a pleasure to make your acquittance," Mikawa Jasmine hannu Neehla tayi tana murmushi.

"Likewise, I'm Jasmine Alejandro," Haunnuta Jasmine ta saka a cikin nata suka gaisa sannan Jasmine ta bar wajen.

Tabo kafadar Basma Jasmine suka juyo suna kallonta dan tarar da su tayi suna hira suke da wani namiji, "Kin gama pictures din Celebrity?" Safna ta tsokaneta.

Murmushi tayi "Ina wani celebrity anan, I'm exhausted wallahi, Ku taho mu tafi gida," Janyo Basma Jasmine tayi amma ta cije tayi taki binta sannan ta  janyo Jasmine baya tace "Okay naji but first ku fara gaisawa da Sabeer, cousin din mu ne,"

Murmushi Jasmine tayi masa tace  "Hi."

Dariya ya danyi sannan yace mata "Hi," yana kare mata kallo yayi sannan ya kalle Basma yace "A ina kuka samo wannan Beauty din?"

Kallonsa ta yi ta dan bata rai saboda bata son irin kallon da yake mata, Hannu ya mikawa Jasmine su gaisa, ta kalli hannun nasa ta dauke kai, bata ankara ba taji ya kamo hannunta, janye hannunta tayi da sauri hade da galla masa harara, shiko kara yake baki yayi yana mata murmushi yace "Oh I'm sorry, I thought....." sai kuma yayi shiru.

"You thought what?" Basma tayi sauri tambayarsa "Matar Yaya Alamin ce fa."

"Aa, ba Nadia zai aura ba?" Yayi saurin tambayarsu.

"Kana chan kana shashancinka ta Ina zaka san wacca ya aura." Khadija ta bashi amsa rai a bace ganin har yanzu bai chanja halinsa na san mata ba.
Juyawa yayi ya kalli Khadija sannan yace "Ina ruwanki to."

"Ni wallahi matsala ta da kai kenan, daman na sani baza ka taba chanjawa ba, Allah ya shirye ka," Basma ta hade rai "Ku taho mu tafi." ta faɗa tare da jan hannun Jasmine wacce ta tsaya tana kallon ikon Allah.

Suna shiga mota Jasmine tace "Wai waye wan chan mutumin."

Khadija ce ta bata amsa "Cousin dina ne, ɗan gidan Yayan Mamana(Yayan Hajiya Saudat) ne kiyi hakuri Dan Allah, haka halinsa yake shi yasa ma bama shiri ko kaɗan."

"Ba komai, ya wuce ai," Jasmine ta faɗa hade yi mata ɗan murmushi.


Assalam Alaikum
Da fatan kowa yana lafiya, yah sanyi?
Dafatan dai kun kula da cigaban da muka samu, yanxu update baya kaiwa sati daya yay 😀 💃🏻💃🏻💃🏻.
Kar dai ku manta ku fada min ra'ayoyin game da wannan shafin domin honestly speaking Comments dinku neh ke motivating dina na cigaba da rubutu, and every single comment matters ❤️❤️.
NA GODE

Instagram @amiratuoo
Twitter @AminaUmzak
Facebook Amina Umzak
Inkitt @amiratuoo

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now