🌷Shafi na 9🌷

Start from the beginning
                                    

Jamal yi yayi kamar bai jita ba ya cigaba da matsowa, "Nace maka ka rabu da ni." Jasmine ta sake fada tare da jan gashinta da ya zurzubo ta ko ina baya dan har ya rufe mata fuska.

Cikin fushi harshen ta ya juye ya koma yaren espanol (Spanish) ba tare da ya lura ba "No quiro verte Jamal, Tu no eres mi hermano, porque mi hermano nunca me hará daño.” (Bana son ganinka Jamal, kai ba dan uwana bane yanzu, ɗan uwana da nasani bazai taba yadda a cutar da ni ba)
Chak Jamal ya tsaya yana kallonta idanuwansa duk sun yi ja da jin kalamanta, domin tunda suka taso, Jasmine bata taba fushi da shi har haka ba, a hankali shima yace mata cikin yaren spanish din "Jazmín Lo siento pero déjame explicarte, Sabes que nunca haré nada para lastimarte.” (Jasmine dan Allah kiyi hakuri ki bari nayi miki bayani, ki saurare ni, kinsan bazan taba yi abinda zai cutar da ke ba)

Dariya takaici tayi, idanuwanta cike da hawaye tace "Cómo si fuera Verdad, Sal por favor, No quiero verte.” (Kamar da gaske, ni dan Allah ka fita ka bani waje bana son ganinka)
Jamal banza yayi da abinda ta fada ya matso daf da ita amma kafin ya tabata ta hankaɗa shi baya, ta fara dukansa a kirji tana kuka tana ta yi magana cikin yaruruka fiye da uku dan ita kanta bata san wani yare take yi ba acikin yarukan da ta iya. Dukansa ta cigaba da yi tana kuka, ya kyaleta ba tare da yace komai ba ko ya hanata domin yasan ta haka ne kawai zata fitar da fushi da fushi da baccin ran da take ji.

Alamin da ke gefe guda a tsaya a yana kallonsu cike da mamakin yadda ta kasa bawa yayan nata dama yayi magana, dan shi a nasa tunanin ko me mutum yayi maka at-least ka bashi dama yayi maka bayani mana kafi ka yanke hukunci. Ji yayi duk ransa ya bacci ganin yadda take ta kuka ta dau abin da zafi da yawa tamkar wacce aka yankewa hukuncin zaman gidan yari, gabaki daya fuskarta tayi ja.

Gani yayi kuka nata yayi yawa tabbas idan ya barta a haka zata iya jawo wa kanta wani ciwon, hakan yasa yayi sauri ya karaso wajen da suke ya janye Jasmine din daga jikin Jamal ya rike mata hannaye tana ta kokarin kwacewa amma ta kasa saboda irin riko da yayi mata.

Fuskar ba walwala ya ce "Jamal you can leave." kallonsa Jamal yayi ya sake kallon ƙanwarsa, ajiyar zuciya sannan ya juya ya fita bai ce komai ba dan ya yarda da Alamin yasan ba yi abinda zai cutar da ita ba.

Yana fita Alamin ya cikata ta faɗa kan kujera, mikewa tayi zata tashi ya daka mata tsawa "Sit back and shut up."

Dan firgita Jasmine tayi saboda bata saba ba, da ba'a yi mata tsawa a gidansu ko fada Papá da Jamal basa yi mata duk abunda take so shi ake mata. Komawa tayi ta zauna a dan tsorace, sannan shima ya zauna a kujerar da ke kallon tata.

Sai da ya ja yan mintuna kafin yace "I never expected something like this from you Yasmine, na dauka zakiyi handling case dinnan differently ba kamar yadda Nadia tayi ba with violence."

Shiru tayi masa fuskarta a rufe da gashi domin har ta gaji da gyara shi, ganin tayi shiru yasa ya cigaba da cewa "Da kin bari an miki bayani kafin ki yanke ko wani irin hukunci, beside ke kika fara wannan mission din na taimakon Nadia fa and it's all part of it."

Jasmine dagowa tayi ta gyra gashinta sannan tahl kalle shi tace "This is ridiculous, taya Aurena da condition din Nadia suka hadu, it doesn't make any sense."

"Well, kinsan dai mu musulmai neh ko?" Ya tambaye ta bata bashi amsa ba sannan ya cigaba da cewa "Musulci ya gindaya mana wasu Sharuda Yasmine, kamar yadda ya bamu damammaki, wanda dole mu bisu domin samun zaman lafiya a duniya da kuma samu rahma a lahira."

Shiru ya dan yi sannan ya cigaba da cewa "Yasmine, Haramun ne Auran mace mai ciki a addinin Musulunci. sannan kince bakya son Nadia tai abortion wanda shima haramun ne kuma zai cutar da lafiyarta, Kinga kuwa idan ba abortion tayi ba, ba zai yiwu na Aure ta ba. Gashi mun tara mutane da yawa, jama’a sun zo domin bikin nan, ya zamuyi da su? you know I can't just call off the wedding at the last minute, mutuncin gidanmu ne zai zube."

Jasmine dagowa tayi tana kallon shi domin ta fara fahimtar abinda yake nufi, Sannan ya cigaba da cewa "Kinga ke kadai ce kika san komai akan wannan maganar, so you're our only option akan aure. nan, bayan an gama all this wedding drama idan zaki koma Cambridge, I'll divorce you, it's nothing serious."

Jin kalmarsa ta karshe ne ya sa hankalin Jasmine kwanciya, domin kuwa indai zai saketa idan zata koma garinsu ai bata da matsala da auren tunda ba auren gaske bane domin ko yan'uwanta na Spain baza ta bari su san zancen nan ba, balle Matthews Masoyinta, baza ta so yaga kamar ta ci amanarsa ba, saboda haka dole tayiwa Jamal magana akan kar ya bari kowa ya san maganar Auren nan.

"Na yarda as long as you keep your words." Jasmine ta fada tare da daukan Jarkar ruwan da ke kan karamin table din gefenta ta sha, sannan ta kara da “And, bazan tare a Gidan da zaka saka Nadia ba anan zan zauna and it’s a phony marriage no strings should be attach.”

Murmushi yayi mata yace “You have a deal, zaki iya zabar ko wani daki kike so nan sai ki zauna,” Sannan ya tashi zai fita, "Alhamdulillah." ya fada a hankali yadda shi kadai yaji abunsa, har ya kai bakin kofa ya sai kuma ya tsaya ya juyo, "Yasmine." Ya kirata a hankali.

Dagowa tayi ta kalle shi, sannan yace "Duk abinda ya faru fa ba lafin Jamal bane, bashi da zabi ne and you're our only hope in saving Nadia and my Family’s reputation, You should talk to him."

Ya na gama magana ya fita daga bangaren nasa domin zuwa ya warware sauran matsalonin.
.
.
.

Don't forget to comment and vote
Follow on
Instagram: @amiratuoo or @amiratuoowrite
TikTok: @amiratuoo
Facebook: Amina Umzak
Inkitt : @amiratuoo

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now