🌷Shafi na 1🌷

5.9K 297 18
                                    

Edited

  Wani kerarran jirgin neh ke tashi a sararin samaniya, shi bah kato bane sosai kamar sauran jiragen da ake hawa yau da kullum, Jirgi ne wanda masu ji da kudi ko mulki ke mallakarsa tamkar motar hawa, domin kai su duk inda suke bukata. Wannan jirgi dai ana kiransa da Private Jet . Duk wanda ka gani acikin irin wannan jirgin to tabbas yafin karfin abubuwan kyalekyalen rayuwar nan ta yanzu. Acikin wannan kerarran jirgin wata Matashiya ce zaune cikin peach din doguwar riga ta kamfanin Gucci wacce ta zarce gwiwarta da kadan, high heels ne a kafarta masu kyan gaske, domin irinsu ne ka ke gani a kafafun celebrities a kan red carpets. Gashin kanta kuwa a tattare yake irin tattarar nan da ake kira da ponytail, sak irin gyran gashi da Ariana Grande ke yi, gashin ya sauko har ya kusa dabo kugunta. Kyakyawar matashiyar dai bata wuce shekaru Ashirin da biyu 22 bah a duniya. Idan kayi mata kallo daya  baza ka taba kawowa tana da hadi da Africa bah domin yanayin kalar fatarta ba irin tamu ta nan bace, dan ko a turawa ma samun mai irin hasken fatar sai an dage, kwayar idanunta kuwa ba brown bane kamar na yawancin yan Africa hazel-green ne. Ga kuma tsabagen kyawun da Allah yayi mata. Kallo daya zaka yi mata kasan tabbas irinsu neh matan da ake rubutawa a cikin littattafai domin ko bata da makosa ta ko kaɗan. 

       A zaune take da littafi mai suna Magana Jari Ce Na 1 a hannunta tana karantawa, gabaki daya hankalintah yana kan littafin amma da alama ba karatun take ba domin kuwa har wani kyakyawan saurayi ya zo ya zauna a kusa da ita bata lura ba. Shima saurayin kallo daya zaka yi masa kasan tabbas jinin turai neh saboda kalar fatarsa iri daya take da ta budurwar da ya zauna akusa da ita, kana ganinsa kaga bature, kamanin da ke tsakaninsa da buduwar yayi matuka dan ko ba’a fada maka ba kasan yan uwa ne.

"Estás leyendo o pensand,” (Karatu kike koh tunani) Tambayar da kyakyawan saurayin yayi wa kanwarsa kenan cikin harshen spanish.

Murmushi tayi sannan ta dago kanta ta kalleshi tace, "Ambas, No puedo esperar para aterrizar,  Todo lo que quiero es verla,” (Duka biyu, kasan na kagu mu isa, domin bani da burin da wuce na ganta)

Yar karamar dariya mara sauti ya fita sannan shima yace "Hermanita, In'sha Allah La verás tanto que estarás aburrida.” (Kanwata kenan, Insha'a Allah zaki ganta har ki gaji da ganinta)

Girgiza kanta matashiyar tayi tace "Nunca puedo aburrirme de ella.” (Nidai bazan taba gajiya da ganin tah bah)

Shiru ya danyi kafin yace "Mi amigo esta fuera de la ciudad, El me llamo. así que no puedo quedarme en Kano, Tengo un negocio urgente que atender, Regresaré el próximo mañana.” (Abokina da zaki sauka a gidansu baya gari, nayi waya da shi. Kinga kuwa bazan dade bah a Kano, ga kuma wata matsala da ta taso min, saboda haka bayan mun sauka washe gari da Yamma zan koma saboda kar ayuka su taru su yi min yawa)

Dan bata rai kadan tayi sannan tace "Okay, pero ía que te quedaras y me mostraras.” (Okay, amma gaskiya naso ka zauna tunda kaga kai ka saba zuwa sai ka nuna mun gari)

Jasmine Baturiyya ceWhere stories live. Discover now