Chapter 50

2.7K 394 35
                                    

"Direct asibiti aka wuce da nabeelah aka fara bata taimakon gaggawa duk da kuwa su kansu likitoci jikinsu sanyaye suke bawa nabeelah kulawar don zeyi wahala ta rayu,,,What?innalillahi wa inna ilaihir raj'uun deen ya fada lokacin da wayar ta sulale kasa jiri ya fara dibansa yai saurin zaunawa a kasa yana goge gumin dake zubo masa,sai da jirin ya lafa mishi tukunna ya mike ya dauki motarsa ya fice daga gidan da gudu,a parking space din asibitin yayi parking ya fito da sauri ya karasa accident and emergency ba tare da ya rufe ko motarsaba sannan likitoci sun tabbatar masa baze samu damar ganin nabeelah ba yanzu tana theatre room,dakin da ake kula da sadiq ya wuce direct ji yake inama Allah ya dauki ransa a wannan lokacin gaba daya duniyar baya jin dadinta,jikinsa sanyaye ya tura kofar dakin ya shiga.....a tsorace doctor ya juyo ya fara yin gumi jikinsa na karkarwa allurar dake hannunsa ta fadi kasa,tsugunawa yayi ya dauki allurar tare da kwalbar....diazepam injection ya fada a takaice yana cigaba da jujjuya allurar a hannunsa,cikin rashin fahimta ya kalli doctor din dake faman karkarwa a tsaye yace doctor diazepam injection for what?cikin rashin gaskiya yayi murmushi yace sorry sir dama nayi mistake ne wajen dauko allurar amma yanzu zan mayar,kyawawan mari guda 2 ya sauke a cheecks din doctor din sannan ya kalleshi zuciyarsa na tsananin bugawa yace meyasa zaka dinga yi masa allurar bacci ta mahaukata?shiru doctor yai ya saukar da kansa kasa jikinsa a matukar sanyaye,riko gaban rigarsa ya sakeyi a fusace yace uban waye ya saka ka dinga yi masa allurar bacci?ganin yanda idon deen ya kada yasa doctor matukar tsorata yace kayi hakuri ka sakeni zan fada maka duk yanda akai.....

"Wayar dake hannunsa ce ta fara kara,sunan dad ya gani jikin screen din da sauri ya daga wayar
cikin rikicewa yace dad a ina aka ga mom din?fita yai da sauri ya samu dad a gida tare da mom cikin tashin hankali yake kallon yanda mom ta fita hayyacinta,kamar ba mom yar gayu da ya saniba,a tsorace ya kalli dad yace ina aka ganta?girgiza kai Alhaji modibbo yai yace godewa Allah ya kamata ka fara yi tukunna domin zulaikha da mahaifiyarta basa kaunarmu ko kadan,da sauri ya mike ya karasa dakin zulaikha sedai wayam babu komai a dakin sun hada kayansu ita da hajiya saratu sun gudu daga gidan

"Sai da nabeelah ta kwana 3 tukunna ta farfado,sosai deen ya shiga damuwa kamar wani zararre komai na duniyar baya masa dadi,tuni yasa aka kama doctor din da zulaikha tasa ya dinga yiwa sadiq allurar bacci an kulleshi tare da takardar korarsa a aiki,an samu sadiq ya farfado inda yake cigaba da samun sauki

"Kallon hajiya saratu tayi cikin damuwa tace momy wlhy muna cikin tsaka mai wahala,momy yanzu me kike tunanin za'ayi mana idan aka kamamu?ajiyar zuciya hajiya saratu tai tace zulaikha na fiki damuwa domin idan aka kamamu toh lallai munyi sallama da farin ciki a rayuwa zamu karashe rayuwar mune a prison....kinfi kowa sanin su waye family alhaji modibbo sun yarda damu sun bamu amana mu kuma munci amanarsu zulaikha meyasa kika bari wannan abun ya kwabe mana haka?

"Tsaki zulaikha tayi tace haba momy meyasa kike wannan maganar amma dai kinsan da sanina bazan bari a samu matsalaba duk wani kokari da zanyi nayi amma seda deen ya gane halin da nake ciki,,,mikewa tai ta kalli hajiya saratu da tai tagumi tace momy ki tashi ki fara hada kayanki don kinsan nan dinma bamu tsiraba yanzunnan zamu siyi ticket mu koma scotland,cikin 20 minutes har sun gama hada kayansu da suke bukata suka fito hannunsu rike da travelling bag zasu wuce airport,driver ne ya karbi jakunkunan nasu yasa a mota sannan suka shiga mai gadi ya bude gate,sedai suna fita sukaga cincirindon motocin yan sanda na jiransu a waje kowanne hannunsa rike da bindiga akayi arresting dinsu

"Sanye yake cikin sky blue shirt da black jeansy trouser wanda yai matukar fito masa da kyansa,jikinsa sanyaye ya tura kofar dakin ya shiga idonsa ya sauka akan nabeelah da take kwance bata iya komai hatta abinci bata iyaci da kanta,sosai ya tausayawa nabeelah kallo daya yai mata ya dauke idonsa ya gaisheda aunty a'i ya zauna akan cushion din dake gefen gadon nata...ya dade zaune kafin mom da alhaji modibbo su turo kofar su shigo cikin tsananin tausayi sukeci gaba da yiwa nabeelah sannu,,,sai da nabeelah tai 2 months a asibiti kafin a sallameta su koma gida kusan kullum sai deen yaje asibitin ya duba nabeelah,itama nabeelah ta saki jikinta sosai da deen

"A palour ya tarar da mom tana watching movie,gefenta ya tsuguna ya gaisheta sannan ya kalleta yace mom gani dazu naji sadiq yace kina nemana,ajiye remote din dake hannunta tayi tace deen ba wani abu bane yasa kaji ina nemanka se ganin yanda kake shisshigewa yarinyarnan nabeelah,toh inaso ka bude kunnenka da kyau ka saurareni nabeelah ba sa'ar aurenka bace yarinyar da ta nuna bata sonka ta fito fili ta nunawa duniya batasonka toh koda yanzu ta dawo tace tana sonka karya takeyi akwai wata manufar a zuciyarta

"Kallonta yai da sauri yace amma mom inaso ki gane sanin da kika yiwa nabeelah wancan lokacin ya banbanta da wannan lokacin,a yanzu inada tabbacin son da nabeelah kemin na gaskiyane kuma nasan idan na auri nabeelah zakuyi alfahari da ita......dakata min mallam,dakata min ta fada cikin masifa sannan ta mike tsaye a zafafe

"Inaso in tabbatar maka wallahi tallahi bazaka auri nabeelah ba indai ina raye domin tsarinta da tarbiyarta bata yiminba,bari kaji in fada maka nifa har yanzu ban yarda hajiya saratu ce da zulaikha sukasa aka saceniba,sannan har yanzu ban yarda zulaikha nada cutar kanjamau ba kuma har yanzu ban yarda zulaikha ita tasa akayi kokarin kashe nabeelah ba.....duk wannan abin makircine irin na nabeelah da gayyar tsiyar iyayenta don haka bazan taba yarda ka auri nabeelah ba indai ina raye,,,,ya isa haka,ki dakata min haka kafin ranki yai mummunan baci sukaji ance,a tare suka kalli inda Alhaji modibbo ke karasowa zuciyarsa na tafasa sannan ya kalli deen yace jeka abinka insha Allah aurenka da nabeelah kamar anyi an gama ne,jikin deen sanyaye ya haye upstairs ya bar mom da Alhaji modibbo tsaye

"Girgiza kansa yai yace aure kamar anyi an gama da yardar Allah kuma kina raye shashashar banza da wofi me musu da ikon Allah,be jira tace komaiba yayi ficewarsa waje,,zubewa tai akan kujera kamar marar lafiya gumi ya fara gangaro mata,murmushi tai a hankali sannan ta janyo wayarta tace indai boka me ruguzau yana nan toh tabbas kuka ya qare min a duniya

It's been a long time people,sorry for my late in update,by the way don't forget to vote,share and comment....it mean alot to me

DeenWhere stories live. Discover now