Chapter 9

3.3K 337 35
                                    

"A daren ranar sam nabeelah bata rintsaba,8am ta tashi duk nauyin da jikinta ke mata be hanata shiryawa da sauriba cikin doguwar riga abaya,travelling bag ta dauka karama ta nufi apartment din dad dinta,gaisheshi tai cikin girmamawa sannan suka yi sallama tare da yi mata transfer din kudade duk da account din nabeelah cike yake da kudi bata bukatar karin hakan

"9:30am private jet din deen ya tashi dasu nabeelah zuwa babban birnin london dake united Kingdom(UK),nesa da seat din deen nabeelah ta zauna,shima bangaren deen ko kallon inda nabeelah take beyiba,suna sauka a jirgi deen ya mikawa nabeelah key din gida tare da address,karba tai ta karanta ba tare da tace komaiba,ajiyar zuciya yayi sannan yace we are here for work and you are still my P.A,zamuyi aiki gobe a Gk enterprises 9:00am dot,be sake cewa komaiba ya shige taxi ya wuce ya barta tsaye

"Itama taxi din ta shige,ta karasa da ita gidan da zata zauna har su koma 9ja

"Salloli tayi,sannan taci abinci saboda gajiyar da tayi yasata hawa gado bacci me karfi ya tafi da ita

"Shima bangaren deen baccin yayi saboda gajiyar da yayi

"Ganin 8am yasa nabeelah saurin saukowa daga kan gado,da gudu ta shiga bathroom tayi wanka ta fito,light makeup tai sannan ta karasa travelling bag dinta ta bude ta saka black pencil skirt da white long sleeve shirt and top kamar yanda ta saba,tea tasha da peppered chicken sannan ta fita ganin har 8:45am,taxi ta shiga cikin sauri aka qarasa da ita G.k enterprises

"Hannunta na rawa ta danna elevator ya karasa da ita inda deen ya fada mata matsayin office dinsa,knocking tai sannan ta tura kofar ta shiga jikinta na matukar rawa ta tsaya gaban kujerar da yake zaune yana danna laptop,tamkar be san mutum ne tsaye yake jiransaba

"Ganin bashi da niyyar yin magana yasa nabeelah bude baki tace morning sir

"Dagowa yai ya kalleta sannan ya janyo file din da zai shigar da details dinta,ba tare da ya kalletaba yace your name?

"Mamakine ya kama nabeelah tare da takaici wato banda iskancin deen,akan zai shigar da information dinta har seya tambayeta sunanta,muryarsa ta qara ji a karo na 2 yace give me a answer because you are wasting my time

"Na....nabeelah ta fada jikinta a sanyaye

"Nabeelah who?did your parents rejected to give you a last name?or are you incapable of answering my question to it's full capacity?ya fadi maganar a zafafe

"May be ta fada a zuciyarta,amma a zahirance saurin bude baki tai tace nabeelah kamal

"Dagowa yai ya kalleta fuskarsa babu alamar dariya yace kinsan london ba Nigeria bane,don haka idan har zakiyi aiki dani a london ya zama dole kiyi amfani da rules dina got it?

"Daga kanta tai tace okay

"Dauke hannunsa yai daga kan laptop ya hadesu guri daya yace rule no 1:you have to be here on time coz i absolutely hate waiting,Rule no 2:you are my personal assistant so you will assist me in everything without asking me a question,Rule no 3:i don't tolerate stupidity or sarcasm coz i am a straight forward person,Rule no 4:you most definitely follow rule 1,2 and 3 are you comfortable with my rules?

"Saurin daga kanta tai alamar eh

"Great ya fada sannan yaci gaba da aiki a laptop dinsa

"Itama kujerar dake gefensa ta samu ta zauna,ta fara karanta messages din da ake turo mata ta WhatsApp

"Dagowa yai ya kalleta yace i don't appreciate laziness,if you don't want to do anything then you have to stay at home and watch cartoons

"Dariya tai a hankali don ita kam yanzu deen ya fara dena bata tsoro,tasowa tai tace how can i help you?

"Coffee ya fada a takaice

"Murmushi tai tace how do you like it to be?

"Dora hannunsa yai akansa ba tare da ya bata amsartaba yace where is your book and pen?

"Saurin kallonsa tai cike da mamaki tace book and pen for what sir?

"Dagowa yai a fusace yace don't you answer my question with a question again.....idan chan kina aiki da laptop toh anan da notebook zakiyi amfani to write all my tasks down

"Daga mishi kai ta sakeyi

"Sai 5pm bayan sun gama gudanar da meeting dinsu,deen ya debi wayoyinsa tare da jacket dinsa har seda ya karasa bakin kofa tukunna ya kalli nabeelah yace you can also go

"Bin bayansa tai da kallo,deen ya kai duk yanda akeson namiji ya kai,kyakkyawane ajin farko sedai halayen deen sun bata masa gaba daya kyawun surarsa,ya kasance mutum mai zafin gaske,mugu,azzalumi kuma mara tausayi wanda ya dauki mace kamar shirt din da kullum seya sake wata,sedai abinda deen be saniba shine ba kowacce riga ake sawa a cire lokaci dayaba,ba tare data shiga ran mutum ba...akwai rigar da dole seta zamewa mutum uniform wato a dole se an maimaitata

"Seda nabeelah ta tabbatar da deen yayi nisa da tafiya tukunna ta fito ta tari taxi ta karasa da ita gida,abinci taci sannan ta gabatar da sallar magriba ta jira isha'i tayi sannan ta watsa ruwa ta nufi bedroom don ta gaji sosai,baccine ya dauki nabeelah,cikin bacci ta fara jin knocking din kofa,a firgice ta mike sannan ta kalli agogon dake jikin bangon dakin,it was 9:56pm ta fada a hankali

"Mikewa tai ta karasa bakin door din ta tsaya a hankali tace waye,muryar deen da ko a dubunnan jama'a nabeelah taji seta ganeshi taji yace "your boss" cikin muryarsa mai zafi

"Gabantane ya fadi,tuni gumi ya fara karyo mata,ganin ashe kofar ba'a rufe take ba ta manta bata rufe da key ba yasa nabeelah dora hannu akanta a hankali tace na shiga 3

"Ganin nabeelah bata da niyyar bude masa kofar ya sashi murza kofar ya bude sukayi ido hudu a tsaye...

Thanks for reading my story
Don't forget to vote,share and comment
Lot's of love from
Heroine

DeenWhere stories live. Discover now