Chapter 44

2.5K 260 26
                                    

"A zahiri deen ya daukarwa kansa alwashin mantawa da duk wani lamari na nabeelah sedai zuciyarsa na wasi-wasin anya ze iya rayuwar farin ciki da wata mace a duniya indai ba nabeelah ba,,,mom ce ta turo kofa ta samu deen zaune yana aiki a system dinsa,dagowa yai ya kalleta a hankali yace hey mom...gefen gadon ta zauna sannan ta kalleshi tace suprise,,,murmushi yayi yace really mom?dariya tayi tace na samo maka yarinyar da nasan itace dai-dai da tsarinka bana doubting akanta don nasan definitely zata birgeka

"Murmushi yayi yace wow sannan ya dago ya kalleta yace thank you mom,a ina yarinyar take?

"Yar gidan kawata ce hajiya saratu sunan yarinyar zulaikha bazaka santaba don last year ta dawo daga Scotland ta gama karatun medicine,yarinyace mai hankali da nutsuwa sannan kuma kyakkyawace

"Murmushi ya sake yiwa mom yace toh shikenan mom yanzu yaushe ya dace naje wajenta?ya karasa maganar yana jin kunya

"Kunnensa taja a hankali tace trouble maker,a yanzu haka zulaikha tana cikin gidan nan tunda mom dinta ta nuna mata picture dinka shikenan ka rudeta dazun nan sai gata tazo gurinka don haka yanzu ina fita zan turota,da sauri walwalar fuskarsa ta sanja ya kalli mom cikin rashin fahimta yace mom ki turota tayi min me?

"Na turota ku dai-daita kanku mana,murmushi yayi yace amma mom ai niya kamata inje in sameta meyasa ita da take mace zatazo gurina?

"A fusace ta kalleshi tace what the hell are you telling me?kaine ka haifeni ko nina haifeka?idan kai bakasan daraja da daukakar da Allah yayi maka ba toh nina sani.....deen kyawunka da arzikinka ya wuce duk inda kake tunani,menene a ciki don mace ta kawo kanta gareka da sunan proposal,ka isane don haka bana bukatar sake jin wani zance daga bakinka just do what i said.....tana gama fadar haka ta fita daga dakin

"Bin ta yayi da kallo har ta fice daga dakin zuciyarsa na tunanin me mom ke shirin aikatawa?wacce yarinyar mom ke shirin bashi a matsayin matar aure

"Kallon agogo yayi yaga 7:30pm,yana sauke idonsa aka fara knocking din door,come in ya fada cikin muryarsa me daukar hankalin me sauraro,turo kofar tayi ta shigo sedai bata sake koda taku daya ba, a bakin kofar kamar gunki ta tsaya tana yi masa murmushi.....farace sosai me dan jiki ba wata doguwa bace kuma baza a kirata da gajera ba tana da siririn hanci ba wani me tsayi sosaiba,idanuwanta manya da dan karamin bakinta me dauke da wushirya a tsakiyar hakoranta...tana da hips sosai da manyan boobs,riga ce gown jikinta wacce ta matseta ta fito mata da shape din jikinta se hula turban kalar rigar jikinta ba tare da mayafiba ta tsaya tana wani girgiza jiki cikin salo irinna yan bariki

"Saurin dauke idonsa yayi daga kallonta muryarsa a sarqe yace have a seat,gefen bed din da yake zaune ta zauna itama kusa dashi....ganin bashi da niyyar dagowa yayi mata magana yasata dafashi kadan tace hey baby

"Rufe system din yayi yace hey ransa a matukar bace sannan ya kalleta yayi murmushi kadan....a zuciyarsa yana sake takaicin wacce irin rayuwa mom keso yayi da wannan yarinyar?wanne irin zama takeso suyi a matsayin mata da miji....ganin bata da niyyar dena yi masa rawar kai yasa deen kallonta yace i'm coming ya fita ya barta nan zaune

"Cigaba tayi da kallon agogon hannunta har 1 and half hour amma be dawoba,Kiran wayarsa ta farayi shima be daga ba,a fusace cikin bacin rai ta dauki motarta ta fita da gudu zuciyarta a bace ba tare da tayiwa mom din deen sallama ba,a palour ta tarar da hajiya saratu tana kallon kwana casa'in series a arewa 24,kamar zata bigeta haka ta wuce dakinta

"Da sauri hajiya saratu ta ajiye remote din dake hannunta ta karasa dakin zulaikha da gudu tace lafiya zulaikha meya faru ne?fashewa tai da kukan shagwaba tace hajiya wlhy deen baya sona,bakiga se wani shareni yakeyiba yanxufa tafiyarsa yayi ya barni zaune se gajiya nayi nima na taho fa.....kallon zulaikha tai cikin mamaki tace kan uba,kinyi duk abinda nace miki kiyi kuwa zulaikha nasan shirmenki fa...mikewa tsaye tai tace wlhy hajiya babu wani salo da banyi mishi ba amma sam bama ya kallona balle ya fahimci me nakeyi mishi,,,,,girgiza kai hajiya saratu tayi tace ki kwantar da hankalinki zulaikha badai mahaifiyarsa na sonkiba kuma meye abin damuwa tunda wani satin zai kawo kudin aurenki asa muku ranar aure dashi

"Murmushi zulaikha tai tace hakane sannan ta wuce bathroom. ...

"Fatima ce zaune a gidan aunty lami tana jiran nabeelah ta fito daga bathroom,tana fitowa ta dauki abaya ta saka ta shafa body lotion kadan sannan ta kalli fatima tace toh sarkin rashin hakuri ba gashinan har na fito ba....murmushi fatima tayi tace eh naji din kinsan matsalata nace miki saurayinane zezo anjima banaso yaje be sameniba kinsan yanzu mazan seda lallabawa musamman irinmu wayanda aka lalatawa rayuwa idan nai sake sena mutu banyi aureba duniya na zagina..kinga kuwa yanda na samu namijin duniya kamar nabeel ai dole na rike abuna hannu bibbiyu

"Murmushi nabeelah tayi duk da fatima ta sosa mata inda ke mata kaikayi sedai a dole ta boye damuwarta tace wannan haka yake tawan,gyara zama fatima tai tace kinga niba zama nazo yiba wata gulma nazo watsa miki kinsan wannan deen dan gidan alhaji modibbo dana baki labarin yayi raping dina ko?gaban nabeelah ne yai mummunan faduwa tai saurin dagawa fatima kai tace ina jinki,,,,ajiyar zuciya tai tace toh in gaya miki Allah dai ba azzalumin bawansaba yanzu haka zancen da nake miki gobe za'asa masa rana da wata kawata zulaikha yar gidan sallau me dollars,kuma kinsan me?

"Sake girgiza kai nabeelah tayi gabanta na matsananciyar faduwa tace go straight to the point teemah ina sauraronki,dukan cinyar nabeelah fatima tayi kadan tace kai kawata akwai kida son jin gulma,toh wannan zulaikhan dai tsohuwar karuwace a Scotland tai karatu babu wanda besan yanda zulaikha ta shahara gurin bin maza har bin mata ma,sannan babban abinma shine saurayinta da suke lalacewa me suna damaske H.I.V ne dashi kuma itama zulaikhan H.I.V gareta....amma shi deen din be saniba a haka zai aureta kinga kuwa Allah yayi gaskiya da yace kome kayi shi za'ayi maka zulaikha itace dai-dai dashi idan yaje ya kwasowa kansa cuta seya gane duniyar bashi kadai ne cikintaba

"H.I.V beelah ta fada tana dafe kirji,tsaki teemah tayi tace toh meye abin damuwa ai abinda yai yake ganin ishara

"Kallon teemah tayi tace amma teemah ina ganin kamar hakan be daceba please ku sanar dashi mana

"Tsaki teemah tayi tace wallahi bazamu sanar dashiba nifa dadina dake rashin kishin kai....kinga ni tun kafin ki bata min rai kinga tafiyata,tana gama fadan haka tai tafiyarta

"Da sauri nabeelah ta mike tsaye gabanta na faduwa zuciyarta na bugawa da sauri,har 2 na dare amma nabeelah ta kasa runtsawa tsaki tayi tace wai meyasa zan damu da rayuwar mutumin da be daceba?meyasa zan damu kaina?meye don ya auri me H.I V dai-dai kenan tunda ba mutumin arziki bane,,,,,,saurin girgiza kanta tayi tace nooooo ba abu me kyau nake shirin aikatawa ba ya zama dole in sanar da deen

"Kwance yake yana juyi ya kasa barci kallon agogo yayi yaga har 2:30am amma babu alamar bacci a idonsa,wayarsa ce ta fara ringing cikin mamaki ya sake kallon agogo sannan ya daga wayar ganin bakuwar number

"Hello

"Hey ta fada muryarta a sanyaye

"Who is on the line?ya fada yana sake kallon agogo

"Nabeel......

"Be jira ta karasa magana ba ya kashe wayar ransa a matukar bace,wanne kalar wasan kuma ta kira tayi min?ta fadawa duniya cewar bata sona meyasa zata kirani kuma....you are late beelah bazan sake saurararkiba,,,,yana gama fadar haka ya mike ya shiga ya dauro alwala ya fara nafila duk da kiranta da yake sake gani amma be dagaba

Check out my new story MU'AMALAT trailer
Don't forget to vote,share and comment
Thank you for reading my story

Deenحيث تعيش القصص. اكتشف الآن