Chapter 39

2.9K 299 14
                                    

4 months

"Bayan anyi duk wani bincike an tabbatar da cewar ba deen ne ya kashe yarinyar da ake tunaniba wasu yan daba ne suka bata silent poison tasha saboda ta damfaresu shine a yammacin ranar deen ya dauko ta don aikata alfasha da ita kafin ya shiga bathroom yai refreshing jikinsa har ta mutu,an dade ana fafatawa da manyan lawyers kafin a gano gaskiyar cewa ba deen ne ya kashetaba daganan aka karkata kan karar mahaifin sumayya akan fyaden da yayiwa yarsa

"Komai deen gani yake yi kamar a mafarki gaba daya mamakin halin da ya shiga yake yi....ashe dama haka duniya take?gaskiyane da akace babu wanda ya isa ya zauna lafiya indai akwai haqqin wani akansa,gashi tun kafin aje ko'ina duniya ta koya masa babban darasi wanda zai dade yana yawo a cikin kwakwalwarsa har karshen rayuwarsa,yana cikin wannan tunanin sadiq ya turo kofa ya shigo kamar kullum jikinsa sanyaye fuskarsa babu wata walwala ya zauna a gefen cushion din da deen yake zaune ya dafa shoulder din deen yace tiger muryarsa kasa-kasa

"Dagowa yai ya kalleshi da jajayen idanunsa sannan ya saukesu daga kallonsa a hankali,sake gyara zama sadiq yayi yace haba tiger all this worries are for what kuma?meyasa kullum bazaka dena wannan damuwar taka ba komai fa ya riga ya wuce to meye kuma zaka damu kanka da tunani

"Ajiyar zuciya deen yayi yace i most worry sadiq,dole na damu...damuwa ta zama dole

"Kallonsa yayi cikin mamaki yace why?

"Beelah ya fada jikinsa a sanyaye

"Tsaki sadiq yai yace sau nawa zan fada maka cewar nabeelah tana sonka

"How can i believe it?deen ya fadi maganar cikin rashin yarda

"Trust me tiger,just trust me please

"Mom ce ta karaso hannunta dauke da katon tray na fruits ta ajiye gaban su sadiq sannan ta hararesu kadan tace oya take it stubborn kids kuma idan kun gama Alhaji yanason ganinku

"A tare sukayi dariya don tunda su deen suka dawo daga court mom ta tabbatarwa kanta abubuwan da deen da sadiq ke aikatawa take kiransu stubborn kids ko tace musu crazy souls

"Basuyi wani taking time ba suka karasa apartment din dad a tare suka zube gabansa suka gaisheshi,murmushi yayi ya kallesu sannan yace zahradeen naga har yanzu baka koma bakin aikinkaba me yake faruwa ne?

"Sunkuyar da kansa yai kasa yace dad ina hutawa ne kadan

"Murmushi dad ya sake yi yace hutun me?gaba daya companies din nawa zaka dauki hutu?ya zama dole gobe ka koma office dinka sannan kaci gaba da tuba kana rokon Allah gafara insha Allah komai zai wuce,bayan dad ya gama yiwa su sadiq nasiha ne suka tashi suka fita

"Bathroom deen ya wuce yayi taking almost 20 minutes a jacuzzi tukunna ya fito,jikin babban mirror din dake dakinsa ya tsaya ya zubawa kansa kallo,yayi kyau ya kara fresh kamar ba shine ya lalaceba kwanaki har kiba ya qara yi kadan,,,sadiq ne ya tura kofar dakin ya shigo fuskarsa dauke da dariyar mamaki yace OMG tiger why are you growing fat again?ya karasa maganar yana taba knuckles dinsa

"Duka ya kai masa a hankali yace get out,where is the fat?

"Cmon

"Red shirt da black trouser ya saka wanda suka yi matukar fito mishi da kyansa kamar yanda yake da,shi kansa jinsa yake very special kamar bashi ba,key din bugatti ya dauka black colour ya karasa parking space din kamshin perfume dunsa na tashi

"A zaune ya tarar da sadiq yana answering call,da sauri ya taso yasha gaban deen cikin tsokana yace mehhn sai ina?

"Key din hannunsa ya jefawa sadiq yace gurin beelah zaka kaini

"Bude baki sadiq yai yace OH GOD see romeo sannan yayi dariya

"Tsaki deen yai don indai tsokanar sadiq ce sai ya kwana yanayi be gaji ba,5pm sukayi parking a gidansu beelah

"Zaune take ita da aunty a'i suna cin wainar shinkafa da coconut juice,sosai nabeelah ke jin dadin abincin inda hankalinta ke gurin kallon data mayar da hankalinta akai,knocking door akayi babban yaron gidan ya shigo ya gaishesu sannan yace deen ne waje yake sallama da nabeelah,kamar an caka mata mashi taji bakin ciki a zuciyarta....wai ma me deen yake nufi danine?ya mayar dani wata abar wasansa kenan wacce aduk lokacin da ya kwaso wani rainin hankalinsa da iskancinsa zai juyesu a kaina?No and never!!!dagowa tai a zafafe tace kaje kace masa bazanzoba kuma daga yau kar ya sake zuwa gidanmu

"Har ya juya zai fita aunty a'i tai saurin dakatar dashi tace kaje kace tana zuwa

"A fusace ta kalli aunty a'i kamar me shirin kai mata duka sedai ganin irin kallon takaicin da aunty a'i ke mata yasha banban dana kowanne lokaci yasa nabeelah saurin dauke hannunta daga cikin kwanon abincin da sukeci ta dauki wayarta ta nufi apartment dinta

"Zonan!murnar aunty a'i ce ta doki kunnenta a fusace

"Tsayawa tai tace gani

"5 minutes na baki maza kije ki shirya ki fita gurin wanda ke jiranki a waje,don baze yiwu ki dinga korar duk wanda yazo wajenki da niyyar neman aureba bacin kuma ba wani tsayayye kika tsayar ba....na gaji da zama dake a cikin gidannan ya zama dole ki fitar da mijin aure nabeelah

"Maganganun aunty a'i ke yawo a zuciyar nabeelah,to wai ma har an gaji da zama dani kenan?yanzu idan nayi auren waye ze yarda ya zauna dani idan ya sameni macen daba budurwaba?musamman yanda auren yanzu ya zama auren sha'awa...ajiyar zuciya tai tace deen ka cuceni ka cuci rayuwata....na tsaneka,na tsaneka sannan ta fashe da kuka

"Wanke fuskarta tayi sannan ta janyo hijab har kasa jikin hanger ta saka ta fesa turare ta fito ta wuce aunty a'i dake zaune,ita kam dariya nabeelah ta bata ganin yanda ta saka hijabi har kasa duk dai don kar deen yace tayi kyau kenan?oho

"Cikin sallama ta tura door din guest room ta shiga idonta ya sauka a kyakkyawar fuskar deen da shima ya zuba mata ido yana kallo,dauke idonta tai sannan ta karasa inda yake zaune ta tsaya saitin kansa tace...i am here to warn you karka sake zuwa gidanmu baka da wani abu da zaka fadamin kamar yanda na tsani jin duk wata kalma da zata fito daga bakinka

"Tana gama fadar haka ta juya ta nufi kofa zata fita daga dakin,da sauri deen ya riko mata hijab muryarsa a sanyaye yace wait please,mari ta sauke mishi a kumatu sannan ta fisge gefen hijab dinta dake hannunsa tace don't you dare touch me again with your filthy hands

"A zafafe sadiq ya daga hannu ze kaiwa nabeelah mari deen yai saurin rike hannunsa a firgice yace don't touch her please koma meye lefinane da nai gangancin taba abu me daraja wanda ba muharrami naba,yana gama fadar haka ya kalli beelah dake tsaye yace am sorry beelah please forgive me..be jira ta sake cewa komai ba yaja hannun sadiq suka fita daga dakin inda ta saki baki bude tana mamaki

"Yaushe deen yasan yayi lefi har ya bada hakuri?Yaushe deen ya dauki mace a wani abu har yake kiranta me daraja?yaushe deen ya fara banbance mace da namiji har yake kiranta wai ba muharramarsaba?

Don't forget to vote,share and comment
Ramadan mubarak
From M.A

DeenWhere stories live. Discover now