Chapter 43

2.3K 268 16
                                    

"Sai da ya dauki morethan 4 hours kafin ya farfado,dad din beelah da dad dinshi ne tsaye akansa fuskokinsu cikin damuwa inka dauke mom din deen da tun da sukazo asibitin take zubar da hawaye,,,a hankali ya bude idonsa da yayi ja da sauri mom ta mike daga kujerar da take zaune ta karasa gurin deen da sauri tana daga hannunta sama tana godewa Allah Alhamdulillah,cikin damuwa dad din beelah ya kalli Alhaji modibbo yace wai menene yake damun deen ne har zuciyarsa ke kokarin samun matsala?ajiyar zuciya yayi yace toh waya sani,wlhy alamarin deen ya fara bani tsoro

"Da sauri mom ta kalli dad din deen tace babu abinda ke damun deen sai soyayyar nabeelah wacce ita kuma sam bata sonshi bata kaunarsa wanda bamusan dalilin yin hakan ba,ta karasa magana cikin takaici

"A matukar fusace dad beelah ya fita daga asibitin ba tare da yayi sallama da kowaba ya shiga motarsa ya nufi gida ransa a bace,a kasan upstairs ya tsaya fuskarsa babu alamar wasa ya fara kiran nabeelah,nabeela.....da gudu aunty a'i ta fito tana kallon dad din nabeelah cikin yanayin da bata taba ganinsa a cikiba

"Hoto ne ni da kika sani a gaba kina kallo?ya tambaya a fusace

"To ai alhaji na ganka cikin tashin hankaline kana kiran nabeelah Allah yasa dai lafiya,ta bashi amsa muryarta na rawa

"Nace ina nabeelah ko kuma ta kai matakin da ina kiranta bazata iya fitowa tazoba sedai in sameta a inda take?ya karasa magana yana kallon apartment din beelah

"Inajin bacci takeyi tunda kaji shiru bata fitoba amma bari na tasota,tana gama fadar haka ta nufi apartment din beelah......kamar yanda take tunani kuwa kwance take sedai idonta bude tana kallon ceiling,nabeelah ta kira sunanta a sanyaye....firgigit ta mike zaune ganin aunty a'i tsaye a gabanta ba tare da tasan sanda ta shigoba tace aunty muryarta na rawa

"Maza kije dad dinki yana kiranki,cikin shagwaba beelah tace aunty nifa bacci nakeji fa Allah amma bari nayi wanka sena fito,wurga mata harara tayi tace ki saurareni da kyau wannan kiran da mahaifinki ke miki yasha banban da kowanne kira gara ma ki tashi kije.....bata karasa magana ba dad ya turo kofa cikin bacin rai ya saukewa beelah mari guda 3,cikin kara ta dafe cheek dinta tana sake kallon dad cikin mamaki

"Idan kin maida kowa dan iska ni bazaki maidani karamin mutum ba,meyasa kika amince kina sonsa gaban mahaifinsa sai daga baya kizo ki chanja magana?me deen yayi miki da kike nuna masa kiyayyar da take barazanar salwantar da rayuwarsa?to bari in fada miki ni ba karamin mutum bane matukar kinason zama cikin farin ciki a gidan nan ya zama dole ki amince da deen idan kuwa ba haka ba wallahi sedai ki tattara kayanki ki bar min gidana don bazan zauna da yarinyar da batasan halacciba a rayuwarta,,,,kinsan waye alhaji modibbo ko a gurina?wallahi ba yarinyar dana haifa kawai ba hatta rayuwata zan iya mallaka masa don haka tunda bakyasonsa ki gaggauta hada kayanki ki bar min gidana

"Haba alhaji wacce irin magana kake fada haka?yarinyar da kake da ita tilo ita zakace ta bar maka gida?ko ka manta irin tarin gata da soyayyar da kake nunawa nabeelan?aunty a'i ta fadi maganar muryarta na rawa

"Muddin bazata bi umarnina ba to wallahi seta bar min gida ya karasa maganar yana nunata da yatsa

"Da sauri aunty a'i ta kalli nabeelah a tsorace tace ki bashi amsa kina son deen din ko bakyasonsa?

"Hawayene ya gangaro daga idon beelah tai saurin girgiza kanta tace bana sonshi kuma bazan taba iya aurensaba.....a firgice suka kalleta gaba daya dad be jira komaiba yaci gaba da dukanta kamar Allah ya aikoshi,,,sai da ya fasa mata jikinta da kyar aunty a'i ta tura nabeelah toilet tukunna ya fita yana sake nanata mata nan  da 1 hour baya bukatar sake ganinta a cikin gidansa

"Da sauri aunty a'i ta hadawa beelah kayanta ta turata gidan yayarta da suke kira aunty lami,tace taje chan tukunna kafin komai yayi dai-dai ba tare da sanin dad dinta ba....

"Cikin damuwa mom ta kalli deen da yake kwance tace deen meyasa kake azabtar da kanka akan yarinyar da bata damu dakai ba balle lafiyarka?meyasa kake son samu cikin damuwa?

"Murmushi deen yayi yace mom ki kwantar da hankalinki indai maganar nabeelah ce a gidan nan bazaki sake jintaba,nima na hakura da ita kamar yanda bata sona nima banasonta,kuma mom na baku zabi keda dad ku zabar min duk yarinyar da kuke ganin ta dace da tsarinku insha Allah ni kuma bazan baku kunyaba,,,,sosai mom tai farin ciki sannan ta bar dakin zuciyarta fes

"Sadiq ne ya dawo kusa dashi ya kalleshi cikin tsokana yace naji wani drama da kakeyi kana fadar ka hakura da nabeelah,,,,,tsaki deen yayi yace kaine kake ganinsa wasan kwaikwayo amma ni gurina gaskiya nake fada

"Murmushi sadiq yayi yace how can i believe it?

"Mikewa yayi zaune sannan ya kalli sadiq yace wallahi asap am serious na hakura da beelah,meyasa zan cigaba da wahalar da kaina akan yarinyar da bata sona kuma bata kunyar fadar kalmar a ko'ina wallahi asap na hakura da nabeelah har abada

Thank you for reading my story!!!
Don't forget to vote,share and comment

DeenWhere stories live. Discover now