Chapter 42

2.5K 285 18
                                    

"Bathroom ta shiga tayi wanka ta fito daure da towel taci gaba da tsane gashinta da wani towel din,dressing chair ta janyo ta zauna ta fuskanci babban dressing mirror din dake gefen dakin....sosai take tsara kwalliya a fuskarta kamar wata sabuwar amarya,kallon fuskarta taci gaba dayi na kusan 2 minutes a hankali tai tsaki ranta a bace tace oh shit!!!what the hell am i doing?wa nake yiwa kwalliya haka?i hate him,i don't like him meyasa zanyi kwalliya har ya gani?fuckkk!!!this is totally wrong,da sauri ta karasa gaban sink ta debi ruwa tana shirin zubawa a fuskarta aka fara knocking door dogon tsaki taja ranta a bace ta bude kofar sedai ganin kawarta fatima ya sata saurin sakin fuskarta tai hugging dinta cikin farin ciki don rabonsu da ganin juna kusan 3 years

"Cikin mamaki fatima ta kalleta tace nabeelah ya naga kin rame kin lalace kamar ba nabeelan dana saniba,meyake faruwa dake?tsaki ta sakeyi tace fatima kenan ai bayan rabuwarmu abubuwa dayawa sun faru dani,fatima rayuwata ta lalace duk ba kowane ya sani cikin wannan tashin hankalinba sai deen,deen shine mutumin da nafi tsana a rayuwata fatima deen ya cuceni ya gama da rayuwata ta karasa magana tana hawaye

"Deen,deen,deen wanne deen din?fatima ta fada a firgice tana sake kallonta,ringing din wayar nabeelah ne ya katse musu hirarsu ta daga wayar jikinta a sanyaye ganin number aunty a'i......okay kawai tace ta kashe wayar sannan ta kalli fatima tace sorry fatima nayi bako amma nan da 5 minutes zan dawo......hawayen da nabeelah ta gani a idon fatima shine ya sata saurin zama tace what's wrong teemah?ajiyar zuciya fatima tayi tace ina addu'a ne kar Allah yasa deen dinda kike min magana ya zama shine wanda nazo fada miki nima,wayarta ta ciro daga jaka ta nunawa beelah picture din deen tabbas shine sedai a wannan lokacin bata da damar tozarta deen a gaban fatima,jikinta sanyaye ta kalli fatima tace am sorry teemah idan na dawo zamuyi magana

"Tamkar drum ake buga mata a zuciyarta tsananin tsana da takaicin kasancewarta da deen wannan wanne irin masifa ce ace mijin da ake kokarin aura mata sanannene a hanyar zina wanda ba ita kadai ma ya lalata ba har kawayenta da suke mafi kusanci suma duk yayi amfani dasu wannan wanne irin abin kunyane?ya zama dole in lalalata aurena da deen baze yiwuba baze taba yiwuba,a fusace ta tura kofar ta tarar dashi zaune hankalinsa na kan wayarsa....abincin da aka jere gabansa ta fara ball dasu cikin kuka take faffasa plates da cups din dake gurin tana zubar da abincin stay away from me,bana sonka bana kaunarka i hate you ka fita daga rayuwana wlhy zan kasheka idan baka dena zuwa gurinaba

"A fusace ya mike ya shaqo wuyanta idanuwansa suka yi jaaa stop it,i said stop it mrs madness....don't you dare repeat your words again meyasa bakya sona?meyasa bakya kaunata?meyasa bazakiyi hakuri akan abinda ya faru a bayaba....daga yau bazan sake wahalar da kainaba akanki nabeelah kamar yanda bakya sona nima bana sonki....ke wacece da har bazaki iya yafiya ba a rayuwarki?Allah me girma daya halliccemu gaba daya munayi masa lefi yana yafe mana ballantana mu.......ok well i will stay away from you bazan sake nemankiba,yana gama fadar haka ya fice daga dakin zuciyarsa na bugawa da karfi tare da zazzafan ciwon kai

"A bakin mota ya tarar da sadiq tsaye yana wasa da wayarsa cikin rashin kuzari ya kalleshi yace asap let's go

"Bin bayansa tai da kallo zuciyarta na bugawa da sauri-sauri gaba daya jikinta yai sanyi wanda kafafuwanta sun kasa daukanta a hankali ta zube kasa tana sake maimaimata maganar deen i don't love you and i will stay away from you......meyasa zece baya sona?meyasa zeyi fushi ya tafi?ko ya manta duk abubuwan da yayi min a rayuwa?fashewa tai da kuka tana sake maimaita kalaman deen.....tunowa tai da fatima na jiranta a daki saurin goge fuskarta tayi ta dauki wayarta ta koma daki

"Fitowa tai fuskarta babu walwala ta kalli aunty a'i tace aunty ina fatima?

"Fatima ai ta tafi tun dazu ta gaji da jira tai tafiyarta,aunty a'i ta fadi maganar a takaice

"Amma aunty ai ba wani dadewa nayiba meyasa bazata jiraniba bacin tasan dadewar da mukayi rabon da muga juna,ta fadi maganar cikin shagwaba

"Oho muku dai ga number nan ta bari tace idan kinzo ki kirata,murmushi tai ta karbi number ta koma apartment dinta jikinta a matukar sanyaye

"Meyasa zan takurawa kaina da tunanin mutumin da ban damu dashiba?meyasa zan damu don yace baya sona baya kaunata.....kalmar da na dinga rokonsa ya furtamin,meyasa don ya furta min ita yau zanji haushi?omg kodai na fara haukacewa ne....maganganu nabeelah ke fada barkatai kamar mahaukaciya ta rasa dalilin damuwarta akan deen yace bayasonta

"Tun da suka shiga mota sadiq ke tambayarsa amma bece komaiba,sadiq na parking deen ya bude mota ya fito ba tare daya rufe motar ba ya nufi cikin gida sedai yana hawa kan veranda ya fara jin jiri,da sauri sadiq ya kira doctor kafin 30 minutes jikin deen ya rikice,cikin tashin hankali aka wuce dashi hospital

Don't forget to vote,share and comment
Don Allah ayi min hakuri gurin wannan slow update din nawa wlhy banda lfy ne ga kuma school issue's please try to understand

DeenWhere stories live. Discover now