Page 27

1.7K 83 0
                                    

_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S P.M.L*_ 💭💭💭

💞💞💞                    💞💞💞
                       *BURINA*
💞💞💞                     💞💞💞

   
                          ©
  *ZULAYHEART RANO*💞

*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*

'''Wannan page din Sadaukarwa ne gareku kawayen kwarai
Balaraba Shehu (Maman Yasmeen)
Juwairiyya Ibrahim (Maman Zainab)
Ba sai na faɗa irin son da nake yi maku ba domin ku kanku kun sani, sai dai na ce Allah ya bar kauna.'''

                        2⃣6⃣

Da kyar ta iya cewa "Umma bana jin zan daina kukan rashin Ya IK domin shi ne mutum na biyu bayan mahaifina da ya fara nuna min kauna, taya zan manta shi Umma?" Ta karasa maganar cikin kuka mai sauti. "Zaki iya jurewa Zainab ba wai ina nufin ki manta shi gaba daya bane, a'a ki bar wannan tunanin da koke-koke ki yi masa addu'a, ki dau dangana uwaye nawa suka rasa ya'yansu amma zaki ga basu bar yin farin ciki ba? Ya'ya nawa suka rasa iyayensu amma daga baya suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki? Mata nawa suka rasa mazajensu daga baya suke rayuwar farin ciki? Ina don ki nutsu ki dawo cikin hankalinki ki fuskanci abin da ke gaban ki." Cikin sigar lallashi Umma ke yi mata wadinnnan maganganun.

Shiru Zainab ta yi jikinta ya yi sanyi tabbas maganganun Umma gaskiya ne, to amma ita bata jin farin cikin ta zai dawo kamar da sai dai zata yi amfani da shawarar Umma ta ci gaba da yi masa addu'a "in sha Allah Umma a bar yin kuka na dau dangana kamar yadda kike so." Maganar kawai ta faɗa amma babu alamun sauyi a fuskarta. "Idan kin san wannan maganar da kika faɗa gaskiya ne to ki amshi abincin nan ki ci." Murmushi ta kalkalo wanda iyakar sa laɓɓa ta ce "Umma bana jin yunwa fa." "Au ashe baki yadda da magana ta ba ko?" Umma ta yi maganar tana tsare ta da ido.

Bata fuska ta yi kamar zata yi kuka sannan ta amshi abincin, loma biyu ta yi ta aje plet ɗin "Umma na koshi." "A'a kara kaɗan kinji?" "Allah Umma na koshi." "Matso ki ga wani abu." Umma ta yi mata magana. Matsowa ta yi da plet din, amsan cokalin hannunta  Umma ta yi ta dibo abincin bakin Zainab ta kai cikin daure fuska, babu musu ta bude baki Umma ta zuba mata, cikin kwanciyar hankali Umma ta rika bata har sai da ta tabbatar da ta koshi kafin ta barta, aiko nan da nan zufa ya fara ketowa Zainab rabonta da cin abinci kamar haka tun kafin IK ya yi hatsari.

"Tashi ki yo wanka." Umma ta bata umarni, tashi ta yi cike da kwarin jiki bata jima ba ta fito cikin doguwar riga baka wanda ya yi mata matuk'ar kyau, sai dai fuskar fayau babu make-up sai hoda da ta shafa "yawwa yar Umma madallah kin ga kin yi kyau, dauko mayafinki sai mu tafi gidan Malam mu gaida shi." Ciki ta koma ta dauko mayafin sannan suka fita Umma rike da hannun Fawzan. Daret gidan suka shiga sosai Abban Zainab ɗin ya yi farin cikin ganin ta saki jiki, sai da suka kai yamma lis kafin suka koma.

Da dare ta ɗauko duk wani abu da IK ya bata ta yi wa Umma bayani kamar yadda IK ya yi mata, umma bata amsa ba sai ce mata ta yi "ki aje a wajenki, idan Allah ya kaimu kafin mu tafi Kano sai a bai wa Malam. "To Umma amma ina son a sanya Usman ya rika kula da ginin domin a kammala da wuri." "Eh nima na yi tunanin haka amma mu bari har mu ji yadda Abban ki zai ce." A haka suka tsaida shawara.

Washegari gari Usman ne ya kawo masu ziyara, bayan sun gaisa ne da ya fuskanci Zainab ta ɗan soma warware wa, saboda da kanta ta yi masa bayanin komai na aikin makaranta da islamiyyar da za a gina, ya yi na'am da yadda suka tsara bayan sun gama maganar ne  ya bukaci ta shirya ya fara koya mata mota kafin su koma Kano domin satin sama za su fara test a school, sannan ga makarantar Fawzan shi ma an koma, bata yi wani musu ba domin girman alkawarin da ta daukarwa Umma "ok Usman amma ka bari sai zuwa gobe domin yanzu yamma ta yi ga sanyi." "To Allah ya kaimu goben." Ya gama maganar yana daukan Fawzan suka fita. Aiko haka aka yi washegarin Usman ya fara koya mata mota, da yake tana da basira bata jima ba ta kware domin da kanta tana ja zuwa gidan Abba.

****

Yau aka ba Alhaji sallama don haka sun hada kayansu tsaf, gaba daya motan Daddy suka shiga domin tafiya Rano, Mummy ce kawai bata ciki domin Daddy ya ce babu inda zata bisu don bai ga abin da zata yi masa a gida ba, don takaici har kuka Mummy ta yi ganin zata rabu da yaranta yau ne ranar farko da ta yi haushin rabuwar ta da Alhaji Ahmad. Tabbas tasan da suna tare babu abin da zai rabata da ya'yanta musamman Alhaji da ba lafiya ce da shi ba ita zata kula da yaronta har ya warware, tana kallo suka tafi dole itama tata motar ta shiga.

Shi kam Daddy Sam ko a jikinsa don bai yi nadamar abin da ya yi wa Mummy ba, hasalima wannan ba komai bane cikin abin da ya yi mata tanadi, cikin nasara  karfe sha biyu suka isa rano kai tsaye bangarensu dake cikin gidan suka sauka, mutanen gidan sai zuwa yi wa Alhaji sannu da jiki suke yi, nan da nan farin ciki ya mamaye su Fatima ganinsu cikin dangin su, nan tabar Daddy da Alhaji su kuma suka nufi gidan Aunty Ameena domin can zata zauna.

A ranar Daddy yaso zuwa wajen Abban Zainab amma zuwan da yan'uwansa suka yi sai ya hana, ai ko da safe kusan goma da mintina ya shirya shi da Ammar domin Alhaji ya ce ba zai iya fita ba, Abba na zaune a dakin kofar gida IK ya gyara masa da kansa, Daddy ne ya yi sallama cikin fara'a Abba ya tarbe su bayan sun gaisa Abba ya sanya aka kawo masu ruwa, sannan suka shiga hira. "Ka yi hakuri Malam tun tafiyata ban samu ɓullo wa ba sai yau, shima zuwan ba na jin dadi bane." "Allah sarki karka damu Alhaji ai dama rayuwa haka take, hira sosai Daddy da Abba suka yi  sun daɗe hak'uri Daddy ya yi ta ba Abba akan walak'ancin da Alhaji ya yi wa Zainab domin ya ji zafi sosai a hiran ne har yake labarta masa abinda ya yi wa Alhaji.

Sosai Abba ya tausaya masa har ya yi masa faɗa akan wannan mataki ya yi yawa, Daddy bai bar gidan ba sai da sha biyu ta wuce bayan tafiyar Daddy Zainab suka yi sallama ita da Umma da Fawzan, gaisawa suka yi sannan suka shiga hira cikin hiran Umma ke faɗawa Abba maganar tafiyar su anjima, murmushi Abba ya yi ya ce "Babu abin da zan ce maki Habiba sai dai Allah ya saka maku da Alhairi, hakika kin nuna min kauna tun da kika so abin da na haifa." "Haba Malam wannan fa ba abin damuwa ba ne kaɗai ka ci gaba da yi mana addu'a domin samun nasara a cikin harkokin mu." "Allah ya baku nasara." "Amin." Umma ta amsa ita kam Zainab hawaye ne suka wanke idonta domin tunawa da Burinta masoyinta IK a fili ta furta "Allah ya jikanka Ya Khalil." "Amin." Su Umma suka amsa.

Sannan Umma ta mik'awa Abba takaddun da ta yi mata bayani, ita dinma haka ta yi wa Abba bayanin komai, sosai ya yi na'am da a danka maganar ginin ga Usman suna gidan har karfe biyu sannan suka tafi bayan sun yi masu sallama domin daga can ba za su dawo ta gidan Abba ba, ko da suka koma wanka Zainab ta yi ta kuma yi wa Fawzan sannan ta shirya shi Umma ma ta yi akwatin kayansu suka fito da shi da yake Usman zai kai su. Sun fito har sun hau bisa titi Fawzan ya fara rigima sai an saya masa yogourt da farko Zainab ta yi banza da shi saboda kanta dake sarawa, ita dai ganin Usman ta yi ya tsaya da motar ya ce "Please Momman Fawzan ki amsan masa sai mu ci gaba da tafiya." Babu yadda ta iya haka ta fita rike da hannunsa, kanta akasa zata shiga shagon kenan ta ji ta yi karo da mutum a matukar razane ta ɗago suna hada ido ta daga hannun ta ta sakar masa mari ta ɗaura da fadin "Kai mahaukacin ina ne da baka kallon gabanka?" Da matukar mamakin ta ya zuba mata ido alamun rashin lafiya sun gama bayyana karara a tattare da shi, muryarsa kaɗai ya isa mutum ya tabbatar daga ciwo ya tashi "Zainab ni kika mara...?


*RANO*

BURINA COMPLETETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon